Hausa Daily News

Hausa Daily News Sahihan Labarai

26/08/2025

KALLI BIDIYON YADDA JIRGIN KASAN ABUJA ZUWA KADUNA YAYI HATSARI A YAU TALATA 26/08/2025

JIRGIN KASAN ABUJA ZUWA KADUNA YAYI HATSARIFasinjoji sun tsallake rijiya da baya bayan da jirgin kasan da suke ciki a ha...
26/08/2025

JIRGIN KASAN ABUJA ZUWA KADUNA YAYI HATSARI

Fasinjoji sun tsallake rijiya da baya bayan da jirgin kasan da suke ciki a hanyar Kaduna zuwa Abuja ya yi hatsari da su a safiyar Talata.

Wani daga cikin fasinjan da ke cikin jirgin kasan ya bayyana cewa jirgin ya sauka daga kan layin dogo, lamarin da ya sa wasu daga cikin taragonsa mirginawa.

Kawo yanzu dai babu bayanai game da musabbabin hatsarin jirgin kasan, ko mutanen da s**a samu rauni da makamantansu..

13/08/2025

Kalli yadda Shugaba Tinubu ya shiga taron majalisar zartarwa ta ƙasa (FEC) a yau Laraba, 13 ga Agusta, 2025

AN SAKE SAMUN AMBALIYAR RUWA A MAIDUGURIMazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno sun tsere daga gidan...
30/07/2025

AN SAKE SAMUN AMBALIYAR RUWA A MAIDUGURI

Mazauna wasu yankuna a Maiduguri, babban birnin jihar Borno sun tsere daga gidanjensu bayan wata mummunar ambaliya ta auka wa wasu sassan birnin sakamakon ruwan sama mai ƙarfin gaske.

Rahotonni daga birnin sun ce lamarin ya shafi unguwannin Damboa road da Moduganari Ngomari da Bulunkutu Abuja da sauransu.

An dai wayi gari da mamakon ruwan sama a faɗin birnin, lamarin da ya haifar da ambaliyar.

A shekarar da ta gabata ne aka samu wata mummunar ambaliya da ta raba fiye da mutum miliyan guda da muhallansu a birnin na Maiduguri.

ABDULKADIR IBRAHIM BELLO YA ZAMA SARKIN GUSAUGwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibr...
29/07/2025

ABDULKADIR IBRAHIM BELLO YA ZAMA SARKIN GUSAU

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da naɗin Alhaji Abdulkadir Ibrahim Bello a matsayin sabon Sarkin Katsinan Gusau.

Alhaji Abdulkadir zai ɗare karagar ne a matsayin Sarki na 16 na masarautar, inda zai maye gurbin mahaifinsa, Marigayi Mai martaba Dr. Ibrahim Bello, wanda ya rasu a ranar 25 ga watan Yulin 2025.

Sakataren gwamnatin jihar Zamfara, Malam Abubakar Mohammad Nakwada ne ya bayyana haka a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Suleman Ahmad Tudu ya fitar, inda ya ce an yi amfani da dokoki da tanade-tanaden doka ne wajen amincewa da naɗin wanda masu zaɓen sarkin masarautar s**a zaɓa.

Sabon sarkin ne babban ɗan marigayin, kuma kafin naɗa shi sarki, shi ne Bunun Gusau.

Gwamna Lawal ya taya sabon sarkin murna, sannan ya yi kira gare shi da ya yi koyi da magabatansa, musamman ganin shi tsatson Malam Sambo Ɗan Ashafa ne.

Ya kuma yi kira ga sabon sarki ya dage wajen kira da samun haɗin kai da ci gaban masarautar Gusau da jihar, da ma ƙasar baki ɗaya.

Kalli Hotunan Yadda Mataimakiyar Gwamnan Kaduna Dakta Hadiza Balarabe Ta Tarbi iyalan Tsohon Shugaban Kasa Marigayi Muha...
28/07/2025

Kalli Hotunan Yadda Mataimakiyar Gwamnan Kaduna Dakta Hadiza Balarabe Ta Tarbi iyalan Tsohon Shugaban Kasa Marigayi Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Buhari da Yusuf Buhari a Kaduna.

KOTU TA DAURE G. FRESH SABODA WATSA KUDI Babbar kotun Tarayya mai lamba daya dake jihar Kano ta gurfanar da jarumin tik ...
24/07/2025

KOTU TA DAURE G. FRESH SABODA WATSA KUDI

Babbar kotun Tarayya mai lamba daya dake jihar Kano ta gurfanar da jarumin tik tok Abubakar Ibrahim wanda aka fi sani da G. Fresh a gaban ta bisa zarginsa da cin mutuncin takardar Naira.

Bayan Karanta masa nan take ya amsa laifinsa.
kuma Kotun bata yi wata-wata ba ta aike dashi zuwa gidan gyaran hali na tsawan wata biyar ko yabiya tarar Naira dubu dari biyu.

An dai same shi da laifin watsa takardun Naira dubu dubu a shagon Rahama Sa'idu dake yankin Tarauni yayin da suke nishadi a junansu.

MAWAKI HAMISU BREAKER ZAI KWASHE WATANNI 5 A KURKUKUHukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta gurfanar da Shahararren...
24/07/2025

MAWAKI HAMISU BREAKER ZAI KWASHE WATANNI 5 A KURKUKU

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC ta gurfanar da Shahararren Mawaki Hamisu Breaker a gaban kotun Tarayya karkashin jagorancin mai shari'a Sale Musa Shuaibu bisa zargin cin mutuncin Kudi.

Bayan karanto masa laifin nan take ya amsa, wanda hakan yasa kotun ta yanke masa hukuncin daurin wata biyar ko biyan tarar Naira dubu dari biyu.

Kotun ta sameshi da laifin watsa takardun Naira 200 har na 30,000 a wani gidan biki a Hadejan Jihar Jigawa.

AKWAI YUWUWAR NENTAWE YA ZAMA SABON SHUGABAN APC NA ƘASAMatuƙar ba a samu sauyin tsare-tsare ba, akwai yiwuwar Ministan ...
24/07/2025

AKWAI YUWUWAR NENTAWE YA ZAMA SABON SHUGABAN APC NA ƘASA

Matuƙar ba a samu sauyin tsare-tsare ba, akwai yiwuwar Ministan Jin-ƙai da Yaƙi da Talauci, Farfesa Nentawe Yilwatda ya zama sabon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa a yau Alhamis.

Majiyoyi da dama a daren jiya sun shaida wa Aminiya cewa Nentawe ne ke kan gaba a cikin mutanen da ake so su ɗare shugabancin jam’iyyar mai mulki.

Sai dai a cewar wasu majiyoyin, tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Umaru Tanko Almakura, shi ma na daga cikin waɗanda ake duba yiwuwar bai wa kujerar.

A daidai lokacin da ya rage ’yan sa’o’i gabanin taron Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar, majiyoyi da dama sun shaida cewa shugabancin jam’iyyar, wanda ya ƙunshi Shugaban Ƙasa da Gwamnoni sun yanke shawarar taƙaita neman wanda zai hau kujerar tsakanin Nentawe da Almakura.

Nentawe dai ɗan asalin Jihar Filato ne, da ke shiyyar Arewa da Tsakiya, yankin da aka tsara zai fitar da shugaban jam’iyyar kafin daga bisani aka naɗa tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, wanda ya ajiye muƙaminsa a farkon wannan watan.

Sai dai majiyoyin sun ce an saka sunan Almakura ne a matsayin zaɓi na biyu.

Tun bayan saukar Ganduje dai ’yan shiyyar Arewa ta Tsakiya ke ta hanƙoron ganin an dawo da kujerar yankinsu, kasancewar ɗan cikinsu, wato Sanata Abdullahi Adamu ne ke kanta kafin ya sauka bayan nasarar Shugaba Tinubu a zaɓen 2023.

Bayanai sun nuna sai da aka yi dogon nazari kafin a yanke shawarar fauko ɗan yankin kuma Kirista, saboda a haƙurƙurtar da waɗanda zaɓin Musulmai guda biyu, Tinubu da Kashim, ya baƙantawa rai.

Duk wanda ya yi nasarar dai shi ne zai karɓi ragamar da shugabanta na riƙo na yanzu, Ali Bukar Dalori, wanda mataimakin shugaba ne kafin saukar Ganduje.

Wasu dai na cewa da shi aka ƙyale ya ci gaba, amma wata majiyar ta ce kasancewarsa daga jiha ɗaya da Shettima sannan kuma Tinubu na so a yi ta ta ƙare kan batun shugabancin ya sa dole a zaɓo wani.

Wata majiyar kuma ta ce, “Tinubu na san wani ɗan-a-mutun shi ya zama shugaban kamar yadda Abdullahi Adamu ya kasance zamanin Buhari”.

Sauran waɗanda a baya aka yi ta raɗe-raɗin za su hau kujerar sun haɗa da Sanata Sani Musa (Neja) da Sanata Salihu Mustapha (Kwara) da Sanata Joshua Dariye (Filato) da Sanata George Akume (Binuwai) da kuma Sanata Abu Ibrahim (Katsina).

23/07/2025

KALLI YADDA JAMA'AR GARI S**A KONA KEKE-NAPEP DIN BARAYIN WAYA A KANO

AN SALLAMI GWAMNA DIKKO RAƊA DAGA ASIBITIAn sallami gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, daga asibiti bayan a...
23/07/2025

AN SALLAMI GWAMNA DIKKO RAƊA DAGA ASIBITI

An sallami gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, daga asibiti bayan an tabbatar da ya samu sauƙi daga raunin da ya samu sakamakon hatsarin mota a hanyarsa daga Katsina zuwa Daura.

Gwamnan ya samu kulawa ta musamman daga masana lafiya, kuma yanzu an tabbatar da cewa ya dace da komawa bakin aiki ba tare da wata matsala ba.

A cewar wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan, Ibrahim Kaula Mohammed ya fitar, likitan da ke kula da lafiyar gwamnan ya tabbatar da cewa ya samu sauƙi sosai, kuma ya shirya tsaf don ci gaba da gudanar da ayyukan mulkinsa.

Bayanin da gwamnatin jihar dai ta fitar game da hatsarin ta ce lamarin ya faru ne a lokacin da gwamna Radda ke kan hanyarsa ta zuwa Daura, inda wata mota ƙirar Golf ta kauce hanyarta, kuma ta faɗa wa motar da gwamnan ke ciki.

Omoyele Sowore Yayi Karar Dan Sandan Da Ya Sace Masa Gilashi A Helkwatar Rundunar Yan Sanda
23/07/2025

Omoyele Sowore Yayi Karar Dan Sandan Da Ya Sace Masa Gilashi A Helkwatar Rundunar Yan Sanda

Address

Fct

Telephone

+2348124905058

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hausa Daily News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hausa Daily News:

Share