02/11/2025
BA MUSULMI BANE KE KASHE KIRISTOCI
A NAJERIYA. Cewar Gorge Udom Kirista daga Arewacin Najeriya:
Matsalar son addini (Religious Bigotry) ba daga Arewa ta fara ba.
Mu koma baya kadan zuwa shekara ta 1962, lokacin da Musulmin Arewa, Sir Abubakar Tafawa Balewa, ya saka Najeriya cikin Majalisar Ikklisiyoyi ta Duniya (World Council of Churches), sannan a 1963 ya kuma saka ta cikin International Bible Society, babu wani kuka daga Musulman Arewa.
Asabar tana daga cikin ranakun aiki a Najeriya har zuwa shekara ta 1973, lokacin da Gowon, wanda yake Kirista daga ƙananan kabilu na Arewa, ya ayyana ta a matsayin ranar hutu don bai wa Seventh Day Adventist Church damar yin ibada — babu wani kuka daga Musulman Arewa.
A watan Fabrairu na 1979, Olusegun Obasanjo ya hana shahararren mai wa’azin Musulunci, Ahmed Deedat, shiga Najeriya — babu kuka daga Musulman Arewa.
A shekara ta 1982, Pope John Paul II ya ziyarci Najeriya, kuma Musulmi ne, Alhaji Shehu Shagari, ya tarbe shi.
Reinhard Bonnke, malamin Kirista mai wa’azi, yana shigowa Najeriya yadda yake so — babu kuka daga Musulman Arewa.
Abacha ma ya tarbi Pope John Paul, ya kuma kafa Papal Square a kusa da hanyar Kubwa Expressway — babu kuka daga Musulmai.
Amma a 1986, lokacin da Babangida ya saka Najeriya cikin Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi (OIC), sai tarzoma ta tashi a Lagos, Port Harcourt da Enugu — wanda CAN (Christian Association of Nigeria) ta shirya.
Don Allah, wa ne ke nuna son addini a nan?
A ‘yan kwanakin nan, Majalisar Koli ta Harkokin Musulunci ta Najeriya (NSCIA) ta bayyana cewa ba ta da hannu cikin siyasa — amma ya ya da CAN?
A shekara ta 2013, an k**a jirgin sama mallakin shugaban CAN a Afirka ta Kudu cike da kuɗin waje — me da za a ce da jirgin nan idan mallakin Sarkin Musulmi ne?
Don haka mu tambayi kanmu: Su waye masu son addini a gaskiya? Kafin mu sake yin kuskure a matsayin al’umma.