SHI'A Nigeria

SHI'A  Nigeria We are All Palestine 🇵🇸 لا إله إلا الله محمد رسول الله

13/03/2026

Muzaharar Qudus karfe 2 na rana ne a garin Suleja.

SANARWAR MUZAHARAR QUDS ABUJAMu na sanar da yan uwa da dukkan al'ummar dake halartar Muzaharar Quds a Abuja cewa, Muzaha...
13/03/2026

SANARWAR MUZAHARAR QUDS ABUJA

Mu na sanar da yan uwa da dukkan al'ummar dake halartar Muzaharar Quds a Abuja cewa, Muzaharar Quds ta yau Juma'a 24 Ramadan, 1447 (13 March, 2026) a Suleja ne za ayi.

*Lokaci:* 10:00 am (na safe).

Domin sanin Wurin da za a fara Muzaharar, a tuntubi Wakilan Yan uwa da na Fora.

Allah ya ba da ikon halarta.

Sanarwa
Mu'assasatu Abul Fadl Abbas, Sisters Forum da Academic Forum.

Muna roƙon Allah Ta'ala yakare ƴan uwa daga wannan ganawar munafurcin.
12/03/2026

Muna roƙon Allah Ta'ala yakare ƴan uwa daga wannan ganawar munafurcin.

Tinubu ya yi ganawar sirri da manyan hafsoshin sojin Nijeriya

“Idan Muzaharar da muke yi ihun mu kawai muke yi, mai yasa maƙiya su ka damu?, Ba sai abar mu, muyi ta ihun mu ba?. Maye...
12/03/2026

“Idan Muzaharar da muke yi ihun mu kawai muke yi, mai yasa maƙiya su ka damu?, Ba sai abar mu, muyi ta ihun mu ba?. Maye nasu na kisa da ɗauri? Sun san cewa wan-nan ne zai kai mu ga zuwa Masjidil Aqsa mu yi sallah, sun san hakan sa rai. Kuma Muzaharar Qudus an shiga yi ke nan har ranar da zamu je masjidil aqsa mu yi sallah”.

—Shaikh Ibraheem Zakzaky [H] Cikin Jawabin tunawa da shekara daya da shahidan Qudus na 2014.

Ja'afar Muhammad Jr

🚨 AlartKasar Amurka na shirin kaiwa kanta hari a  Najeriya, kuma zata lakawa wasu sharrin su s**a kai mata harinIdan bak...
12/03/2026

🚨 Alart

Kasar Amurka na shirin kaiwa kanta hari a Najeriya, kuma zata lakawa wasu sharrin su s**a kai mata harin

Idan baku manta ba sun fitar da sanarwa cewa ana kokarin kaiwa Embassy dinsu dake Abuja harin ta'addanci, tare da wasu muhallansu dake wasu wajaje a kasar"

Akwai yiyuwar inde ankai wannan harin sune s**a kai wa kansu da kansu harin domin cimma wata manufa na yiwa wasu sharrin su s**a kai hari" ga duk wanda yasan Embassy din Amurka dake Abuja, shine a kusa da Defence Headquarters, tako ina kewaye yake da jami'an tsaro, babu wasu da zasu iya kaiwa wajen nan hari a cikin gida Najeriya, matukar ba su s**a kai wannan harin da kansu ba.

Saboda haka muna gayawa al'ummar Najeriya cewa ta'addancin da suke yiwa wasu a kasashensu shi sukeso su cigaba dayi a kasarmu da sahalewar gwamnatin kasar, inde wani abu ya faru su s**a kaiwa kansu da kansu hari, sannan kuma basu isa su fito su yiwa wasu kage, da karya, da sharrin sun kai musu hari ba.

Shere Please 🙏

IMC
11th/ Mar/ 2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Yusuf Badaru, Akaka Ka, Bin Mustapha, Mk Prince, Muhammad...
11/03/2026

Shout out to my newest followers! Excited to have you onboard! Yusuf Badaru, Akaka Ka, Bin Mustapha, Mk Prince, Muhammad Hudu, Raubilu Yahaya, Nafisa Abubakar, Zuhra Muhammad

Bamu taɓa kashe kowa ba, saboda haka Ranar Juma'ar ƙarahen watan nan na Ramadan sai mun fito ƙwanmu da ƙwarƙwatar mu mun...
11/03/2026

Bamu taɓa kashe kowa ba, saboda haka Ranar Juma'ar ƙarahen watan nan na Ramadan sai mun fito ƙwanmu da ƙwarƙwatar mu mun nuna goyon bayan mu ga al'ummar Palastinu...!

Cewar Harkar Muslunci

A firar su da manema labarai, sun ce mun gani yadda ƴan Biafra s**a fito da tutocin America da Isra**ila s**a nuna goyon bayan su garesu, ba wanda ya ce musu uffan, to saboda haka mu ma ba gudu ba ja da baya, kowa yana da ƴancin yin abunda yake so a ƙasar nan...

Sun ce, aƙalla shekaru 78 kenan, babu wata rana da za ta fito ta faɗi Isra**ila ba ta kashe mutum a Palastine ba, amma wai Jakadan Isra**ila yake iya kiran wasu da ƴan ta'addan, to amma tunda ya ambaci Iran a Najeriya mun san damu yake, kuma insha Allahu za mu tabbatar masa da mu ba ƴan ta'adda bane sune ƴan ta'adda.!

S**a ce, Sannan wannan Harkar da ya gani ta girmi juyin juya halin na Iran, dama akwai ta kawai dai faɗuwa ce ta zo dai-dai da zama. Saboda ana ta tunanin ya za'ai a koma wa tsarin da Shehu Usman Dan Fodio ya bari, ana haka kawai sai gashi mun gani a Iran sun yi kuma sun samu nasara, shine aka ce to Alhamdulillahi shine muka karɓi wannan hanya ta Imamul Khumaini muka riƙe shi a matsayin jagora, to batun a ce wai Iran ce ke goyon bayan Harka ko take ɗaukar nauyin Harka in ma akwai shi to ba mu san wane iri suke nufi ba. Amma Jakadan ƙasar Isra**ila dai bai da bakin da zai buɗe ya yi maganar ta'addanci, don Yakamata ma ya ji kunya ne...!

S**a ci gaba da cewa, Saboda haka muna ma gayyatar kowa da kowa jerin gwano da za mu yi, don taro ne na lumana, taro ne na ƴanci na sani darajar ƴan adamka, ba abunda zai faru in kuma aka ga ya faru to ba daga garemu bane daga jami'an ne. Shi dai zalunci da adalci baida Addini kuma baida ƙabila, batun ba na iya Musluncin bane, ƴan adamtaka ne.! Taro ne na duk duniya da ake yi a London, Berlin, Paris, Athens, Madrid, New York, Washington D.C., Los Angeles, Toronto, Sydney and Kuala Lumpur. Da dai sauran su. To a nan Najeriya ma Harkar Muslunci na shirya shi duk shekara.!

Saƙon Professor Abdullahi Ɗanladi

Husaini Ahmad na rubuta wani abu daga ciki.

The DSS cannot arrest them, yet they arrest our people for expressing their harmless opinions. So, do northerners mean n...
11/03/2026

The DSS cannot arrest them, yet they arrest our people for expressing their harmless opinions. So, do northerners mean nothing to you? Shame on you. You're evil.

JAMI’AN TSARO NA SHIRIN ZUBAR DA JININ AL’UMMAR MUSULMI A JIHAR KATSINA–Taron Manema Labarai Al’umma na sane da yaƙin da...
10/03/2026

JAMI’AN TSARO NA SHIRIN ZUBAR DA JININ AL’UMMAR MUSULMI A JIHAR KATSINA

–Taron Manema Labarai

Al’umma na sane da yaƙin da ke gudana yanzun haka tsakanin Ƙasar Amerika da Isra’el tare da haɗin bakin wasu daga cikin Ƙasashen Larabawa irin su Saudiyya, Qatar, Bahrain, Jodan da Dubai. Waɗannan Ƙasashe sun haɗa kai suna ta yaƙar Jamhuriyyar Musulumci ta Iran.

Wannan yaƙin ya sanya Duniya ta rabe zuwa gida biyu, Muminai a ƙarƙashin Jagorancin Ƙasar Iran, sai kuma masu goyama Azzalumai baya a ƙarƙashin Jagorancin Ƙasar America da Isra’el da munafikan shugabannin Ƙasashen Larabawa.

Akan hakane Gwamnatin tarayyar Nigeria take taka rawar zama Ƴar amshin Shata ga Ƙasar America da Isra’el, daman ta gayyato waɗannan Ƙasashe zuwa wannan Ƙasar wai da sunan samar da tsaro.
Wannan alaƙa dake tsakanin Gwamnatin Nigeria da ta Isra’el ta baiwa Jakadan Isra’el dake a Nigeria damar zargin Harkar Musulumci a Nigeria ƙarƙashin Jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) da cewa wai tana horas da yara Ƴan Ta’ada.

Sai ga shugaban Ƴan sanda na Ƙasa (IG) ya baiwa Police ummarni akan cewa su sanya idanu da ɗaukar mataki ga duk waɗanda s**a fito s**a nuna goyon baya ga Jamhuriyyar Musulumci ta Iran. Sai muke ganin gamayyar Jami’an tsaron Sojoji da Police sunyi comber ta fiye da motoci Ashirin (20) ɗauke da muggan makamai da motocin yaƙi masu sulke suna ta sunturi a garin Katsina tun tsawon mako ɗaya a wannan Jihar ta Katsina mai fama da rashin tsaro na Bandits, ɓangaren da yafi kamata gwamnati ta maida hankali, Jami’an tsaro ya kamata su kai ɗauki don samar da tsaro, sai s**a ɓuge a cikin gari suna tada hankalin Jama’a suna neman afka ma mutanen da basu da tarihin tada hankali.

Fitowa a nuna goyon baya kuwa ga waɗanda ake zalunta amsa kiran Manzo (S.A.W.W) ne da yake faɗa a Hadisin sa cewa; “Idan Mumini yai yekuwa daga bangon gabas to wajibin Muminin dake a bangon yamma ne ya karɓa masa”. Wannan goyon baya da Addu’o’i shine abinda zamu iya nunawa ga Ƴan' uwanmu Musulmi da ake zalunta.

Kuma Ƙasashen Duniya anata yin Muzaharori sai anan Nigeria ake take wannan ƴancin da Constitution ya rigaya ya bada damar ayi. Don haka mu Ƴan'uwa Musulmi Almajiran Sayyid Ibrahim Zakzaky (H) na Jihar Katsina muna kira da babbar murya ga Gwamnatin Jihar Katsina da duk wasu masu faɗa aji da sauran Jama’a cewa, duk wani abu da s**a ga ya faru a cikin al’umma to su tuhumi da zargi Jami’an tsaron da s**a zaƙu don su shekar da jinin al’umma.

Mun saba gudanar da jerin gwanon Muzaharori daban-daban, muyi mu tashi lafiya sama da shekara Talatin (30) batare da an kashe koda kiyashiba, ko an ɓannata dukiyar kowa ba, Al’ummar Katsina su shedane akan haka.

Don haka, idan anga wani abu yafaru a yanzu daga Jami’an tsaro ne.

Amincin Allah ya tabbata ga masu neman zaman Lafiya.

Daga: Ƴan'uwa Musulmi Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky (H), na Yankin Katsina.

(Talata 21-09-1447/10-03-2026)

Daga Sayyid zuwa ga wani Sayyid ɗin. Daga Ali zuwa ga Mujtaba ɗan Ali. Khomeiniyanci zai ci gaba da wanzuma ko kafirai d...
08/03/2026

Daga Sayyid zuwa ga wani Sayyid ɗin. Daga Ali zuwa ga Mujtaba ɗan Ali. Khomeiniyanci zai ci gaba da wanzuma ko kafirai da munafukai sun ƙi.

–Haj Baqeer

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when SHI'A Nigeria posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to SHI'A Nigeria:

Shortcuts

Share

Category