24/12/2025
Shugaban APC na kasa ya nada tsohon Sanata, Imran Mohammed da wasu mutane 14 a matsayin mataimaka
Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa Nentawe Yilwatda, ya amince da nadin mataimaka 15, ciki har da tsohon sanata da wani mashahurin mai amfani da kafafen sada zumunta, domin karfafa ayyukan gudanarwa da tsare-tsaren jam’iyyar.
Nadin sun hada da mashawarta na musamman da mashawarta, da manyan mataimakan musamman, kuma an tsara su ne domin bunkasa hadin kai, tsara manufofi, da kuma hulda da masu ruwa da tsaki a Babban Ofishin Jam’iyyar.
Wannan ya fito ne a cikin wata sanarwa da Mustapha Dawaki, Babban sakataren shugaban kasa na APC, ya fitar.
Sanarwar ta ce ana sa ran wadanda aka nada za su yi amfani da gogewa da kwarewarsu wajen tallafawa shugaban jam’iyyar wajen gudanar da ayyukansa.
Daga cikin wadanda aka nada akwai tsohon sanata Danladi Sankara, wanda zai zama Mashawarci na Musamman kan Al’amuran Siyasa.
Daniel Reyenieju Oritsegbubemi an nada shi Mashawarci na musamman kan Al’amuran majalisar dokoki, yayin da Sorochi Longdet ya zama Mashawarci na Musamman kan bincike, tsare-tsare da shirye-shirye.
Wasu daga cikin mashawartan sun hada da Jibrin Abdullahi Surajo (Hulda da Al’umma), Paul Domsing (Ayyuka na Musamman), da Suleiman Bukari.
Taiwo Ajibolu Balofin kuma an nada shi a matsayin Mashawarci na girmamawa kan hadin kai da tattara ‘yan ƙasashen waje.
A matakin manyan mataimakan musamman, mashahurin mai amfani da kafafen sada zumunta, Imran Mohammed, an nada shi a matsayin Babban Mataimaki na Musamman kan Sabbin Kafafen Sadarwa.
Mildred Bako an nada ta Babban Mataimaki na Musamman kan Kungiyoyin Al’umma, Yusuf Dingyadi ya zama Babban Mataimaki na Musamman kan Kafofin Watsa Labarai, yayin da Enenedu Idusuyi aka nada shi Babban Mataimaki na Musamman kan tsari da sauransu.
Sanarwar ta ce nadin mataimakan wani bangare ne na kokarin da ake ci gaba da yi don kara inganci a shugabancin kasa na jam’iyyar.