DMA - PRESS

DMA - PRESS Born to struggle

SAƘON TA'AZIYYAR SAYYID HASSAN NA§RÜLLÆHA madadin Matasan Harƙar Musulunci ƙarƙashin Jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky ...
25/02/2025

SAƘON TA'AZIYYAR SAYYID HASSAN NA§RÜLLÆH

A madadin Matasan Harƙar Musulunci ƙarƙashin Jagorancin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H), muna miƙa ta'aziyyarmu ta musamman ga Sahibul Asr (ATFS), Sayyid Qa'id (DZ), jagora Sayyid Zakzaky (H) gami da iyalai da ƴan uwan Shaheed Hassan Næsrųllæh da Sayyid Hashim Safiyyudeen na wannan babban rashi.

Saƙon ta'aziyyarmu ga ɗaukacin iyalan waɗannan Shahidai masu girma, tare da sauran al'ummar duniya (Musulmi da Kirista) gami da raunana na rashin waɗannan waɗanda s**a kasance garkuwa garemu baki ɗaya.

Duk da cewa waɗannan Shahidai ba sa cikinmu a zahiri, amma muna da yaƙinin suna tare da mu a baɗini, kuma muna nan a kan turbarsu, sannan za mu tabbar wa Yahudawa cewa har yanzu Sayyid Hassan bai mutu ba, kuma za su ga hakan a zahiri.

A ƙarshe muna roƙon Allah (SWT) da ya karɓi shahadar Sayyid Hasan Næsrüllæh da ɗan uwansa Shaheed Sayyid Hashim Safiyyuddin tare da sauran shahidan gwagwarmaya baki ɗaya, Allah (T) ya ɗaukaka darajarsu.

Youth Forum Media Team
Ja'afar Mustapha Sarina
A madadin Dandalin Matasa
25 - 02 - 2025

Taron Nisfu Sha'aban A AbujaDa misalin karfe 3 na ranar Juma'a 15 ga Sha'aban 1446 (14/2/2025) Harkar Musulunci a Nijeri...
14/02/2025

Taron Nisfu Sha'aban A Abuja

Da misalin karfe 3 na ranar Juma'a 15 ga Sha'aban 1446 (14/2/2025) Harkar Musulunci a Nijeriya karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta gudanar da gagarumin bikin Nisfu Sha'aban a muhallin 'Nigerian Airforce Event Center' da ke Abuja.

Taron, wanda aka fara shi da addu'a da karatun Alkur’ani, sannan ziyarar Imamul Asr (AJ), Sayyid Abdullahi Ashura ne ya gabatar da jawabi akan munasabar ta Nisf Sha'aban.

Ana cikin gabatar da taron ne gamayyar jami'an tsaron 'yan sanda (Police), soja (Army), DSS s**a zo wajen cikin motoci sama da 50, inda s**a tare 'bakin shiga wajen taron, s**a hana 'yan uwan da suke zuwa shiga, inda wasu wasu 'yan uwa s**a tsaya a kofar wajen har zuwa lokacin da aka yi addu'a aka watse.

Jami'an tsaron sun zo da shiri na musamman ne, a yayin da wasu daga cikinsu ke kokarin harzuƙa 'yan uwa, wasunsu suna ɗaukar Video, yayin da 'yan uwa s**a dauki matakan kaucewa tarkonsu ta hanyar sanya ido, da tattaunawa har aka tashi.

Jiya Alhamis ne aka fara gudanar da taron na Nisf Sha'aban a Abuja, inda aka gabatar da taron musamman, tare da majalisin mawaka.

Nisf Sha'aban rana ce mai daraja a Musulunci, a yayin da ta dace da ranar haihuwar jikan Manzon Allah (S), Imam Mahdi (AS) wanda shi ne limami na 12 a cikin halifofin da Manzon Allah (S) ya bar wa al'umma a bayansa.

— AliAssajjad Ibn Taheer
— Isa Charis
14/2/2025

Duk Wani Brother Ko Sister Bisa Wannan Matsayar Yake, Akasin Hakan Tashi Daga Aiki Ne.
10/02/2025

Duk Wani Brother Ko Sister Bisa Wannan Matsayar Yake, Akasin Hakan Tashi Daga Aiki Ne.

Zazzafan labari daga Kasar Farisawa.Shugaban kasar lɍañ da kansa ya sanar da cewa, daga yanzu kasar ta rufe kofar tattun...
10/02/2025

Zazzafan labari daga Kasar Farisawa.

Shugaban kasar lɍañ da kansa ya sanar da cewa, daga yanzu kasar ta rufe kofar tattunawa da kasar Amrka.

A lokacin da yake jawabi a wurin gangamin taron murnar cikar Daular Musulunci shekaru 46 da kafuwa, shugaban ya bayyana cewa a irin wannan ranar ce al'ummar kasar s**a kari azzaluman mahukunta daga kan mulkin kasar.

Shugaban kasar lɍañ din ya zargi kasar Amurk kan cewa ita da kanta ne ta fice daga yarjejeniyar tattauwa da lɍan ɗin a shekarun baya, ya ce ci gaba da tattaunawa da kasar Amrk a daidai wannan lokacin babu wani sakamako mai kyau da zai haifar.

Shugaban ya kuma ce, amincewa da bukatar Turom na neman zaman tattaunawa tamkar mika wuya ne ga kasar ta Amrk, don haka daga yanzu kasar lɍan ta dauki matsaya na kin amincewa da tattunawar.

Ya kuma zargin lzɍæl dake samun goyon bayan kasar Amrk da tayar da hankula a yanki, domin ta kaddamar hare-hare akasar lɍaki, Suriya, Levnon da kuma lɍañ.

Almujtabah Abubakar

SANARWA YAUMU TAKALIF DAGA DANDALIN MATASA ABUJADandalin Matasa yankin Abuja na sanar da Iyayen yara wannan shekarar ma ...
07/02/2025

SANARWA YAUMU TAKALIF DAGA DANDALIN MATASA ABUJA

Dandalin Matasa yankin Abuja na sanar da Iyayen yara wannan shekarar ma an shiryawa yara taron Yaumu takalif Wanda aka saba shiryawa.

SHEKARUN DA AKE BUKATA NA YARAN
Maza kar su wuce shekara 14 zuwa 15
Mata kar su wuce shekara 9 zuwa 10

Taron na wannan shekarar zai kasance ne kamar haka:-

Rana: 16 ga watan Sha'aban.

Wuri: Abuja

ABUBUWAN DA AKE BUKATA IYAYE YARA SUYI
1. za a yiwa yaro ko yariya sabon dinki
Maza: Fararen Kaya
Mata: Bakaken Kaya

2. Kudin transport daga yankin da kuke zuwa gurin gudanar da program din

Lambobin tuntuba
07087612429
07034343207
09116885492

Allah ya bada ikon halarta

SANARWA DAGA
KWAMITIN TAKLIF ABUJA ZONE

Inna lillahi Wa Inna Ilahirraji'uun 😭Yanzu Nan muka rasa Wakilin matasa na Jos Malam Musa Umar (Chaji-Chaji)Hasbunallahu...
04/02/2025

Inna lillahi Wa Inna Ilahirraji'uun 😭

Yanzu Nan muka rasa Wakilin matasa na Jos Malam Musa Umar (Chaji-Chaji)

Hasbunallahu Wa Ni'imal Wakil 😭

Za'a sanar da jana'izar sa zuwa anjima



04-Feb-1025

-Ga Wani Sirri da Ake Yinsa A Cikin Wannan Watan Na Sha'aban.-An Ruwaito Daga Imam Ali (AS) Shi Kuma Yaji Daga Manzon Al...
02/02/2025

-Ga Wani Sirri da Ake Yinsa A Cikin Wannan Watan Na Sha'aban.

-An Ruwaito Daga Imam Ali (AS) Shi Kuma Yaji Daga Manzon Allah (S) Yace: "Duk Wanda Ya Karanta Waɗannan Surorin A Cikin Wannan Wata Na Sha'aban Allah Zai Biya Masa Dukkan Buƙatunsa Kuma Ya Gafarta Masa Dukkan Zunubansa.

-Ga Surorin Kamar Haka:

-(1) Surar Fatiha, ×3
-(2) Ayatul Qursiyyu,×3
-(3) Kulya-Ayyuhal- Kafirun, ×3
-(4) Kulhullahu-Ahad, ×3
-(5) Kul A’uzu Birabbil Falak, ×3
-(6) Kul A’uzu Birabbin Nas, ×3

-Bayan An Kammala Karantawa Sai A Roƙi Allah Dukkan Buƙatun da Ake Nema, Cikin Gaggawa Za'a ga Biyan Buƙata.

-Ana Karantawa A Dukkanin Ranakun Sha'aban.

-Muhammad Jiddah Nguru
07037009525

ABUN MAMAKI BAYA ƘAREWAAƙalla akwai mabiya Sayyid Ibraheem Zakzaky(H) fiye da Miliyan Biyu masu aiki da manyan wayoyi, a...
01/02/2025

ABUN MAMAKI BAYA ƘAREWA

Aƙalla akwai mabiya Sayyid Ibraheem Zakzaky(H) fiye da Miliyan Biyu masu aiki da manyan wayoyi, amma Sayyid ya buɗe shafi na office ɗinsa a Facebook, har yau babu ko mutum 50,000 masu bibiya, ya buɗe channel na gidan talabijin nasa mai suna ABS Hausa channel a YouTube, amma har yau babu koda mutum 20,000 masu bibiya, ya buɗe shafin gidan radiyo mai suna ABS Radio a facebook amma har yanzu babu koda mutum 2000 masu bibiya. Duk ko babu indaa za su samu sakonninsa da karatunsa sabbi sai a can.

Alhali mabiyansa sun fi kowa bibiyar shafukan wasu malamai, dama wasu influencers wajen yin comments da like. Inna lillahi wa Inna lillahi rajiun.

Shin wannan me yake nufi? Shin rashin sani ne ko sakaci ne ko gafala ko rafkana ko rashin sanin ciwon kai?

Idan Ɗan Uwa bai ɗauko daga wajen Malam ba, shin daga wajen wa zai ɗauko kenan?

Idan Ɗan Uwa ya guji shafin Jagoransa, ya yi nisa da inda zai samu Irshadinsa me zai hana wani yayi wasa da hankalinsa?

Wannan abun yanada ɗaure kai, wannan abun yana da ban mamaki, ga korama a gidan wasu, amma sun je waje lalaben rijiya.
Idan mutum ya san baya bibiyar shafukan Jagora to tun da wuri ya fara, domin ci gaba ne, ya riga ya zo, kuma babu ranar ja baya.

Idan Abuja ta yi nisa, ko ta yi tsada, shin itama ABS channel da ABS Radio da Sayyid Ibraheem Al-zakzaky' office nisa s**a yi?

Kada dai wannan ya zamo alamar kangara da juya baya. Allah ka tausaya mana, kasa mu fadaka mu falka.

Shamsudeen Hassan Zuru

ALHMMADULLILAH!An Ɗaura Auren Salim Sassaki da Muhammad Lambata a garin Sabon Wuse dake Jahar Neja.An ɗaura auren Salim ...
31/01/2025

ALHMMADULLILAH!
An Ɗaura Auren Salim Sassaki da Muhammad Lambata a garin Sabon Wuse dake Jahar Neja.

An ɗaura auren Salim a bisa Sadaki Duba 800,000 ɗari takwas. Ya biya Lakadan ba Ajalan ba.

Muna fatan Allah ya basu zaman lafiya da zuri'a ɗayyiba🙏😊

DMA PRESS S/WUSE

Allah ya Kara lafiya da kariya ta musamman.اللهم صلى على محمد وآل محمد 💖💗Allahumma salli ala Muhammad wa Ali Muhammad wa...
31/01/2025

Allah ya Kara lafiya da kariya ta musamman.

اللهم صلى على محمد وآل محمد 💖💗
Allahumma salli ala Muhammad wa Ali Muhammad wa ajjil farajahum

31/01/2025

اللهم صلى على محمد وآل محمد 💖💗
Allahumma salli ala Muhammad wa Ali Muhammad wa ajjil farajahum

JIYA MUN SHA MADADI DAGA SAYYID ZAKZAKY (H)Wato Saboda tsananin fadi da girman da Musulunci yake dashi, da kuma irin dim...
28/01/2025

JIYA MUN SHA MADADI DAGA SAYYID ZAKZAKY (H)

Wato Saboda tsananin fadi da girman da Musulunci yake dashi, da kuma irin dimbin tarin ilimin da Allahu SWT ya kimsawa wasu bayin Allah, irin Sayyid Zakzaky (H) Babu yadda za ayi ka zauna gaban su baka ji sabon abu ba, wanda baka taba ji ba, ko ka taba ji to baka jishi daidai ba sai ka tsinci kanka a gaban Sayyid Zakzaky H zaka sha mamaki yadda zai fayyace maka shi sanka sanka,

Duk tarin Malaman Nigeria ko Africa ma baki daya, baka da wani Malami da ka taba jin munasabar Yaumu Mub'as a bakin sa, har ya ware mata rana da lokaci don fayyace wa Al'ummar musu yadda aka aiko Manzon Allah SAWW da yadda ya isar da sakon da yadda Al'umma ta karbi sakon da wadanda s**a yaki sakon da wadanda s**a amsa kiran da wadanda s**a tallafawa tafiyar

Jiya fa Sayyid Zakzaky H sai da ya dauko mana tarihi tiryan tiryan tun daga kakannin Manzon Allah SAWW tsatso bayan tsatso tun daga Annabi Ibrahim da Annabi Isma'el (Alaihimus Salam) har yanzu ga Sayyid Abdulmudallib (AS) tukewa ga Sayyid Abdullahi Mahaifin Manzon Allah SAWW da Nana Aminatu (SA) da duk abubuwan tarihi da Mu'ujizozin da s**ai ta faruwa da yadda Annabawa (AS) suke magana da iyayen su mata tun suna cikin ciki, Kai ba wannan ba ma" har yadda Annabawa AS suke magana da iyayen su maza a cikin tsatson su na mazan, Ya Allah, kai Wannan Al'amari da girma yake,

Kuma Sayyid Zakzaky H ya rika kafa hujjoji da nassi daga ayoyin Alkur'ani mai girma da ingantattun hadisai, Su Malam (H) s**ace in baka sani ba ba yana nufin babu bane, ko ba haka yake ba, a a in baka sani ba kawai kace baka sani ba, kaje ka nemi sani, in kuma bakason ka sani ne, Su Malam (H) s**ace to kayi shiru da bakin ka, ka bari masu son sani su sani fakat,

Dan uwa ka nemi tashar ABS YouTube TV channel kasha madadi kaima, don dai mu kam jiya ji nayi kamar na koma sabo fil game da Imani da Manzon Allah SAWW da Ahlulbaity AS 🌹

Jagora Sayyid Zakzaky (H) Muna Rokon Allahu SWT Ya kara lafiya da nisan kwana yasa kuga bayan makiyan ku 🤲🌹

LABBAIKA YA RASULULLAH ✊
LABBAIKA YA IMAMU ALI ✊
LABBAIKA YA AL ZAKZAKY ✊

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when DMA - PRESS posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share