14/10/2025
DA ƊUMI-ƊUMI: Sojojin Madagascar Sun Karɓe Mulki Bayan Rusa Majalisar Dokoki Da Shugaba Rajoelina Ya Yi.
Rikicin siyasa a ƙasar Madagascar ya shiga sabon salo, bayan da rundunar sojin ƙasar ta sanar da cewa ta karɓe mulki daga hannun Shugaba Andry Rajoelina, wanda a kwanakin baya ya rusa majalisar dokokin ƙasar domin kauce wa yunƙurin ’yan'adawa na tsige shi.
A cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters, rundunar sojin ta tabbatar da karɓar mulkin a safiyar Talata, yayin da AFP ta ruwaito wani soja mai muƙamin Kanal, Michael Randrianirina, shugaban rundunar tsaron fadar shugaban ƙasa, yana karanta sanarwar a gidan radiyon ƙasar.
A cikin sanarwar, Kanal Randrianirina ya ce: “Mun karɓe mulki daga yanzu.” An ce rundunar da ke tsaron fadar shugaban ƙasa ta juya masa baya ne a ƙarshen mako, ta hanyar shiga cikin zanga-zangar masu neman shugaban ya yi murabus.
Tun a baya, Shugaba Rajoelina ya rusa majalisar dokokin ƙasar domin hana ’yan'adawa kada kuri’ar tsige shi, bayan makonni biyu na zanga-zangar da ta rikide ta zama tashin hankali, wadda matasa s**a jagoranta suna zargin gwamnati da cin hanci da rashawa da kuma zalunci.
Fadar shugaban ƙasa ta bayyana a wata sanarwa cewa dokar rusa majalisar “ta fara aiki nan take bayan wallafawa ta rediyo ko talabijin.”
Duk da kiraye-kirayen da ake masa da ya yi murabus, Rajoelina ya ci gaba da kare matakinsa a shafukan sada zumunta, yana cewa matakin ya zama wajibi domin dawo da doka da oda da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyya.
Sai dai rahotanni sun nuna cewa shugaban ya tsere daga ƙasar a ƙarshen makon nan a cikin jirgin soja na Faransa, duk da cewa hukumomin Faransa ba su tabbatar da hakan ba.
Rajoelina, tsohon magajin garin babban birnin Antananarivo, ya ce yana cikin “wuri mai tsaro” bayan yunkurin kisan shi, amma bai bayyana inda yake ba.
Kamar yadda Jaridar Taskar Labarai ta tattaro, Zanga-zangar dai ta fara a ranar 25 ga Satumba ta ƙara ƙamari bayan da wasu sojoji da jami’an tsaro s**a koma gefen masu zanga-zanga, suna kir