07/09/2025
CIKIYA! CIKIYA! CIKIYA!
Jama'a, ku taya mu yaɗawa, don Allah.
A na cikiyar ahalin wannan yarinya mai suna Maimuna Shuaibu, wacce aka tsinta yau Lahadi a nan garin Jos, jihar Filato.
Ta ce an sako su a mota ne daga garin Yola dake Jihar Adamawa, kuma basu san inda zasu je ba.
Ta ce ita da ƴan-uwanta uku ne mahaifin su ya sako a Mota, Wanda yanzu haka ba'a san inda sauran ƴan-uwan nata suke ba.
Da wannan ne mu ke yin cikiyar ahalinta ko wani wanda ya santa.
Ku taimaka da SHARE ko Allah zai sa a dace da samun ƴan-uwanta.
Zaku iya tuntuɓar wannan lamba 07015898279 Ko 08133356677 don neman ƙarin bayani a kan inda take.
Allah Ya sa mu dace, amin.