23/08/2025
ZAMAN MAKOKI WAFATIN MANZON ALLAH (S,A,W) DAGA GARIN GOMBE.
A yau asabar 29 ga watan safar aka Shiga rana ta biyu kuma ta qarshe na zaman makokin annabin rahama muhammad (s,a,w) wanda yan'uwa musulmi Almajiran Sayyid Ibrahim Yaqoub El-Zakzaky (H) s**a saba gabatarwa duk shekara a cikin garin gombe.
Anfara da gabatar da waqoqi na juyayi (zikrah) daga mawaqa tare da amsawa da nuna alhini daga mahalarta.
Daga bisani sheikh muhammad adamu abbare ya cigaba da jawabai da cire darussa daga rayuwar ma'aikin (s,a,w) inda yake cewa manzon allah (s,a,w) shi haskene wanda ya haskaka ilimi da addinin musuluci a duniya bakidaya wanda ya zamo a lokacinsa ba inda labarinshi bai shigaba a fadin duniya.
Ya cigaba da cewa bayan wafatin ma'aikin Allah banu umayya sun ta qoqarin bata komai na addini tun aiko annabi har wafatinsa ta hanyar hadisan qarya da saka qiyayya na iyalan gidan manzon allah da muzan tasu a tsakanin al-umma Kuma abun baqin cikin da wasu sahabbansa akayi wannan ta'asar, musamman karya alkawarin mubai'a da s**ayiwa imam ali amirul mu'uminin (As) da barin jikin manzo(s,a,w) a kwance a cikin gida ba'amai sallah aka bizneshiba zuwa wajen nada sabon khalifa wanda a duk duniya ba wani malami ko sarki da aka taba yiwa irin wannan ace allah ya karbi rayuwarsa amma kafin akaishi saida aka nada sabon Khalifa babu shi amma sai manzo(s,a,w) saboda tsananin qiyayya, dama sauran abubuwan da s**a auku bayan wafatin manzo (s,a,w).
Daga qarshe Sheikh Muhammad abbare ya ja hankalin yan'uwa akan cewa kada mudauka cewa abinda aka yiwa manzon allah a wancan lokacin baza'a iyan yinshiba a wannan lokacin saboda haryanzu wannan rudani da qarerayi da akayi su ke aikin kuma suketa barna a cikin addinin musulunci, ta hanyar a sakama shakku akan jagora Kuma yace a kula.
Daga qarshe akayi addu'a tare da ziyarar Manzo (s,a,w) aka sallami kowa daga wajen majalisin.
Ga kadan daga cikin Hotunan majalisin.
'irar Gombe Media
29/Safar/1447
23/August /2025