11/10/2025
Rahotanni sun tabbatar cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da afuwa ga Maryam Sanda, wadda aka yankewa hukuncin kisa a shekarar 2020 bisa tuhumar kashe mijinta, Bilyaminu Bello.
Daga Abubakar Saleh
An bayyana cewa afuwar ta fito ne a cikin jerin mutane da s**a amfana da pardon na shugaban ƙasa bisa shawarar majalisar bada afuwa (Prerogative of Mercy), wanda aka yi a lokacin bikin independence day na 2025.
Maryam Sanda dai ta kasance a gidan yari tun daga lokacin hukuncin kotu, bayan shari’a mai tsawo da ta jawo cece-kuce a fadin ƙasa. Wannan afuwa daga Tinubu na nufin za ta sami ‘yanci daga gidan yari, bayan kusan shekaru biyar da ta shafe a can.
Me za ku ce?e e