03/11/2025
ALAMOMI 8 DA SUKE NUNA KAI BA NAMIJI NA GARI BANE.
Ka auna kanka da waɗannan, ɗan uwa. Idan ka ga ɗaya a jikinka, lokaci yayi da zaka gyara:
1. RASHIN KAMUN KAI: Yana bin jin daɗi, yana gujewa wahala. Kamun kai ƘARFI NE. Idan babu shi, namiji zai zama rago, malalaci, kuma ba za'a damu da shi ba.
2. NEMAN YABO: Yana rayuwa don a yaba masa, ba don ya gina kansa ba. Namiji jarumi ya ishi kansa shaida.
Namiji jarumi yana samun gamsuwa ne daga ci gabansa, ba daga yabon mutane ba. Idan ra'ayin wasu shine yake sarrafa ka, ba za ka taɓa sarrafa rayuwarka ba.
3. GUDUN NAUYI: Koda yaushe wasu ne suke da laifi. Namiji na gaske yana ɗaukar nauyin halin da yake ciki.
Yana zargin abin da ya wuce, iyayensa, maigidansa, gwamnati... kowa sai dai kansa. Namiji na gaske yana ɗaukar nauyin halin da yake ciki, koda kuwa ba shi ya jawo ba.
4. ZUCIYA CE KE JANSA: Yana abu da zafin rai, ba da hankali ba. Ikon sarrafa zuciya shine alamar jarumta.
Idan ka mallaki zuciyarka, ka mallaki duniyar da ke kewaye da kai.
5. RASHIN MANUFA: Yana rayuwa ne kawai ba tare da wata alkibla ba. Manufa ita ce take bawa wahala ma'ana.
Idan babu manufa, kowane irin shagaltuwa zai zama kamar yana da muhimmanci, kuma kowace irin wahala za ta zama kamar azaba.
6. ZAMA DA RAGWAYE: Abokanka sune madubinka. Idan kana zama da marasa ƙarfi, kai ma zaka zama ɗaya.
Ka zauna da malalata, masu tsegumi, ko masu shaye-shaye, kai ma zaka zama ɗaya daga cikinsu.
7. YAWAN SURUTU, BABU AIKI: Magana barkatai, amma babu abin da ake gani a ƙasa. Aiki shine ainihin ma'auni.
Mutum mafi hayaniya a cikin taro, galibi shi ne mafi rauni.
8. WASAssalam DA SALLAR ASUBA (Musamman a Jam'i): Fagen fama na farko da ake cin nasara a kowace rana shine akan gado da Shaiɗan. Wanda ya kasa wannan yaƙin, ya nuna alamar rauni babba.
Ka gina kanka, ka guji waɗannan halayen. Nasararka ta duniya da lahira tana cikin haka.