01/08/2026
Wasu daga cikin matasa 'yan asalin jihar Gombe sama da 100 da Professor Isa Ali Pantami ya samawa aiki a Ma'aikatar Galaxy Backbone sun ziyarci Majidadin Daular Usmaniyya a Ofis din shi da ke Abuja.
Matasan sun kai ziyarar ne a shekarar 2025 a lokacin da s**a cika shekara biyu da fara aiki, wanda zuwa yanzu sun cika shekaru 3 da fara aiki.
Shugaban tafiyar, Shehu Na-Allah ya mika sakon godiya a madadin wadanda basu samu halarta ba, wanda aka musu Posting zuwa LAGOS, KANO, GOMBE, ENUGU, KADUNA da wasu sassa na Birnin tarayya Abuja.
Kimamin matasa su 641 'yan jihar Gombe Professor Isa Ali Pantami CON, PhD (Majidadin Daular Usmaniyya) ya samawa aiki, a iya lokacin da ya rike mukamin NITDA da Ministan Sadarwa zuwa shekarar 2023.
Daga shekarar 2023 zuwa yau, Majidadin Daular Usmaniyya, ya kara samawa matasa da yawa ayyukan yi a wurare da dama da bamu san adadinsu ba.
A tarihin jihar Gombe kaf babu wanda ya taba rike mukami ya samawa matasa ayyukan yi kamar yadda Malam Pantami yayi. Idan kuma akwai a kawo mana shi?
Me kuke tsammanin zai faru idan ya zama Gwamnan jihar Gombe?
Ga jadawali na wasu wuraren da ya samawa matasa ayyukan;
1️⃣ Chief Executive Officers/Executive Directors- 12
2️⃣ Board Chairmen & Members – 19
3️⃣ Directorate Cadre Appointment- 6
4️⃣ NITDA – 78
5️⃣ NCC – 69
6️⃣ Galaxy Backbone – 103
7️⃣ NIMC – 170
8️⃣ Data Protection Bureau – 3
9️⃣ Emergency Call Centres – 62
🔟 NFIU – 6
1️⃣1️⃣ CBN – 9
1️⃣2️⃣ Fed. Polytechnic, Kaltungo – 4
1️⃣3️⃣ Immigration – 6
1️⃣4️⃣ Police Academy, Wudil – 2
1️⃣5️⃣ NIMASA – 2
1️⃣6️⃣ Fed. College of Horticulture – 3
1️⃣7️⃣ Borno State University – 1
1️⃣8️⃣ Fed. Teaching Hospital – 18
1️⃣9️⃣ NSITF – 2
2️⃣0️⃣ Police Force – 9
2️⃣1️⃣ Civil Defence – 5
2️⃣2️⃣ Health Registration Council – 5
2️⃣3️⃣ Transmission Company – 1
2️⃣4️⃣ Airspace Management – 2
2️⃣5️⃣ National Population Commission – 5
2️⃣6️⃣ Civil Aviation Authority – 2
2️⃣7️⃣ Federal Airports Authority – 2
2️⃣8️⃣ Jos Electricity Distribution – 10
2️⃣9️⃣ FUT Minna – 2
3️⃣0️⃣ FCE Gombe – 3
3️⃣1️⃣ FCE Zaria – 3
3️⃣2️⃣ Kaduna Polytechnic – 2
3️⃣3️⃣ PPPRA – 2
3️⃣4️⃣ Petroleum Equalization Fund – 2
3️⃣5️⃣ Federal Fire Service – 2
3️⃣6️⃣ BUK – 2
3️⃣7️⃣ Ministry of Communications & Digital Economy – 2
3️⃣8️⃣ FIRS – 1
3️⃣9️⃣ Miscellaneous / Others – 3
Total: 641
Iya wa 'yan nan jerin muka iya samowa kasancewar akwai wasu a boye da yawa da bamu iya ganowa ba. Cikin mutane 641 akwai 'yayan talakawa masu yawan gaske, akwai 'yayan Sarakuna, akwai 'yayan Malamai, akwai 'yayan manya da sauran su.
Da iznin Ubangiji Prof Isa Ali Pantami, Alkhairi ne ga al-ummar jihar Gombe, kuma sharri da kazafi da mutanen banza suke mishi a banza, bazai rage shi da komai ba sai ma dai ya kara mishi farin jini ga al'umma.
PM24 News
PMHN Hausa News