03/12/2022
Sun Taba Wakiltar Mu Basuyi Komai Ba, Kuma Yanzu Sun Kawo Wani Suna so Ya Zama Su Bishi Chan Su Anshe Hakkin Al'umma_____ Inji Hon. Malam Ya'u Ahmad Nowa
Shugaban Karamar Hukumar Dandume Jihar Katsina Hon. Malam Ya'u Ahmad Nowa Ya Furta Haka A Yayin Taron Bude Ofishin Yakin Neman Zaben Hon. Barrister Abubakar Ahmad Muhammad (Gardi) Dan Takarar Kujerar Majalisar Wakilai Mai Neman Wakiltar Kananan Hukumomin Funtua Dà Dañdume Jihar Katsina Karkashin Inuwar Jam'iyyar APC, Na Karamar Hukumar Dandume Wanda Masoya Da Magoya Bayansa S**a Gina Domin Bada Tasu Gudummawa, A Ranar Asabar 03/12/2022.
Inda Ya Chigaba Da Cewa, Dan Takarar Da S**a Kawo Bai Iya Bayyana Akwatunan Zaben Dake Mazabar Dantankari, Baisansu Ba, Ballantana Akwatunan Zaben Dake Karamar Hukumar Dandume Ko Funtua, To Ya Za'ayi Mutumin Da Baisan Yankunan Ba, Kuma Yace Zai Waklice Su, Bayan Ko Gida Baidashi A Karamar Hukumar Dandume,
Daga Karshe Ya Chigaba Da Cewa "Kada Ku Yarda Wani Ya Yaudareku Da Maganar Matsalar Tsaro, Domin Tun A Mulkin Jam'iyyar Su Aka Fara, Ni Ina Daya Daga Cikin Wanda Aka Kashe Ma Dan Uwa A Gona Lokachin Mulkinsu, Matsalar Tsaro Bata Da Nasaba Da Jam'iyya, Bace Muyi Addu'ar Allah Yakawo Mana Zaman Lapiya".
Ajawabin Hon. Barrister Abubakar Ahmad Muhammad (Gardi) Ya Bayyana Godiyarsa Ga Al'ummar Kananan Hukumomin Funtua Dà Dañdume Bisaga Amince Da Karamci Da Kyawawan Zato Da Sukeyi Agreshi, Tareda Godiya Ga Al'ummar Da S**a Samu Damar Halaktar Taron Bude Ofishin Yakin Neman Zabensa Daga Karshe Ya Rufe Da Addu'ar Nema Ma Kasa Zaman Lapiya.
Taron Yasamu Halaktar Shugaban Karamar hukumar Dandume Hon. Malam Ya'u Ahmad Nowa Da Shugaban Jam'iyyar APC Alh. Nasiru Garba Da Hon. Muntari Dandutse Wanda Ya Samu Wakilci Alh. Abdu Isah Funtua Da Katukan Katsina Hakimin Dandume Alhaji Jafaru Ibrahim Wanda Yasamu Wakilci Alh. Shamsuddeen Jafar (Mai Garin Jiruwa) Da Hon. Abubakar Wada Nas Funtua Dà Alh. Haruna Abdulrashida Da Alh. Ibrahim Mai Bula, Da Tawagar Kansilolin Karamar hukumar Dandume Da Sauran Maza Da Mata Da Dattijai Da Matasa Yan Gwagwarmaya Yan Asalin Kananan Hukumomin Funtua Dà Dañdume Da Sassan Jihar Katsina Da Kasa Baki Daya.