09/09/2026
Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta damke wani mutum da ake zargi da yin basaja a matsayin jami’in ’yan sanda tare da damfarar masu neman aiki, ta hanyar yi musu alkawarin samar musu da guraben aikin ’yan sanda.
Ana zargin mutumin da amfani da hotunan jami’an ’yan sanda da aka yi wa kwaskwarima ta hanyar fasahar AI, domin ya nuna kansa a matsayin jami’in rundunar tare da ƙara wa ikirarin nasa sahihanci.
A cewar rundunar, wanda ake zargin ya dade yana tuntuɓar mutane tare da neman kuɗi ko wasu bayanai, bisa alkawarin zai taimaka musu wajen samun aikin ’yan sanda.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna, ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.
Sanarwar ta ce bayan rundunar ta samu bayanai kan lamarin, jami’an tsaro s**a gudanar da bincike, wanda ya kai ga cafke wanda ake zargin.
Rundunar ta gargadi jama’a da su yi taka-tsantsan da mutanen da ke neman kuɗi ko bayanan sirri da sunan samar da aikin yi, musamman ta kafafen sada zumunta.
Ta kuma shawarci masu neman aiki da su tabbatar da sahihancin duk wani bayani game da ɗaukar ma’aikata daga hukumomin da abin ya shafa, domin kauce wa fadawa hannun masu damfara.