19/10/2025
Takaitaccen Tarihin Annabi Muhammadu (S.A.W)
1. HAIHUWAR SA DA ASALINSA
Annabi Muhammadu (S.A.W) an haife shi ne a garin Makka a shekara ta 570 Miladiyya, shekarar da ake kira shekarar giwaye – a shekarar da sarki Abrahata yazo da rundunar giwaye domin rusa ka'aba, amma Allah ya halaka su da tsuntsaye masu jifa da duwatsu na wuta.
Sunansa Muhammadu ɗan Abdullahi ɗan Abdul-Muṭṭalib, daga zuriyar Annabi Isma’il ɗan Annabi Ibrahim (AS). Mahaifinsa ya rasu tun kafin a haife shi, mahaifiyarsa kuma, Aminatu ta rasu tun yana ƙarami.
2. ƘURUCIYAR SA DA HALAYENSA
Yayin da yake ƙarami ya girma ne a wajen wata mace mai suna Halimatu sa’adiyya wadda ta reneshi a karkara
ya kasance mai kamala gaskiya da amana har ma mutanen makkah suna kiransa da "Al-Amin" (Amintacce).
3. AUREN SHI DA SAYYADA KHADIJAH
Yana da shekara 25, ya yi aure da Sayyida Khadijah bint Khuwaylid, wata babbar mace mai arziki kuma mai daraja, Ita ce mace ta farko da ta karɓi Musulunci kuma ta kasance garkuwa gare shi (s.a.w)
4. FARKON WAHAYI
Yana da shekara 40, a yayin da yake zaune a (dutsen hira) sai Mala’ika Jibrilu ya zo da saƙo daga Allah:
"Karanta!" (Iqraa’)
Wannan shine farkon saƙon Annabci – wanda ya kai shekaru 23 yana yada shi.
5. GWAJI DA ƘOƘARIN YAƊA SAƘO
A Makka, mutane da yawa sun ƙi karɓar saƙonsa, musamman ‘yan ƙabilar Quraysh, sun tsananta masa da sahabbansa, sun ƙuntata musu, har aka tilasta wasu yin hijira zuwa Habasha..👌
6. HIJIRARSA ZUWA MADINA 🌴🌴
Daga ƙarshe, Allah (s.w.a) ya umarce shi da yayi hijirah daga makkah zuwa garin madina, Ya bar Makka tare da abokinsa Abubakar As-siddiq (RA)
Wannan hijirah itace ta wanzar da sabuwar rayuwa ga musulmi baki ɗaya..🫵👌
7. JIHADI
A madina ne Annabi (S.A.W) ya kafa al'umma ta musulunci bisa gaskiya, adalci da zumunta tsakanin mabiya, an yi wasu yaƙe-yaƙe don kare Musulunci kamar 1-Badr
2-Uhud
3-Khandaq
Annabi bai taɓa zaluntar kowa ba–hatta da maƙiyansa ma idan sunyi masa abu na cutarwa yakan yafe musu (s.a.w)
8. KARƁAR MAKKAH:
Bayan shekara 8 da hijira, Annabi (SAW) ya koma Makka cikin nasara da ladabi, baiyi ramuwa game da azabar da kafiran makkah sukayi masa ba, yakan ce dasu:
"Ku tafi, kun ƴanta, babu laifi a kanku."
Wannan ya nuna tausayi da yake dashi a zuciyarsa da rahama
9. WAFATIN SA
A shekara ta 11 bayan hijira (632 Miladiyya), Annabi (SAW) ya rasu yana da shekara 63. Ya rasu a cikin dakin matarsa da yafi ƙauna A’isha (RA), kuma aka binne shi a can.
Annabi Muhammadu (SAW) rahama ne ga duniya baki ɗaya, saƙonsa da yazo dashi babu komi a ciki face gaskiya da adalci...❤️❤️💞