08/05/2025
🎬SABON SHIRIN GWAMNATI: Sheikh Zakzaky Ya Bayyana Yadda Gwamnatin Najeriya Ke Ƙulla Makirci Kan Harkar Musulunci
—Freedom Fighters Nigeria🎙️
8 ga Mayu, 2025
Jagoran Harkar Musulunci a Najeriya, Sheikh Ibraheem Zakzaky, ya bayyana a cikin jawabinsa jiya Laraba, 7 ga watan Mayu, 2025, cewa, akwai wani babban shiri da gwamnatin Najeriya tare da haɗin guiwar wasu ƙasashen yamma k**ar Amurka da Birtaniya ke yi domin murkushe Harkar Musulunci da kuma hallaka mabiyanta.
A taron cikar kwanaki 40 na waɗanda aka kashe a Abuja ranar 28 ga watan Maris, 2025, yayin gudanar da Muzaharar Quds, a zaman da ya shirya a gidansa da ke Abuja tare da iyalan shahidan, Sheikh Zakzaky ya tona asiri cewa, tun a bara wani babban hafsan soja ya sanar da su cewa, gwamnati na yunƙurin kitsa makirci da nufin tsokano ƴan uwa domin samun dalilin kai musu hari, ya kuma bayyana cewa sun shirya sake dira gidansa a Abuja tun Yaumul Arba’een ɗin bara, bayan cin zarafin almajiran nasa, sai dai basu yi nasara ba sak**akon tafiyarsa don taron Arba'in ɗin a Iraqi.
Sheikh Zakzaky ya ce, wannan maƙircin na daga cikin dalilan da yasa s**a je har gidajen almajiransa s**a k**a mata da yara s**a tafi dasu tare da cire musu hijabi, da kuma yaɗa hotunansu a kafafen sada zumunta, inda har ya zuwa yanzu suke ci gaba da tsare ƴan’uwa mutum 33 a gidan yarin Keffi tun waƙi’ar ta Yaumul Arba'in na bara, abin da ke ƙara nuni da ƙoƙarin tayar da tarzoma da gangan, musamman lamarin Hijabi tunda sun fahimci illar cire wa mace hijabi ga Musulmi. Shehin ya kuma yabawa almajiran nasa sosai bisa matakan hankali da hikima da s**a ɗauka ta hanyar muzaharorin nuna rashin amincewa da lamarin.
Sheikh Zakzaky ya ci gaba da jaddada cewa muzaharar Quds ta bana an gudanar da ita cikin lumana a jihohi 35, sai dai a Abuja ne kawai sojoji s**a kai hari, inda dakarun da ke gadin shugaban ƙasa s**a bude wuta ga masu Muzaharan. Ya bayyana cewa sojoji sun aikata keta haddi da cin zarafin mata, ciki har da cire hijabin mace ɗaya da aka hangi dakaru bakwai suna yi a lokaci guda.
A cikin jawabin na Sheikh Zakzaky, ya bayyana cewa, bayan an samu labari cewa gwamnati na shirin kai farmaki gida-gida, sai sojoji s**a fito da wani bayani cewa wai an harbi soja guda ɗaya domin fakewa da hakan a matsayin hujjar gudanar da bincike. Daga baya kuma dai gwamnati da kanta ta musanta hakan, kuma babu wani ƙarin bayani daga hukumomin tsaro.
Jagoran ya bayyana cewa akwai wani shiri da gwamnati ke yi na harzuka mabiyansa (ƴan uwa Musulmi) ta hanyar tsokano su ta hanyar farmaki, domin su sami hujjar kai hari gidan Sheikh Zakzaky. Ya kuma bayyana cewa, takardar da mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan tsaro ya rubuta kafin Muhazarar ta Quds ba shi ya rubuta ba, inda ya fallasa cewa, wani jami’in tsaro ya bayyana cewa wata Ba’amurkiya ce da ke aiki a ofishin nasa (Malam Nuhu Ribaɗu) ce ta rubuta takardar.
Jagoran ya ƙara da cewa, ƙasashen yamma musamman Amurka da Birtaniya na tsoma baki kai tsaye a cikin wannan al’amari, yana cewa suna amfani da jami’an tsaron Najeriya a matsayin kayan aiki don cimma muradunsu a nan gida.
Daga ƙarshe, Sheikh Zakzaky ya ja hankalin gwamnatin Najeriya, yana mai gargadin cewa, duk wanda ya aikata kisan kai koda bai yi imani da Lahira ba, to zai tozarta, ga kuma masu ikirarin musulmi, to lallai za su fuskanci hukuncin Allah, tun a duniya kafin Lahira. Ya kuma yi addu’a ga shahidan da s**a rasa rayukansu tare da jaddada cewa jinin da aka zubar ba zai tafi a banza ba.
Domin samun sauran bayanai dangane da jawabin na Sheikh Zakzaky, ku shiga wannan madadin: https://www.facebook.com/100069545017600/posts/1008996384761853/?app=fbl