Hausa Daily News

Hausa Daily News Sahihan Labarai

AN KASHE UBANGIDAN TURJI KACALLA ƊANBOKOLO A ZAMFARAGwamnatin Zamfara ta bayyana cewa jami’an sa-kai sun kashe wani riƙa...
01/07/2025

AN KASHE UBANGIDAN TURJI KACALLA ƊANBOKOLO A ZAMFARA

Gwamnatin Zamfara ta bayyana cewa jami’an sa-kai sun kashe wani riƙaƙƙen ɗan bindiga da ya addabi wasu yankunan jihar mai suna Kacalla Ɗanbokolo.

Mai bai wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro, Ahmad Manga wanda ya tabbatar da hakan ya bayyana kisan Ɗanbokolo a matsayin gagarumin nasara a yaƙi da matsalar tsaro.

“Ɗanbokolo mutum ne da ya fi Bello Turji fitina, ya fi Turji aikata miyagun laifuka, illa kawai shi Turji sunansa da ya karaɗe kafofin yaɗa labarai,” in ji Ahmad Manga.

“Mutanensa da aka kashe sun haura 100, saboda haka wannan gagarumar nasara ce a gare mu,” in ji Manga.

Ya bayyana cewa Kacalla Ɗanbokolo ya rasa ransa a wata arangama a ƙauyen Kurya, tsakanin jami’an sa-kai na Gwamnatin Jihar Zamfara da mayaƙan ɗan bindigar.

Bayanai sun ce Ɗanbokolo ya shafe shekaru masu yawa yana kai hare-hare yankunan Jihar Zamfara tare da sace mutane domin neman kuɗin fansa.

Riƙaƙƙen ɗan bindigar ya gamu da ajalinsa ne tare da wasu ɗimbin mayaƙansa a lokacin da jami’an tsaron sa-kai -— da Gwamnatin Zamfara ta samar.

Mazauna yankin na kallonsa a matsayin mutum marar imani da tausayi da ya addabi yankunansu, ta hanyar kai hare-hare da kisan mutane.

“Shi mutum ne da bai yarda da sulhu ko ta wane hali ba, hatta ɗan uwansa Bello Turji ya taɓa nuna alamun amincewa da sulhu, amma shi wannan bai taɓa nuna hakan ba”, k**ar yadda wani mazaunin yankin ya bayyana wa BBC.

Wannan ne karo na biyu da jami’an tsaro ke kashe riƙaƙƙun ’yan bindiga da ake gani a matsayin iyayen gida da Bello Turji.

Ana iya tuna cewa, a watan Satumban 2024 ne jami’an sojojin Nijeriya s**a kashe Halilu Sububu, wanda shi ma ubangida ne ga Bello Turji a wani kwantan ɓauna da s**a yi masa tare da mayaƙansa.

DANGOTE YA RAGE FARASHIN LITAR MAI ZUWA ₦840Matatar man Dangote ta rage farashin litar mai a depot daga ₦880 zuwa ₦840.A...
01/07/2025

DANGOTE YA RAGE FARASHIN LITAR MAI ZUWA ₦840

Matatar man Dangote ta rage farashin litar mai a depot daga ₦880 zuwa ₦840.

An tabbatar da raguwar farashin ne a cikin wani sabon bayani da kakakin matatar man Dangote , Tony Chiejina ya bayar ranar Litinin.

Chiejina ya ce sabon farashin ya fara aiki ne a ranar Litinin, 30 ga watan Yuni, 2025, kimanin mako guda bayan da matatar man da ke Legas ta yi watsi da farashin a depot na litar man fetur zuwa ₦880.

Ana sa ran gidajen mai irin su MRS Oil & Gas, Ardova Plc, Heyden, da sauran su da s**a kulla yarjejeniya ta musamman da matatar Dangote za su rage farashin famfunan su zuwa kasa da ₦900.

Rage ₦40 din ya biyo bayan faduwar farashin man fetur a ranar Litinin yayin da ake samun sassaucin rikicin Gabas ta Tsakiya na tsawon makonni biyu tsakanin Isra'ila da Iran.

Tsagaita wuta tsakanin kasashen biyu ya sa danyen mai ya fadi da cent 16, ko kuma 0.24%, kan dala 67.61 daga kusan dalar Amurka 80 akan ganga.

30/06/2025

KALLI BIDIYON YADDA JAMI'AN TSARO S**A RIKA FITAR DA MUTANE DAGA SAKATARIYAR PDP DA ABUJA

JAMI'AN TSARO SUN TARWATSA TARON PDPJami’an tsaro da aka tura Sakatariyar babbar jam’iyyar adawa ta PDP sun hana mambobi...
30/06/2025

JAMI'AN TSARO SUN TARWATSA TARON PDP

Jami’an tsaro da aka tura Sakatariyar babbar jam’iyyar adawa ta PDP sun hana mambobin kwamitin amintattu gudanar da taronsu a hedikwatar jam’iyyar.

Har zuwa lokacin gabatar da wannan rahoto, an ga wasu daga cikin ‘yan jam'iyar suna tattaunawa a kan halin da ake ciki a hedikwatar jam’iyyar.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an umurci jami’an tsaro da su tabbatar da cewa ba'a gudanar da taro a hedkwatar jam’iyyar ba.

Jami’an da ke da ba'a bayyana adadinsu ba sun kutsa kai cikin dakin taron da ya k**ata a gudanar da taron inda s**a bukaci wadanda s**a halarci taron su fice.

wasu majiyoyi sun kwarmato yadda aka ji wani babban jami’i yana shaida wa wadanda ke karkashinsa cewa su tabbatar kowa ya bar wajen.

"Ku tabbata babu kowa a zauren da ke can, umarnin kenan, na ji akwai wani zauren da ke sama, ka tabbata babu wanda zai ci gaba da zama a wurin," in ji shi.

Jam’iyyar PDP dai ta fada cikin rikici tun bayan gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa a zaben 2023 inda kusan dukkan sassan s**a rabu gida biyu.

Rikicin baya-bayan nan kan wanene Sakataren jam’iyyar na kasa ya haifar da rudani, inda mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa Ambasada Umar Damagum da mataimakin shugaban a Kudu Taofeak Arapaja ke jagorantar bangarorin kwamitin gudfanarwa na jam’iyyar.

ZARGIN BATA SUNA: SANATA NATASHA TA ISA KOTU A ABUJA Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta isa babban kotun tarayya Abuja do...
30/06/2025

ZARGIN BATA SUNA: SANATA NATASHA TA ISA KOTU A ABUJA

Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta isa babban kotun tarayya Abuja domin gurfanar da ita a gaban kotu.

An gurfanar da ita a gaban kotu a karo na biyu kan zargin bata sunan shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Sanata Natasha ta samu rakiyar mijinta, Emmanuel Uduaghan; mai fafutuka Aisha Yesufu; da magoya bayanta.

BADARU YA JAGORANCI TAWAGAR GWAMNATI WAJEN DOMIN JANA'IZAR AMINU DANTATAWata tawaga daga gwamnatin Najeriya ta isa ƙasar...
30/06/2025

BADARU YA JAGORANCI TAWAGAR GWAMNATI WAJEN DOMIN JANA'IZAR AMINU DANTATA

Wata tawaga daga gwamnatin Najeriya ta isa ƙasar Saudiyya domin jana'izar marigayi, fitaccen ɗan kasuwa kuma dattijo, Alhaji Aminu Alhassan Dantata a birnin Madina.

Marigayi Dantata ya rasu ne a Abu Dhabi, babban birnin Hadaddiyar Daular Larabawa, a ranar Asabar yana da shekara 94.

Tawagar ta bar Najeriya da yammacin Lahadi, inda ta isa Madina da safiyar Litinin.

Tawagar na ƙarƙashin jagorancin ministan tsaro kuma tsohon gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar.

Sauran mambobin tawagar sun haɗa da ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi (SAN) da ministan yaɗa labarai, Alhaji Mohammed Idris, da ƙaramin ministan gidaje da raya birane, Hon. Yusuf Abdullahi Ata da dai sauran su.

Akwai kuma manyan malamai a cikin tawagar da s**a haɗa da sheikh Aminu Daurawa da Dr Bashir Aliyu Umar da kuma Khalifa Abdullahi Muhammad.

YAU ZA A YI JANA’IZAR AMINU DANTATA A MADINAA ranar Litinin din nan za a gudanar da Sallar Jana’izar hamshakin attajiri,...
30/06/2025

YAU ZA A YI JANA’IZAR AMINU DANTATA A MADINA

A ranar Litinin din nan za a gudanar da Sallar Jana’izar hamshakin attajiri, Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu a birnin Dubai na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

Alhaji Aminu Dantata, wanda ke matsayin kaka ga attajirin Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ya rasu ne bayan rashin lafiya yana da shekaru 94.

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa Majalisar Malaman Jihar Kano, ta gudanar da sallar jana’izar marigayin ba tare da gawar ba a ranar Asabar, a Masallacin Dangi da ke Kundila Kano. Sallar ta samu halartar dubban jama’a da shugabanni daga ciki da wajen Kano.

Hakan kuwa ta faru ne bayan iyalan marigayin sun sanar bayan rasuwarsa cewa ya bar wasiyya cewa a idan Allah Ya dauki rayuwarsa, binne shi a birnin Madina ta Kasar Saudiyya.

A ranar Lahadi, Sakatarensa, Mustapha Junaid, ya sanar cewa hukumomin Kasar Saudiyya sun bayar da izinin kai gawar Alhaji Aminu Dantata kasar domin yin jana’iza da binne shi a Madina, k**ar yadda marigayin ya bar wasiyya.

Alhaji Aminu Dantata, wanda ya shahara da taimakon jama’a da ayyukan addini ne, fitaccen dan kasuwa ne a duniya, kuma tsohon dan siyasa kuma ma’aikacin gwamnati.

Tuni manyan shugabannin Nijeriya da na kasashen duniya s**a fara yi wa birnin Madina na Kasaa Mai Tsarki tsinke, tare da tawagawar Gwamnatin Tarayya da gwamnoni da sarakunna da manyan malaman Musulunci domin halartar jana’izar.

Tun bayan rasuwar Aminu Dantata shugabanni da ’yan kasuwa da daidaikun jama’a daga bangarori daban-daban suke ta tururuwar yin ta’aziyya tare da bayyana halayensa na gari da irin gudummawar da ya bayar wajen kawo ci gaba da samar da sauki ga rayuwar al’umma.

SOJOJI SUN YIWA 'ƳAN BINDIGA RUWAN WUTA A NEJARundunar Sojan Saman Najeriya sun ƙaddamar da gagarumin farmakin sama kan ...
27/06/2025

SOJOJI SUN YIWA 'ƳAN BINDIGA RUWAN WUTA A NEJA

Rundunar Sojan Saman Najeriya sun ƙaddamar da gagarumin farmakin sama kan sansanonin ‘yan bindiga a jihar Neja a ranakun Laraba da Alhamis, a wani yunƙuri na kawar da ƴan fashin da s**a kai hari kan dakarun ƙasar a baya-bayan nan.

Wata sanarwa da rundunar sojin saman ta wallafa a shafinta na sada zumunta ta ce an kai harin ne ƙarƙashin shirin FANSAN YAMMA "domin kawar da barazanar tsaro da 'yan ta’adda ke haifarwa.

"A ranar 26 ga watan Yuni, bayan samun bayanan sirri, rundunar sojin saman Najeriya, bayan haɗa gwiwa da sauran jami'an tsaro ta gano ayyukan ƴan bindiga da s**a hada da satar shanu a yankin Kakihun da Kumbashi," in ji sanarwar wadda ta samu sa hannu daraktan yaɗa labarai na rundunar Air Commodore Ehimen Ejodame.

"Nan take rundunar ta ƙaddamar da hare-haren da s**a yi sanadin kashe ƴan fashin daji da dama, lalata kayan aikinsu da kuma hana su haɗuwa," k**ar yadda sanarwar ta bayyana.

A cikin makon nan ne aka samu rahotannin da s**a ce ƴan fashin daji a jihar ta Neja, arewa maso tsakiyar Najeriya sun kai samame a wasu sansanonin sojin Najeriya inda s**a kashe jami'an soji "aƙalla 17".

Wata sanarwa da rundunar sojin ƙasa ta Najeriyar ta fitar ta tabbatar da kai harin sai dai ba ta yi bayani kan yawan sojojin da s**a rasa rayukansu ba sanadiyyar farmakin.

Jihar Neja na cikin jihohin Najeriya masu fama da matsalar tsaro, inda ƴan bindiga s**a tarwatsa ƙauyuka da dama, lamarin da ya haifar da asarar ɗimbin rayuka da kawo cikas ga ayyukan tattalin arziƙi.

RIVERS: ZA'A MAYAR DA FUBARA KAN KUJERAR GWAMNA BISA SHARADIN BA ZAI NEMI TAZARCE BA - RAHOTOShugaban Ƙasa Bola Ahmed Ti...
27/06/2025

RIVERS: ZA'A MAYAR DA FUBARA KAN KUJERAR GWAMNA BISA SHARADIN BA ZAI NEMI TAZARCE BA - RAHOTO

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da mayar da Siminalayi Fubara a matsayin Gwamnan Jihar Rivers — amma da sharadin cewa ba zai sake tsayawa takarar shugabancin jihar a 2027 ba, k**ar yadda rahoton TheCable ya bayyana.

An cimma wannan yarjejeniya ne a wani taro da aka gudanar a daren Alhamis a fadar shugaban ƙasa, inda Tinubu ya karɓi bakuncin Nyesom Wike, Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT); Gwamna Fubara; Martin Amaewhule, shugaban majalisar dokokin jihar da aka dakatar; da wasu ‘yan majalisa.

Majiyoyin fadar shugaban ƙasa sun bayyana wa TheCable cewa wannan mataki wani ɓangare ne na ƙoƙarin da ake yi don dawo da tsarin dimokuraɗiyya a Jihar Rivers, kuma yana kunshe da gagarumin yarjejeniya da sauye-sauye.

Bisa bayanan da s**a fito daga cikin masu ruwa da tsaki, ɗaya daga cikin muhimman sharuɗɗa shi ne a ba Fubara damar kammala wa’adinsa na shekaru huɗu, amma ya hakura da kowanne yunƙuri na neman wa’adi na biyu a 2027 — wani mataki da zai rage masa ƙarfi a siyasa, amma ya amince da shi.

Wata majiya ta bayyana cewa a cikin yarjejeniyar, Wike zai sami damar zaɓar dukkan shugabannin ƙananan hukumomi guda 23 na jihar.

Majiyar daga fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa hakan zai ba Wike babbar dama a siyasa, musamman wajen riƙe ikon siyasa daga tushe a matsayin Ministan Abuja.

Jaridar TheCable ta kuma gano cewa Fubara ya amince da biyan dukkan hakkokin da ake bi na ʼyan majalisar jihar guda 27 da s**a goyi bayan Wike waɗanda aka dakatar.

A sak**akon haka, ‘yan majalisar ba za su ƙaddamar da yunƙurin tsige Fubara daga mukaminsa ba.

IRAN TA K**A MUTANE 6 KAN ZARGIN LEKEN ASIRI GA ISRA'ILAKasar Iran ta k**a mutane shida kan zargin kasancewa ’yan leken ...
24/06/2025

IRAN TA K**A MUTANE 6 KAN ZARGIN LEKEN ASIRI GA ISRA'ILA

Kasar Iran ta k**a mutane shida kan zargin kasancewa ’yan leken asiri ga Isra’ila.

Rahotannin kafofin watsa labarai na ƙasar Iran sun nuna cewa mutanen shida suna leken asiri ne ga hukumar leken asiri ta Isra’ila, Mossad, kuma an k**a su ne a lardin Hamadan da ke yammacin kasar.

Ali Akbar Karimpour, wani jami’in Rundunar Juyin Juya Halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa an k**a “‘yan cin amanar ƙasar,” ne a garuruwan Hamadan, Razan, da Nahavand a cikin lardin.

Ya kara da cewa ana zargin su da gudanar da ayyukan ta intanet da nufin haifar da tashin hankalin jama’a, ɓata sunan gwamnatin Iran, da kuma gurɓata sunanta.”

Iran ta k**a mutane da dama kuma ta kashe wasu da dama saboda leƙen asiri ga Isra’ila tun bayan fara yaƙinta da Isra’ila.

NNPCL YA ƘARA FARASHIN LITAR MAN FETURKamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin litar mai daga naira 910 zu...
24/06/2025

NNPCL YA ƘARA FARASHIN LITAR MAN FETUR

Kamfanin man fetur na Najeriya, NNPCL ya ƙara farashin litar mai daga naira 910 zuwa naira 945 a gidajen mansa da ke Abuja, babban birnin ƙasar.

Haka kuma kamfanin ya ƙara farashin litar mai a gidajen mansa da ke Legas daga naira 870 zuwa 915, k**ar yadda rahotanni s**a nuna.

Wannan ƙarin ya nuna an ƙara naira 35 a kowace lita a Abuja, da kuma ƙarin naira 45 a Legas.

Jaridar Daily Trust mai zaman kanta ta ruwaito cewa tuni wasu gidajen man s**a fara sayar da fetur ɗin a sabon farahi, inda ta ruwaito gidan man NNPCL da ke babbar hanyar Fin Niger Badagry ya fara sayar da man a naira 915.

Haka kuma a gidan man kamfanin NNPCL da ke yankin Kubwa na Abuja, tuni aka fara sayar da man a naira 945.

Shahararriyar ‘yar jarida Bilkisu Babangida ta rasu.Yar jaridar ta shafe shekaru da dama ta na aiki da sashen Hausa na B...
24/06/2025

Shahararriyar ‘yar jarida Bilkisu Babangida ta rasu.

Yar jaridar ta shafe shekaru da dama ta na aiki da sashen Hausa na BBC.

Address

Fct

Telephone

+2348124905058

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Daily News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausa Daily News:

Share