16/10/2025
Mun maida Kano ta zama cibiyar kasuwanci ta yankin Sahel — Gwamna Yusuf
Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano ya bayyana cewa cikin sauri jihar Kano na zama babbar cibiyar kasuwanci ta yankin Sahel, sak**akon sauye-sauyen da aka aiwatar tare da janyo masu zuba hannun jari.
Gwamnan, wanda mai ba shi shawara kan harkokin jiha, Alhaji Usman Bala, ya wakilta a wajen kaddamar da littattafai biyu a Abuja, ya jaddada cewa gwamnatin sa na amfani da tarihin kasuwancin Kano tare da rungumar sabbin hanyoyin kasuwanci na zamani.
Ya ce gwamnatinsa ta dauki matakan farfado da tattalin arziki ta hanyar inganta tsaro, i'ababen more rayuwa, da bunkasa wutar lantarki.
Haka kuma, ya bayyana cewa an fara aikin sauya tsarin karbar kudaden shiga zuwa na zamani da kuma toshe hanyoyin salwantar kudade.