
20/09/2025
Kungiyar United Nigeria Chaplaincy ta Nada Shugaban Shiyyar Jihar Katsina tare da Karrama Sheikh Dr. Isma’il Zakariyya Alkashanawi da Lambar Girmamawa
Kungiyar United Nigeria Chaplaincy (UNC) ta gudanar da babban taron ta na kasa a dakin taro na makarantar KCK da ke Katsina, inda ta sanar da nadin sabon shugaban shiyyar Katsina na kungiyar tare da karrama fitattun mutane da lambar yabo.
Daga cikin waɗanda aka karrama akwai babban malamin addini, Sheikh Dr Isma’il Zakariyya Alkashanawi, wanda ya samu lambar girma ta National Muslim Affair.
A jawabin maraba da ya gabatar, sabon shugaban ƙungiyar a shiyyar Katsina, Malam Bello, ya bayyana farin cikinsa da yadda jama’a s**a halarci taron cikin natsuwa da kwazo, tare da bayyana wasu daga cikin manufofin kungiyar musamman wajen wanzar da zaman lafiya a kasa.
Shi ma da yake nasa jawabin, Dr Isma’il Zakariyya Alkashanawi ya gode wa Allah bisa wannan yabo, tare da bayyana cewa wannan alhaki ne babba da ke bukatar hada kai. Ya kara da cewa:
“Kungiyar tana bukatar matasa, malamai, da ‘yan siyasa su bada gudummawar su domin kara tabbatar da ci gaban kungiyar da kuma wanzar da zaman lafiya a cikin al’umma.”
Hakazalika, Alaramma Malam Kalu ya yi kira ga masu hannu da shuni da su tallafa wa tafiyar kungiyar, domin ganin an cimma burin tabbatar da zaman lafiya.
Shi ma Rev. Luka Yohana wanda aka tabbatar dashi a matsayin Uban ƙungiyar, ya nuna jin dadinsa tare da kira ga jama’a da su hada kai wajen inganta zaman lafiya da hadin kai a kasa.
Daga karshe, an karrama wasu fitattun shugabanni da ‘yan siyasa, ciki har da Hon. Aliyu Abubakar Albaba, dan majalisar da ke wakiltar karamar hukumar Katsina, Ambassador Khadija Sulaiman Saulawa, Alaramma Malam Habibu ƙalu da sauran shugabannin al’umma.
Nigerian Post ta bibiyi cewa, taron dai ya samu halartar jami'an gwamnati, jami’an tsaro, malamai, da shugabannin kungiyoyin al’umma maza da mata, lamarin da ya nuna cikakken hadin kai wajen tallafa wa ci gaban kasa da raya zaman lafiya.