03/12/2025
LABARI CIKIN HOTUNA: Rundunar 'Yan Sandan Jihar Bauchi Ta K**a Babban Dilan Miyagun Kwayoyi a Ningi
Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta tabbatar da k**a wani da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi, Mr. Ogbu Simon, tare da kwato sama da kwayoyi 18,000 a Ningi, Jihar Bauchi.
A cewar sanarwar da Jami’in Hulɗa da Jama’a na Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya fitar, an k**a wanda ake zargin ne da Tramadol guda 17,500 na da kwanduna 487 na Diazepam (D5), da ake kira “Yellow Voice”.
Lamarin ya faru ne ranar 26 ga Nuwamba 2025 da misalin ƙarfe 8 na dare, bayan samun sahihan bayanan sirri daga wani mai kishin al’umma game da zargin ana sauke buhunan kwayoyi a shagon mutumin da ake zargi a cikin garin Ningi.
A bisa wannan bayanin, tawagar ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin DPO na Ningi, CSP Surajo Ibrahim Birnin Kudu, s**a kai samame a shagon. An gano buhuna huɗu cike da Tramadol da Diazepam.
Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ya umarci a mika lamarin ga Sashin Binciken Manyan Laifuka na Jihar (SCID) domin zurfafa bincike.
Daga nan aka tura tawagar Operation Restore Peace (ORP) ƙarƙashin CSP Abdulrazak Fada domin cigaba da bincike, wanda daga bisani ya kai ga cafke mutumin da ake zargi. Ya amsa laifinsa inda ya ce yana kawo miyagun kwayoyin ne daga Onitsha zuwa Ningi da kewaye.
Abubuwan da aka kwato sun haɗa da:
Kayayyakin da aka kwato ya kai na naira miliyan 12.2 (₦12,200,000).
Kwamishinan ‘Yan Sanda, CP Sani Omolori Aliyu, ya jaddada kudirin rundunar wajen yaƙi da duk wani laifi na miyagun kwayoyi, tare da roƙon jama’a da su ci gaba da taimaka wa ‘yan sanda da bayanai.
An ce za a mika wanda ake zargi tare da kayayyakin da aka kwato ga Hukumar NDLEA domin ci gaba da bincike da gurfanarwa a kotu.