29/11/2025
INNA LILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI’UN: Wani Yaro Ya Ràśu A Wajen Jana'izar Sheik Dahiru Bauchi
Rahotanni daga babban filin Idi na Kofar Wambai dake cikin garin Bauchi, sun tabbatar da cewa wani yaro da ba a tantance asalinsa ba ya rasu yayin gudanar da sallar jana’izar fitaccen Malamin Addinin Musulunci, Marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi, a yau.
Lamarin ya tayar da hankalin jama’a, kasancewar babu wanda ya san daga inda yaron ya fito, ko kuma tare da wane yake kafin faruwar rasuwar. Hakan ya sa ake kira ga jama’a da su taimaka wajen yada wannan bayani domin a gano danginsa ko wanda ya san shi.
Rahoto ya nuna cewa an kai gawar yaron Asibitin Bakaro bayan Fada a cikin garin Bauchi. Ana sa ran cewa da zarar an samu danginsa, za su zo su karɓe shi.
Sai dai, idan babu wanda ya bayyana a lokaci kusa, hukumomi za su mika gawar zuwa dakin ajiye gawa na Asibitin Koyarwa na Sir Abubakar Tafawa Balewa (ATBU Teaching Hospital) domin ci gaba da adana ta bisa ƙa’ida.
Allah Ya jikansa, Ya kuma bai wa iyalansa hakurin jure wannan rashi idan aka same su.
Daga Eagle Radio