07/06/2025
Ibtila'in Gobara a Otal ɗin Alhazai da ke Titin Shari Mansur – Babu Wanda Ya Rasa Ransa.
Hukumar Kula da Hajji ta Ƙasa (NAHCON) na mai bakin cikin sanar da al’umma cewa an sami wani hatsarin gobara da ya auku a ɗaya daga cikin otal-otal da ke masaukin alhazai ‘yan Najeriya da ke titin Shari Mansur a birnin Makkah, a yau Asabar, 7 ga Yuni, 2025, da misalin ƙarfe 12 na rana (lokacin Saudiyya).
Otal ɗin da lamarin ya shafa, Imaratus Sanan, yana masaukin alhazai kimanin 484 daga cikin kamfanonin yawon shakatawa guda shida masu zaman kansu na Najeriya. Muna gode wa Allah, babu wanda ya rasa ransa, kuma duka alhazan suna cikin koshin lafiya a Mina. Da sauri jami’an ceto na Saudiyya tare da ma’aikatan otal ɗin s**a taka rawa wajen dakile wutar kafin ta bazu zuwa sauran sassan ginin.
Bayan faruwar lamarin, Shugaban/CEO na NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, tare da Kwamishinan Ƙididdiga, Ma’aikata da Kuɗi (PPMF), Alhaji Aliu Abdulrazak, da Mataimakin Kwamishinan Makkah, Darakta Alidu Shutti, sun ziyarci wurin domin tantance yanayin da alhazan ke ciki da kuma tabbatar da kula da walwalarsu.
A yayin ziyarar, Farfesa Abdullahi ya bayyana damuwarsa tare da bayar da umarnin gaggauta sauya masaukin alhazan zuwa wani sabon wuri. Ya jajanta musu kan abin da ya faru, yana mai tabbatar da cewa Hukumar za ta bayar da dukkan goyon bayan da ya dace domin rage musu radadin lamarin.
Shugaban ya gode wa Allah Madaukakin Sarki da ba a sami asarar rai ba a cikin wannan mummunan lamari. Ya kuma tabbatar da cewa NAHCON na aiki tare da kamfanonin yawon shakatawar da abin ya shafa domin tabbatar da cewa an sauya wa alhazan masauki da kuma samar musu da taimakon da ya dace. Shugaban da tawagarsa sun riga sun duba sabon ginin da aka ware, kuma an kammala shirye-shiryen sauya masaukin alhazan.
Shugaban da Kwamishinan PPMF sun nuna godiya ga saurin amsa kiran gaggawa daga jami’an ceto na Saudiyya da kuma haɗin kai daga ma’aikatan otal ɗin wajen shawo kan lamarin.
Za a ci gaba da sanar da al’umma da zarar an sami sabbin bayanai.
Fatima Sanda Usara
Daraktar Ƙarƙashin Jagora, Sashen Yada Labarai da Wallafe-Wallafe
Domin Shugaban/CEO
NAHCON