04/08/2026
Ana fargabar cewa aƙalla mutane 21 sun rasa rayukansu, yayin da 37 aka yi garkuwa da su, sakamakon wani mummunan h@ri da wasu 'yan b!ndiga masu ɗauke da m@kamai s**a kai a ƙauyen Tsamaye da ke Ƙaramar Hukumar Sabon Birni a jihar Sokoto.
Rahotanni sun ce maharan sun mamaye ƙauyen ne da m@kamai masu yawa, inda s**a k@she mutane tare da yin awon gaba da wasu da dama. Harin ya kuma tilasta wa dubban mazauna yankin tserewa daga gidajensu domin neman mafaka.
Majiyoyi daga yankin sun bayyana cewa h@rin ya haifar da f!rgici da t@shin h@nkali, yayin da iyalai da dama s**a rasa 'yan uwansu ko kuma aka raba su da gidajensu.
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, jami'an tsaro ba su fitar da cikakkiyar sanarwa kan adadin waɗanda s**a mutu ko kuma matakan da ake ɗauka ba. Ana ci gaba da gudanar da bincike tare da ƙoƙarin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su.
Lamarin ya sake nuna irin ƙalubalen tsaro da al'ummomin yankin Arewa maso Yammacin Najeriya ke ci gaba da fuskanta sakamakon hare-haren 'yan bindiga.
Sarauniya Radio - Kafar Al'umma