03/07/2026
TARIHIN SHAHID MUHAMMAD HABIBU ZAKARIYYA BICHI.
Sunan mahaifinsa Malam Zakariyya, mahaifiyarsa kuma sunanta Fatima Shi dan asalin garin Daddauda ne a Karamar Hukumar Bichi ta jihar Kano. Ya yi makarantar LEA Primary School Rigasa da ke Kaduna. Shahid Habibu mutum ne mai natsuwa. Kuma yana da wuya ka ga hushinsa, koyaushe za ka gan shi cikin kyawawan dabi'u.
Mun sami labarin cewa wata rana suna zaune da mahaifinsa, sai ya ce shi ne zai gaji kakansa. Sai mahaifinsa ya ce "Yaya za a yi ka gaje shi?" Sai shi kuma ya ce "Bari ka gani in Allah ya yarda." To dama kakan nasa ya dade da rasuwa. Wata rana da aiki ya zo makabarta aka tono shi, sai ga shi cikin likkafani k**ar yanzun aka rufe shi, face suma da ta rufe duk ilahirin jikinsa. Kuma ran da Shahid Habibu zai yi shahada ya fada wa wasu 'yan uwa cewa "Lalle yau ga dukkan alamu za a samu shahidi," kuma yana jin a kansa rabon zai fada. Sai wani abokinsa ya ce ba abin da zai faru. Shi kuma sai ya ce "To bari ka gani zuwa yamma." Sai kuwa abin da ya faru ya faru. Kuma a gidan da yake, saboda alamta addini da kuma yawan nasihohin da yake musu har kiran sa suke da 'Zakzaky'. Kuma wani lokaci in yana zaune da 'yan uwa yakan ce shi yana jin ba dadewa zai yi shahada.
Hakika ko ga al'umman gari ya sami kyakkyawan shaida. Hakika akwai wata baiwar Allah da yake yi musu aikin kwado da linzami (dama sana'arsa kenan) ta ce a je a nuría mata wadanda s**a kashe shi ta dauko masa fansa, saboda kyakkyawar shaida da ta yi masa. Wasu matasan gari ma saboda sanin da s**a yi masa, har muzahara s**a yi suna cewa in dai abin da yake na halin kwarai shi'a ne su ma a kashe su 'yan shi'a ne. Wasu ma har rubuta wa Malam Zakzaky takardar ta'aziyya s**a yi.
Aminci ya tabbata Gun Shuhada🥀
*Shuhada Channel Tv