25/07/2025
Mahadi Shehu ya Soki Gwamnatin Tarayya Kan Kudaden Tsaro, Ya Bukaci Samar da ‘Yan Sanda na Jihohi kuma Shugabanni su Gyara Halayen su
Fitaccen mai sharhi kan harkokin yau da kullum, Dr. Mahadi Shehu, ya bayyana rashin jin daɗinsa kan yadda Gwamnatin Tarayya ke kashe makudan kuɗaɗe a sunan samar da tsaro da zaman lafiya, alhali kuma matsalar na ci gaba da tabarbarewa.
ATP Hausa ta ruwaito cewa ya zargi gwamnati da rashin tallafa wa jami’an tsaro da kayan aiki da albashi, wanda hakan ke rage musu ƙwarin gwiwar yaki da 'yan ta’adda da masu tada zaune tsaye. Dr. Mahadi ya bukaci gwamnonin jihohin Arewa da su ƙara himma wajen samar da rundunar 'yan sandan jiha, ba tare da jiran amincewar Gwamnatin Tarayya ba, yana mai kawo misalin wasu jihohin Kudu da s**a yi nasara a wannan fanni.
Dr. Mahadi ya kuma ce dole ne a sauya dokar da ke cikin kundin tsarin mulki wacce ke hana rundunonin tsaron jihohi mallakar manyan mak**ai. Ya ce wannan doka na hana su samun ƙarfi wajen yaki da ‘yan ta’adda. Ya kara da cewa, “Ko Allah idan ya kafa doka da ta gagari mutane, zai sauya ta don amfanin jama’a,” yana nuni da muhimmancin doka da za ta yi amfani ga rayuwar al’umma.
Da yake magana kan 'yancin kai na Najeriya, Dr. Mahadi ya bayyana cewa 'yancin da ake cewa Najeriya ta samu, kawai a rubuce yake, domin har yanzu mutane na rayuwa cikin wahala k**ar lokacin mulkin mallaka. Ya soki kasashen waje, musamman Birtaniya da ta yi wa Najeriya mulkin mallaka, da cewa ita ce ke karɓar dukiyar haramtacciyar da barayin gwamnati ke sacewa daga Najeriya, suna kuma amfani da ita wajen gina manyan gidaje da otal-otal a kasashen waje.
Dr. Mahadi ya ce, idan har Najeriya na son ta ci gaba k**ar ƙasashen China, Indonesia, Malaysia da Jamus, to dole ne ta koyi yadda suke gudanar da mulki na gaskiya da rikon amana. Ya ce a irin waɗannan ƙasashe, shugabanni ba su halarci sata ko almundahana ba, kuma kafin a zabi mutum a matsayin shugaba sai an bincike shi sosai. A wasu ƙasashen, idan mutum ya saci dukiyar ƙasa, to a kofar gidansa za a kashe shi. A wasu kuma, idan an k**a mutum da laifi, kunya na sa shi kashe kansa. Amma a Najeriya, mafi kwarewa wajen sata shi ake girmamawa da bashi mukami.
A karshe, Dr. Mahadi ya bayyana cewa matsalar tsaro da rashawa a Najeriya ba wai na gwamnati kaɗai ba ne, matsala ce ta kowa da kowa. Ya ce dole ne al’umma su tashi tsaye wajen taimaka wa jami’an tsaro, su daina ɓoye bayanan da za su taimaka a k**a masu aikata laifi. Ya kuma nuna cewa cin hanci da rashawa yana farawa tun daga lokacin zaɓe, inda ‘yan siyasa ke biyan mutane da kuɗi don su samu kuri’a. Ya ce haka na sa shugabanni su mayar da siyasa kasuwanci. Ya ƙara da cewa babu buƙatar sauya kundin tsarin mulki k**ar yadda Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke shirin yi, illa dai shugabanni su gyara halayensu ne.