12/01/2026
Rahotanni daga Jaridar Times of Israel sun bayyana cewa rundunar sojin Isra’ila (IDF) ta riga ta kammala tsare-tsare na sake fara manyan hare-haren soja a Zirin Gaza.
Majiyoyi sun ce ana hasashen waɗannan hare-haren za su fara ne kusan watan Maris na wannan shekarar. Tsare-tsaren sun haɗa da sake kai farmaki Gaza City tare da yunƙurin ƙwace birnin gaba ɗaya.
Rahoton ya ƙara da cewa za a umarci sojoji su matsada layin rabewa da ake kira Yellow Line zuwa bakin teku. A wani yanayi, sojojin na iya mamaye dukkan yankin, suna tura ‘yan gwagwarmayar Hamas zuwa gaɓar teku.
Shin me za ku ce game da wannan?
Follow Kasata ayau 👉🇳🇬domin samun ingatattun labarai