M Gawo

M Gawo Barka da zuwa shafin haruna hassan maruruci manazarcin harshen hausa mawaki siyasa biki sarauta suna

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN Allah Madaukakin Sarki Ya karbi rayuwar Babbban Malamin Tauhidi na Afirka Sheikh Dr I...
04/04/2025

INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJI'UN

Allah Madaukakin Sarki Ya karbi rayuwar Babbban Malamin Tauhidi na Afirka Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Dutsen Tanshi Bauchi

Malam ya koma ga Allah a cikin daren nan yana mai maimaita kalmar shahada a bakinsa

Hakika babban bango majingini ga da'awar Sunnah a Afirka ya fadi😭😭😭

Allah Ka jikan Malam, Ka yafe masa kura-kuransa😭😭🙏🙏

30/03/2025
YANZU YANZU: Ministan Abuja Wike ya nemi yan Nigeria Su Saka shi a cikin Addu'a domin jikinsa yayi tsanani da yawa yanac...
30/03/2025

YANZU YANZU: Ministan Abuja Wike ya nemi yan Nigeria Su Saka shi a cikin Addu'a domin jikinsa yayi tsanani da yawa yanacan Rai a Hannun Allah

likitoci Sunce Rashin lafiyar Wike ta tsananta—Likitoci

Taqabbalallahu Minna Wa Minkum!On this blessed day, I pray that peace, happiness, and prosperity fill your life and the ...
30/03/2025

Taqabbalallahu Minna Wa Minkum!

On this blessed day, I pray that peace, happiness, and prosperity fill your life and the lives of your loved ones. As we bid farewell to the sacred month of Ramadan, let us strive to leave behind all wrongdoings and negative behavior, and continue on the path of righteousness.May Allah accepts all our acts of worship, forgives our shortcomings, and grants us His endless mercy.

Eid al-Fitr Mubarak🤍

Allah ya maimaita mana ya karbi ibadunmu 🙏🙏

Duk Yawan Kuɗin Nan Mutunci Yafisu🥱
29/03/2025

Duk Yawan Kuɗin Nan Mutunci Yafisu🥱

29/03/2025

Da dumi duminsa anga jinjirin watan shauwal a Nigeria gobe lahadi take sallah

Shékaru 50, Marigayì Sa'adú Zungur Yayi Wànnan Wa'azin A Sigar Wàƙa ~ Matukar a arewa da kãruwái,~ yan dâudu dasu da mag...
29/03/2025

Shékaru 50, Marigayì Sa'adú Zungur Yayi Wànnan Wa'azin A Sigar Wàƙa

~ Matukar a arewa da kãruwái,
~ yan dâudu dasu da magajiya.
~ Da samari masu ruwâɲ kudi,
~ Ga mâshaya can a gidaɲ gîyâ.
~ Matukar yayan mu suna bara,
~ T**i da Loko-lokon Nijeriya.
~ Hanyar birni da na kauyuka,
~ Allah baku mu samu abin miya.
~ Sun yafu da fatar bunsuru,
~ Babu mai tanyonsu da dukiya.
~ Babu shakka yan kudu zasu hau,
~ Dokin mulkin Nijeriya.
~ In ko yan kudu sunka hau,
~ Babu sauran dadi, dada kowa zai
sha wuya.
~ A Arewa zumunta ta mutu,
~ Sai karya sai sharholiya.
~ Camfe-camfe da tsibbace
tsibbacen,
~ Malaman karya yan damfara.
~ Sai karya sai kwambon tsiya,
~ Sai hula mai annakiya.
~ Ga gorin asali da na dukiya,
~ Sai kace dan annabi fariya.
~ Jahilci ya ci lakar mu duk,
~ Ya sa mana sarka har wuya.
Ya sa mana ankwa hannuwa,
~ Ya daure kafarmu da tsarkiya.
~ Bakunan mu ya sa takunkumi,
~ Ba zalaka sai sharholiya.
~ Wagga al’umma mai zata yo,
~ A cikin zarafofin duniya.
Kai Bahaushe ba shi da zuciya ,
~ Zaya sha kunya nan duniya “.
~ “Mu dai hakkin mu gaya muku,
~ Ko ku karba ko kuyi dariya.
~ Dariyar ku ta zam kuka gaba,
da nadamar mai kin gaskiya.
~ Gaskiya ba ta neman ado,
ko na zakin muryar zabiya.
~ Karya ce mai launi bakwai,
ga fari da baki ga rawaya.
~ Ga kore ga kuma algashi,
toka-toka da ja sun garwaya”.
~ Marigayi Sa’adu Zungur a cikin
~ waken sa mai suna “Arewa
~ Jamhuriya ko Mulukiya”

Allah Yajiƙan Malam Saadu Zungur

Allah kayimasa Rahama. Amin

29/03/2025

Ba'a Gwagwarmaya da kwadayi, sannan ba a fadan gaskiya da Maula
📌📌📌📌📌📌

29/03/2025

Kamata yayi Kafin a fara binciken yan arewa su tura kamar mutum 100 bar**hu, sai ayi binciken daga Baya

29/03/2025

Zamu dauki mataki akan yan'uwansu dake kusa damu dazaran mungama azumu insha Allah

29/03/2025

Shuwa gabannin da muke zaba a arewa karnukane

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when M Gawo posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share