
05/07/2025
Na yi takaicin rashin musuluntar Michael Jackson-
"In ji Jermaine (Yayan Michael jackson)
A Wata Hira Da BBC a Ranar 23 Ga Watan Yuni 2010 Yau Shekaru (14)
A wata hira ta musamman da yayi da BBC, Jermaine Jackson, ya ce da Michael Jackson ya shiga musulunci, da bai samu kansa a wancan hali ba, abinda har ya yi sanadiyyar rasuwar sa.
"Yace kodayaushe nakan yi takaicin cewa ban samu damar ceto rayuwar sa ba".
Ga dai yadda hirar tasa da BBC ta kasance:
BBC: To ko menene dalilinka?
Jermaine: Idan da Michael Jackson ya shiga musulunci, da tuni yana raye. Saboda idan kana da yakini a kan abinda kake aikatawa da kuma wadanda suke kewaye da kai, to lallai rayuwarka za ta inganta, domin Allah zai taimake ka.
Ya kara da cewa yana karanta litattafai da dama, na sayo masa wasu daga Saudi Arabiya da kuma Bahrain. Ni ne na fara kai shi Bahrain saboda ina so ya bar Amurka domin rayuwar Amurka na jefa shi cikin mawuyacin hali.
BBC: Sai dai bai so ya shiga musuluncin ba ko kuwa?
Jermaine: Ba wai ba ya so ya shiga musulunci bane. Duka masu gadinsa musulmai ne saboda ya amince da musulunci, kuma ganin wadannan mutane tare da shi zai taimaka Allah ya bashi kariya ko don saboda su.
BBC: Shin ko ka yarda da zargin da aka yi masa na cin zarafin yara?
Jermaine: Ai kotu ta wanke shi game duk wadannan zarge-zargen. Yaron da ake magana a kansa Jordan Chandler ya ce bai taba taba shi ba. Abinda ya sa kuma mahaifinsa ya kashe kansa.
Kuma da wannan ne kafafen yada labarai s**a yi ta zuzuta lamarin suna s**ar dan uwana a kan abinda bai aikata ba, kuma har yanzu wasu ba su amince da hakan ba.
Ya ce kaunar da aka nunawa dan uwana lokacin da ya rasu, ita ya k**ata a nuna masa lokacin da yake raye. Hukumar bincike ta FBI a Amurka ta bincike shi har na tsawon shekaru 17, amma ba ta same shi da wani laifi ba.
Sai daga baya s**a zo suna yabonsa, a gani na irin wannan yabon ya k**ata su nuna masa tun yana raye, kuma da hakan ya karfafa masa zuciya.
BBC: To ko yaya rayuwa take bayan mutuwa