29/09/2025
LABARUN DUNIYA
SAM BA GASKIYA BA NE ZARGIN KISAN KARE DANGI GA MABIYA ADDININ KIRISTA-GWAMNATIN NAJERIYA
Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da wasu bayanai daga wasu shafukan labaru na ketare da wasu ma’abota yanar gizo da ke cewa akwai kullalliya ta yin kisan kare dangi ga mabiya addinin kirista a Najeriya.
Ministan labaru Muhammad Idris ya baiyana haka a wata sanarwa, ya na mai cewa labarun sam ba su da tushe b***e madafa.
A nan ministan ya ce gaskiya ne Najeriya k**ar wasu kasashe na fuskantar kalubalen tsaro, amma hakan bai ware wani addini ko kabila ba, fitinar ta shafi kowa.
Ministan ya ce daga watan Mayun 2023 zuwa Febrerun bana, jami’an tsaro na gwamnatin sun hallaka fiye da ‘yan ta’adda 13,000 da kubutar da ‘yan kasa da a ka yi garkuwa da su sama da 10,000.
Don fito da abun fili, minista Idris ya ce masu yada shacifadin su sani cewa shugaban sojoji da na ‘yan sanda duk mabiya addinin kirista.
Muhmmad Idris ya ce gwamnatin shugaba Bola Tinubu na daukar duk matakan da su ka dace wajen kare rayuka da dukiyoyin dukkan ‘yan Najeriya.
KOTU TA HARAMTA KAFA GWAMNATIN SA-IDO A NAJERIYA
Babbar kotun taraiya ta yanke hukuncin haramta yunkurin kafa gwamnatin sa-ido da za ta zama tamkar kishiyar zababbiyar gwamnati.
Wannan ya biyo bayan karar da rundunar tsaron farin kaya ta DSS ta shigar da Farfesan tattalin arzikin siyasa Pat Utomi wanda ke shirya kafa gwamnatin.
Alkalin babbar kotun taraiya James Omotosho ya zaiyana irin wannan gwamnati da cewa ta yi karantsaye ga tsarin shugaba mai cikekken iko na Najeriya.
Omotosho ya zaiyana kafa gwamnatin ta sa-ido da haramtacce kuma shigo da dokokin wasu kasashen ketare ne da babu tsarin a Najeriya.
Gwamnatin sa-ido dai na aiki da shugaban kasa da ministoci tamkar yanda zababbiyar gwamnati ke yi amma ba karfin zartarwa sai dai tsara manufofin adawa da sa ido kan aiyukan gwamnatin da ke kan gado.
Utomi wanda ya taba tsayawa takarar shugaban kasa a jam’iyyar ADC a 2007, ya so nacewa cewa ya na da hurumin kafa gwamnatin bisa dokar fadar albarkacin baki.
A NA NUNA DAMUWA KAN RIKICIN MATATAR DANGOTE DA KUNGIYAR PENGASSAN
A na nuna damuwa kan matsalar da za a samu a sanadiyyar takaddamar kungiyar manyan ma’aikatan fetur da iskar gas PENGASSAN da matatar fetur ta Dangote.
Dambarwar dai ta sa PENGASSAN umurtar hana kai danyen mai da iskar gas zuwa matatar ta Dangote da ke Lagos.
Damuwar ta shafi musamman iskar gas da karancin ta zai haddasa katsewar wutar lantarki na kasa.
PENGASSAN ta bukaci membobin ta su kawo cikas ga lamuran aiki a matatar don nuna fushi kan korar wasu membobin daga aiki.
Kungiyar ta manyan ma’aikatan na fetur da gas ta zargi matatar da daukar matakan da su ka ci karo da dokokin kwadago hakanan da amfani da damar wajen yada bayanan da ba su da inganci.
AMURKA TA BAIYANA SHIRI MAI KARFI NA SAMUN SULHU A YAKIN GAZA
Amurka ta baiyana shiri mai karfi na samun daidaitawar dakatar da yaki a Gaza da ya doshi shekaru 2.
Tuntuni a ka tabbatar da kashe fiye da Falasdinawa 62,000 a Gaza da kuma jefa wasu dubban cikin galabaita.
Trump na magana ne gabanin ganawar sa a litinin din nan da firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a fadar White House.
Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya ce manyan jami’an Amurka na ganawa da Isra’ila da shugabbanin Larabawa don samar da maslaha.
In za a tuna mummunan harin da Isra’ila ta auna kan masu tattaunawar sulhu na Hamas da ita a birnin Doha ya karya guiwar Larabawa inda har Sarkin Katar Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani ya zaiyana Isra’ila da cewa tamkar kasa ce da ke gaba da makwabtan ta.