31/07/2025
Duk wanda ya yi silar buɗe idon wani Allah kaɗai ne yasan irin ladar da zai Shimfiɗa ma sa- Inji Isah Muhammad Mai'adua
Ya bayyana haka a lokacin da ake horar da jami'an lafiya a matakin farko (Primary Health Workers) inda ake ɗaukar kowanne mutum ɗaya a cikin mazaɓu 361 na sassan Katsina, a wasu daga cikin al-ummar Katsina ta tsakiya a ranar Laraba 30 ga watan Yuli 2025 a jihar Katsina.
Tun da farko dai, ma'aikatar lafiya ta jiha, ta shirya bada horon na kwana 2 kan kula da lafiyar Idanu a matakin farko (PRIMARY EYE CARE) a Katsina ta tsakiya.
Wanda Gwamnatin jihar Katsina, a ɓangaren Ma'aikatar lafiya ta jiha, ta shirya bada horon na kwana 2 kan kula da lafiyar Idanu a matakin farko (PRIMARY EYE CARE) a Katsina ta tsakiya, bayan sun kammala kwana 2 kan bada horo a Shiyya Funtua.
An gudanar da taron a mazaɓar Gabas 01 dake cikin Shiyyar Katsina ta tsakiya, wanda kafin fara gudanar da horaswar, jami'an sun tsara cewa, daga kowacce mazaɓa sun ɗauki mutum ɗaya, daga cikin Mazaɓu 361 dake jihar Katsina, domin ba su horo kan inganta lafiyar idanu.
Kazalika, horon wanda aka fara bi Shiyyar Funtua don bada horo, tare da kammalawa da Shiyyar Funtua, inda ya zuwa yanzu ake ci gaba da gudanarwa a Katsina ta tsakiya, da kuma Shiyyar Daura nan ba da jimawa ba.
Nigerian Post ta samu cewa, tunda farko, Kwamishinan Lafiya na jihar Katsina, Hon. Musa Adamu Funtua, shi ne ya umarci jami'an da su ɗauki Mutum ɗaya kowacce mazaɓa don ganin shirin ya inganta a sassan jihar.
Ya shaida ma su da su kasance masu bin kanun abubuwan da aka koyar da su, tare da bada ilimin da aka ba su ga al'ummar jihar Katsina don ganin kwalliya ta biya kuɗin sabulu.
Shirin horaswar wanda gwamnatin jihar Katsina ta ɗauki nauyi, ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umaru Raɗɗa, za a kammala nan ba da daɗewa ba a jihar Katsina.
Ana horar da jami'an lafiya a matakin farko (Primary Health Workers) inda ake ɗaukar kowanne mutum ɗaya a cikin mazaɓu 361 na sassan Katsina.
Horon ya samu kulawar; Perm Sect, Dr. Ahmed Tijjani Hamza da Director Public Health, Dr. Ma'awuya Aliyu, da kuma Director Planning SPHCA,Dr. Ibrahim Nalado, da sauran su.