
29/03/2025
YADDA HAIHUWAR JARIRIN WATAN SALLAH ( SHAWWAL ) DA BAYYANARSA A SARARIN SAMANIYA DA IZININ ALLAH, 29/03/2025.
FANIS /NS/KD/001/1446 - 2025/00031
KUNGIYAR MALAMAI MASANA ILIMIN TAURARI-NAJERIYA
(FALAKI NETWORK)
Bismillahir-Rahmanirr-Raheem was salatu was-salamu ala Atimmanil-Akmalaniy Sayyidna Muhammadur RasulilLah wa Ahali baitihil Dayyibinal Dahireen : Kamar kullum shi ilimin Falaki ilimine Qa'imi da aka gada tun iyaye da Kakanni amma kullum qara fadada yake musamman yanzu da ake ta samun cigaba duk bayan lokaci , to zamu bi lamarin ganin Jinjiri Watan Sallah bisa lura da yadda Malamnanmu na zaure da ma Turawa suke yin nasu a zamanin ce (Westrrn Astrology) .
Insha Allahu za a haifi jinjirin watan sallah (Shawwal) na shekarar 1446H (wato haduwar wata a tsakiyar rana) a Yau din nan Asabar, 29 ga watan Maris, 2025 dai dai 29 ga Watan Ramadhan 1446 bayan hijrar Shugaba (S.A.W) daga Makkah zuwa Madinah da ƙarfe 11:58 na rana amma bisa daidaitaccen lokaci na duniya (UTC) za'a samu ragin sa'a guda wato (-1 hour) sabanin Agogon GMT da akan qara sa'a daya (+1 hour) Agogon Najeriya , Qasar Kamaru da kuma Chadi .
Kamar yadda taswirar da ke qasa ta nuna, ana iya ganin jinjirin watan Sallah (Shawwal) da ido qarara a yammacin Arewacin (Northwestern) Amurka (Kanada) a daren Asabar (daren shiga Lahadi), sannan ana iya ganin sa da na’urar hangen nesa a mafi yawan yankunan Arewacin da Tsakiyar Amurka.
A yammacin Lahadi (daren shiga Litinin), ana iya ganin jaririn watan da ido qarara cikin sauƙi a mafi yawan sassan duniya irinsu Arctic, Kanada da wasu Qasashenmu na nan Nahiyar Afirka da izinin Allah .
A halin yanzu watan da muke ciki na Ramadhan Ya samu kwanaki 29 da sa'o'i kusan bakwai da haihuwa inda ya qure dukkan wani haske na sa da ya tsururuta daga Rana (Illumination) kuma ba zai qara samun wani ba har zuwa bacewarsa tunda ya kai darajajin qarshe (Last Degrees)har 357° a halin yanzu kenan sai dai mu jira jinjirin Watan da Allah (SWT) zai qara halitta nan da kimanin sa'o'i 4 da daqiqoqi 24 zuwa 25 . A daidai lokacin da Junjirin wata yake lullube bai kai qwarin bude idon da zai iya karbar hasken rana ba ballanta na ya haska kansa idaniya ta iya ganinsa .
Akarshe kamar yadda mai girma sarkin musulmi ya bada na cewa kowa ya duba watan sabon jinjijirin wata ayau 29 ga Ramadan, muna fatan kowa zai himmatu, ga wanda Allah yasa yadace da ganinsa, ya sanar zuwaga hanyoyin da aka samar domin tabbatarwa.
Sanya Hannu :
Muhammad Misbahu
Hamza Ahmad (Falaki);
Amadadin :
Shugaban Kwamitin Bincike na Kasa.
Allah yasa mudace.
Allah ya amsa Ibadun mu. Amin
[email protected]