18/01/2026
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Kano, ta yi amfani da dabarun tsaro na tattara bayanan sirri wajen k**a mutane uku da ake zargi su ne s**a shirya ki$an gi||a na wata matar aure da ‘ya’yanta shida a Unguwar Dorayi Chiranchi, Kano jiya asabar
A karkashin jagorancin Kwamishinan ‘Yan Sandan Kano CP Ibrahim Adamu Bakori, PhD, sfipma, mnim, mnips, masis, tawagar kwararrun jami’an ‘yan sanda ta samu nasarar k**a wadanda ake zargin.
Wadanda aka k**a sun hada da Umar Auwalu dan shekara 23, mazaunin Unguwar Sabuwar Gandu, Kano, Isyaku Yakubu wanda aka fi sani da “Chebe” dan shekara 40, mazaunin Unguwar Sagagi Kano da kuma Yakubu Abdulaziz wanda aka fi sani da “Wawo”, dan shekara 21 mazaunin Unguwar Sabon Gida Sharada Kano
An k**a su ne yayin wani samame na sirri (Sting Operation) da ya gudana daga karfe 10 na dare a ranar 17 ga Janairu, 2026 zuwa karfe 4 na asubahin yau Lahadi
Shugaban da ya jagoranci aikata ta'addancin mai suna Umar Auwalu dan uwan matar ne da s**a ka$he, ya amsa laifin aikata ki$an, tare da bayyana cewa