Cibiyar Wallafa Ayyukan Shaikh Zakzaky

Cibiyar Wallafa Ayyukan Shaikh Zakzaky Shafin Cibiyar Wallafa Da Yada Ayyukan Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)

JAN HANKALI DANGANE DA HAƊIN KAN MUSULMI— Daga Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)“Saboda haka, mutum ya k**ata ya yi naz...
15/09/2025

JAN HANKALI DANGANE DA HAƊIN KAN MUSULMI

— Daga Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)

“Saboda haka, mutum ya k**ata ya yi nazarin wa yake ma aiki? Mun sha fada mukan nanata ba daya ba biyu ba, duk wanda ka ji ya na kira ga rarrabar kawukan Musulmi, ya yarda ko bai yarda ba, ya sani ko bai sani ba, yana ma makiya aiki ne—ko ya yarda ko kar ya yarda, ko ya sani ko kar ya sani yana ma makiya aiki ne. Domin aikin makiya ne, shirinsu ne na rarraba din. Yanzu al'ummar Musulmi ya zama abinda ya dame su shi ne; me ya raba su ba meya hada su ba.

“Na'am ba muce ba abinda ya raba su ba, Manzon nan (S) ya zo da sako, kuma ya isar da sako ɗin. Allah Ta'ala Ya saukar masa da Alƙur'ani kammalalle cikakke, babu abinda ya kara shi babu abinda ya rage shi. Kuma ya bayyana ma'anar Alƙur'anin, kuma bai bar duniyar nan ba sai da ya kafa al'umma akan Addini.

“To amma al'ummar ita ta bamu gadon waɗansu abubuwan. An samu sabani akan shugabanci—wannan sabani ne aka samu. Ba a samu sabani akan matsayin Allah Ta'ala a matsayin Shi ne kadai Abin bauta ba. Ba a samu sabani akan shi Manzon Allah ne, kuma bawan Allah Manzon Allah, ba wani wanda ya ke kiranshi Ubangiji ko ɗan Ubangiji, ko daya daga cikin wadanda s**a taru s**a yi Ubangiji. Har ma a tashahud (zaman tahiya) dinmu sai mun ambaci; shi bawa ne kafin mu ce shi Manzo ne. A kullum sai mun ce; “Wa Ashhadu Anna Muhammadan Abduhu wa Rasuluhu”.

“Saboda haka bamu da sabani akan matsayin Manzon Allah, ba wani wanda yake ce mishi Ubangiji ko ɗan ubangiji ko abinda ya yi k**a da haka. Bamu da sabani akan Alƙur'ani. Na'am za ku ji zancen wawayen gari suna ce muku akwai wani Alƙur'ani daban, amman dai ‘Fi'ilan' dai Alƙur'ani guda daya ne, bashi da ƙari ba ragi shi ne Wannan.

“To amma al'umma ta saba akan fassara da ruwayoyi, don haka aka samu abinda ake ce ma ‘Firƙa' an samu ‘Firƙoƙi’ an samu Mazahib— Mazhabobi, an samu ‘Ɗuraƙat’ an samu Ɗariƙoƙi, wannan a cikin addinin suke. Lokacin da muke magana kan Mazhaba ko Firƙa, ko Ɗarika, muna magana ne kan ‘Juz'i’ bangare muke magana akai. Amma in muka zo muna magana akan Musulunci muna magana ne akan abinda ya doru ne akan dukkan wadannan, shi ne a sama, Musulunci ne a sama. Su wadannan karkashin Musuluncin suke. Duk wanda ka ji yana rigima akan Firƙa to yana rigima akan bangare ne, ya bar tushe, ya bar asali, yana magana akan reshe ne.

“Duk wanda ka ji yana magana akan Mazhaba shi ma ya bar tushe ne ya koma yana rigama akan reshe ne. Duk wanda ka ji yana rigama akan Ɗarika shi ma ya bar tushe ne ya koma reshe, don wadannan rassa ne. Firƙoƙi, Mazhabobi, Ɗariƙoƙi, da ma yanzu da ake yayin ƙungiyoyi, duk waɗannan ƙungiyoyi juz'iyai ne.

“Na'am da manufofi daban-daban, ba su (manufofin) ne asasi ba, ba su ne kuma asali ba. Muna magana kan asali ne; sunanmu Musulmi, ba sunanmu wadannan rarrabe-rarraben ba. Sunan al'ummarmu Musulmi shi ne ainihin Allah Ta'ala Yake cewa: “Huwallazi Sammakumul Muslimin min Kab, Wafihazalik” Ainihin shi ne tun farko mun ambace ku addinin Babanmu Ibrahim shi ne ya ambace ku, ma'ana Allah Ta'ala shi ne Ya ambace ku Musulmi tun farko da kuma a wannan lokacin da wannan Manzon ya zo, domin ku zama shaida ga sauran al'ummu, kuma Manzo ya zama shaida akan ku.

“Yanzu kiraye-kirayen sunannaki da daukan kowwane suna a matsayin shi ne ma addinin ayi ta rigima akai. Da kuma katangar karfen da aka sa a kwakwalwa, babu katangar sam, ba ta da wujudi sam-sam! Amma sai a kirkireta a raba tsakanin al'umma, har mutum ya riƙa ganin cewa wancan tsakaninsa da shi akwai shamaki, ra'ayinsu daban ne, fahimtarsu daban ne, har ma in tayi k**ari ma sai ya ce addininsu daban ne, alhali katanga aka sa masa a kwakwalwarsa—ta fi katangar karfe karfi. Saboda ainihin ta raba shi da ɗan'uwansa Musulmi alhali addininsu guda.

“To wannan lokaci namu da ainihin bamu son ya zama sai maƙiya ne zasu ingiza mu izuwa hadin kai, don shi hadin kan nan a cikin addinin namu ne yake, umarni ne na Allah Ta'ala: “Wa Atasimu Bi Hablillahi Jami'an Wala Ta Farraƙu” ku yi riko da igiyar Allah gabadayanku kar ku rarraba, aka nuna illar rarraba tun a na farko, sannan kuma harwalayau shi wannan Manzo ya k**anta al'ummar Musulmi da misalin jiki guda, wanda idan wani ɓangare nasa ya yi ciwo, duk sauran bangarorin za su amsa da rashin bacci da kuma zazzabi. Saboda haka idan aka taba wani bangare duk gabadaya jikin ne yake amsawa, to haka al'ummar Musulmi suke, tamkar jiki Guda ne”

— Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yayin jawabinsa na Khatamar Makon Hadin kai na shekarar 1447/2025.

— Cibiyar Wallafa Ayyukan Shaikh Zakzaky




22 ga Rabi'ul Auwal 1447
15 September, 2025

“Saboda haka ya k**ata mutum ya yi nazari, wa ya ke ma aiki?  Mun sha faɗa muna nanatawa, duk wanda ka  ji yana kira ga ...
13/09/2025

“Saboda haka ya k**ata mutum ya yi nazari, wa ya ke ma aiki? Mun sha faɗa muna nanatawa, duk wanda ka ji yana kira ga rarrabar kawukan Musulmi, ya yarda ko bai yarda ba, ya sani ko bai sani ba yana ma makiya aiki ne”.

— Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yayin jawabinsa na Khatamar Makon Hadin kai na shekarar 1447/2025.

— Cibiyar Wallafa Ayyukan Shaikh Zakzaky



Alhamdulillah!Bayan halartar taron ƙasa da ƙasa na haɗin kan Musulumi karo na 39, a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Jagora...
12/09/2025

Alhamdulillah!

Bayan halartar taron ƙasa da ƙasa na haɗin kan Musulumi karo na 39, a Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya dawo gida Nigeria lafiya.

— Sayyid Ibraheem Zakzaky Office
Cibiyar Wallafa Ayyukan Shaikh Zakzaky




12/September/2025

GANAWAR JAGORA (H) DA DALIBAN MASHHADDaga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)Da yake jawabi ga 'yan'uwa dalibai da ke ka...
11/09/2025

GANAWAR JAGORA (H) DA DALIBAN MASHHAD

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

Da yake jawabi ga 'yan'uwa dalibai da ke karatu a birnin Mashhad, a ranar Alhamis 18 ga Rabi'ul Awwal 1447 (11/8/2025), Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya ja hankalinsu akan yin karatu da sunan Allah, kuma saboda Allah Ta'ala.

Shaikh Zakzaky ya karfafi daliban akan su fahimci cewa shi arziki daga Allah Ta'ala yake zuwa. “Na'am, ba yana nufin cewa ba za ka tashi ka nemi abinci ba, amma ya zama rayuwarka tana da manufa, ka fahimci cewa ana cin abinci ne don a rayu, ba ana rayuwa don a ci abinci ba ne.”

Yace, daliban da s**a fito don yin karatu, su sani cewa Allah Ta'ala Ya zabo su daga cikin dandazon al'ummarsu ne don su wakilce su, kuma su amfanar da su in sun koma gida. “Don haka kar su dauka cewa sun zo ne su zauna dindindin.”

Jagora ya yi bayani dangane da daidaito wajen wazifa a tsakanin daliban addini na Hauza da kuma daliban jami'o'i, yace kowa a cikinsu yana tsai da wajibinsa ne, kuma kowa da inda ake da bukatarsa. Ya bayar da misali da yaƙin da Iran ta yi da Isra'ila na kwanaki 12, inda yace 'Technology' din da aka yi amfani da su, daliban jami'a ne s**a samar da su, amma tare da shiryarwar Malaman Hawza Ilmiyya.

Don haka ya jaddada bukatar cewa, ko wane fanni mutum yake karantawa, ya zama yana yi ne da sunan Allah, kuma saboda Allah.

Yayin da yake tsokaci akan wasu ra'ayoyin da suke kutsowa cikin 'yan'uwa a 'yan tsakan-kanin nan, musamman masu kawo ra'ayin kira zuwa ga Mazhaba maimakon kira zuwa ga addini gabaɗaya, ya bayyana cewa ta hanyar gwagwarmayar Imam Khomeini ce muka san da Shi'anci kansa. “Bamu san ita kanta Shi'a din ba, sai don juyin da Imam Khomeini (QS) ya yi.”

Shaikh Zakzaky ya bayyana yadda sama da shekaru 50, tun suna karatun 'Advance level' har zuwansu Jami'a, duk daga Jami'ar London da ke Ingila ake shiryo musu jarabawar karatun 'Islamic Studies', kuma duk kusan tambayoyin da ake shiryawa na baƙanta Shi'a ne a lokacin. Ya ce: “Tsarin karatun Islamic Studies na jami'o'i, asalinsa daga Ingila ne, wasu Malaman ma Yahudawa ne, domin mu a lokacinmu Malamanmu na jami'a 'product' ne na Ingila. Gwagwarmayar Imam Khomeini (QS) ce ta fito da asalin yadda Shi'a suke, a yayin da Shi'a sun boye kansu ne kafin 'revolution' din Imam (QS).”

Don haka, Jagora (H) ya bayyana mamakinsa akan wanda yake jin cewa yanzu zai koma yin Shi'a ba gwagwarmaya. “Kai a matsayinka na wanda ya fahimci Shi'a ta hanyar gwagwarmaya, ta yaya za ka karbi wannan ra'ayi, alhali ta hanyar aikin wasu na gwagwarmaya ne ka fahimci Shi'ancin kansa?" Ya tambaya.

Jagora, har ila yau ya yi tsokaci akan yan Shi'an London, da ake amfani da su wajen bata Shi'anci. Yace, shi wannan ra'ayin nasu, yana kokarin tabbatar da abinda maƙiya suke tuhumar Shi'a akai ne, ta hanyar nuna cewa ana zage-zage da tsine-tsine, wanda su ne suke yi.

Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) wanda ya jaddada dakewa saboda Allah a matsayin kashin bayan gwagwarmaya, ya jinjinawa Jamhuriyar Musulunci ta Iran akan yadda nasararta na yakin kwanaki 12 ya baƙanta ran maƙiya addini, ya kuma fito da ƙarfin Musulunci. Yace: “Su kansu Turai suna fatan Iran ta cece su daga Sahayoniyawa, saboda Sahayoniyawan sun rike musu wuya su ma.”

Jagora ya gana da daliban ne a birnin Mashhad, biyo bayan kammala taron Makon Haɗin kan Musulumi karo na 39, da kuma taron ƙasa da ƙasa akan haɗin kan goyon bayan Palasdinu, da ya gudana a birnin Tehran, a Jamhuriyar Musulunci ta Iran a makon da muke ciki.







12/September/2025

Bayan kammala taron ƙasa da ƙasa akan haɗin kan Musulumi karo na 39, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ziyarci Haram...
11/09/2025

Bayan kammala taron ƙasa da ƙasa akan haɗin kan Musulumi karo na 39, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ziyarci Haramin Imam Ali Bin Musar Ridha (AS) a Mashhad.

— Sayyid Ibraheem Zakzaky Office
Cibiyar Wallafa Ayyukan Shaikh Zakzaky




11/September/2025

Da yammacin yau Alhamis 18 ga Rabi'ul Awwal 1447 (11/09/2025), Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ziyarci ofishinsa (...
11/09/2025

Da yammacin yau Alhamis 18 ga Rabi'ul Awwal 1447 (11/09/2025), Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya ziyarci ofishinsa (Szakzakyoffice) da ke Mashhad, Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

— Sayyid Ibraheem Zakzaky Office
Cibiyar Wallafa Ayyukan Shaikh Zakzaky




11/September/2025

JAGORA (H) YA GANA DA ‘YAN UWA DALIBAI DA KE KARATU A JAMI’O’I DABAN-DABAN A IRANDaga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H...
11/09/2025

JAGORA (H) YA GANA DA ‘YAN UWA DALIBAI DA KE KARATU A JAMI’O’I DABAN-DABAN A IRAN

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

A ranar Laraba, 17 ga Rabi’ul Auwal, 1447, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ya gana da ‘yan uwa dalibai da ke karatu a jami’o’i daban-daban a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Ganawar, wadda ta auku a irin ranar Mauludin Manzon Rahma (S) na wannan shekarar, ta auku ne a Tehran, babban birnin Iran, biyo bayan kammala taron makon hadin kan Musulmi, wanda “Majma’ut Taqrib Bainal Mazahib” ta shirya a karo na 39, da kuma taron gangamin goyon bayan Palasdinawa da “Majalisar Kasa da Kasa na Farkawar Musulunci” ta gabatar a Tehran.

A yayin jawabinsa ga daliban, Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana dalilin kasancewarsa a Jamhuriyar Musulunci a daidai wannan lokacin, da kuma irin yadda taron makon hadin kan Musulmi da ake gudanarwa a gida (Nijeriya da makwaftanta) ya rika tasirin da har yakan sa ya kasa halartan taron Majma’ da ake gudanarwa duk shekara a Iran din.

Da yake bayanin Mauludin Manzon Rahma (S), Shaikh Ibraheem Zakzaky ya bayyana Manzon (S) da sakon da ya zo da shi a matsayin abu guda. Yace: “Manzon nan (S) shi aka aiko da sako. Kuma shi ba aikinsa ne kawai yace muku ga sakonku kawai ba. Ba ya zo ne ya samu mutane ya mika musu, yace musu ga sakonku (shikenan) ba. A’a, shi an rika saukar mashi da bayanin sakon ne a hankali a hankali har ya kammala. Ana saukarwa yana aikatawa, yana kuma koyar da mutane akan aikatawar, saboda haka shi ne alami na wannan sakon. Wato shi ne ‘ramzi’, da shi da sakon abu guda ne, abu daya ne.”

Yace: “Don haka ne ma a wajenmu, in mutum ya tauye darajar Annabi (S) ko da dan yaya ne, to a wurinmu ba ya tauye darajar addini da mikidarin wannan tauyewan ba ne (kawai), a’a, ya rusa addinin ne ma gabadaya.”

Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa: “Da zaran an tauye darajar Annabi (S), to an rushe addinin ne. Don haka za ku ga makiya addinin gaskiyar magana, kullum s**an yi s**a ne kan al’amarin Annabi (S), don in s**a soki Annabi (sun san) suna rusa addinin ne.”

Ya kara da cewa: “Shi kan-kansa Manzon Allah (S) shi ma sakon ne, saboda haka shi ne aka ajiye a matsayin samfurin da za a kwafa. Wato ba za ka zama ka yi daidai da shi ba dama, amma za ka yi koyi da shi ne. Allah Ta’ala yana cewa: ‘Lakad kana lakum fi Rasulillahi uswatin hasanatun, liman kana yarjul Laha wak yaumal akhira….’ Kuna da kyakkyawan misali ga Manzon Allah (S), ga wanda yake kaunar Allah da ranar Lahira – shi ne Manzo ya zama abin koyi a gare ku.”

Jagora ya jaddada cewa, duk abinda ya shafi Manzon Allah, ko mene ne, to yana da daraja, don ya alamta Annabi (S) din ne. Don haka yace: “Muna iya cewa, ranar Mauludi ma yana daga cikin Sha’airullah”

Ya kawo fadin Sayyid Ibn Dawus da ke cewa: “Daidai gwargwadon murnarka a ranar haihuwar wani bawan Allah, daidai girman wannan bawan Allah din a wajenka.” Yace, idan aka ce ga fiyayyen halitta, shugaban Manzonni, shi kuma ana Mauludinsa (tuna ranar haihuwarsa), shi kuma ya kenan? “Kun ga ba za mu taba fifita wani kan Manzon Allah (S) ba, kuma ba za mu taba murnar da ya wuce wanda za mu yi a lokacin haihuwarsa ba.” Ya jaddada.

Jagora ya bukaci al’umma da su duba kawukansu su kwatanta da kammalallen sakon da Manzon Allah (S) ya zo ya isar a tsawon shekaru 23 na isar da sako. Yace: “Sakon nan da Manzon Allah (S) ya isar, ya kuma bar al’umma dore a kai, tambaya, a wane miqidari ne al’ummar nan take akan sakon? Ka dubi sakon da Annabi (S) ya zo da shi, ka kuma dubi al’ummar nan yadda take a yau. Sun yi daidai?”

A nan ne ya tunatar akan muhimmanci da wajabcin hadin kan Musulmi, da damuwa da al’amarin junansu, k**ar yadda Manzon Allah (S) ya bar wasiyya. Ya kuma tunatar dangane da halin da al’ummar Palasdinu suke ciki, tare da kokawarsa akan halin ko in kula da duniyar Musulmi suke nunawa akan hakan. Sannan ya yi magana akan yadda makiya suke ta kokarin tarwatsa kasashen Musulmi, da kuma halin da aka jefa mu a Nijeriya na rigingimu daban-daban da sunan Kabilanci, ko da sunan bangaranci, ko da sunan addini.

Jagora (H) ya yi kira ga daliban akan su fahimci wazifar da ke kansu na cewa al’umma na jiransu a gida don su shayar da su tare da amfanar da su daga abin da s**a samo na ilimi. Inda ya nuna babu bambanci tsakanin masu karatun Hauza da masu karatun Boko, dukkansu za su yi karatu ne na addini, wanda zai wa addini aiki. Yace: “Ku yanzu kun zo ne ku kamfata don ku je inda ake da kishin ruwansa… Kun zo ne ku dibi ilimi, sawa’un ko wane fanni kake karantawa, ko da ‘Engineering’ ne ko ‘Medicine’, in ka koma gida za ka yi ‘engineering’ da ‘medicine’ din addini ne.”

Ya bayyana cewa: “Da ace mutane sun bi koyarwar A’imma (AS) da shi kenan sun warke.” Yace: “Ban ce muku ba za a yi bincike (research) ba, to amma da ya yi sauki. Kawai nan da nan da mun fitar da ‘scientists’ wanda za su fitar mana da abubuwa daban-daban daga koyarwarsu. Alhamdulillahi ai an dan gwada a nan (Iran) an gani ko? Da aka dan kwama, aka yi tsokana, ai an gani ko?”

Shaikh Zakzaky (H) ya yi martani ga masu cewa cigaban fasahar Iran ba daga addini ba ne. Yace, su gane, lallai wannan ‘Technology’ din daga Allah ne. Domin cikin gajeren lokaci s**a iya kai ga wannan matakin. “Ko ku yarda ko kar ku yarda, al’amarin Allah ne ke cikin (cigaban Iran), kuma shiriya ce ta Allah, kuma kadan ma kuka gani insha Allahul Azeem.”

Da yake bayan kammala jawabin Jagora (H), an bukaci ya dora rawani ga wasu ba’adin ‘yan uwa, sai ya zama mutum guda ne ya samu halartan muhallin a cikinsu, don haka bayan dora masa rawanin, Jagora (H) ya yi masa addu’a, sannan kuma ya ja hankali akan kiyaye daraja da alfarmar rawani.

Yace: “Da na ji kun yi magana dangane da rawani, nace to dama rawani ba sarauta ne ba fa, dawainiya ne. Wato ana nufin mutum ya alamta addini ne.”

Ya ce, ya k**ata tunda shi an saka masa rawani, ya zama ramzi na abinda yake siffatawa. “Dazu ina magana akan cewa, Manzon Rahma (S) shi ne ramzi ‘perfect’ na addini. To kai kuma daidai gwargwado za ka zama ramzi ne na addini din, ta yadda za a ga addini a ‘suluk’ dinka, a zantukanka da ayyukanka, ta yadda ba za a ga wadansu ayyuka wanda s**a saba ma addini ba.”

Jagora ya ja hankali akan kar sanya rawanin ya zama don ‘business’ kawai, ta yadda za a rika ajiye shi a lokutan rayuwa, sai in za a yi jawabi sannan a dauko a saka. “Ya zama ainihin in mutum ya sa rawanin nan, to yana nan a kansa ko ma ina ne za shi, don ya zama yana alamta abin (a dukkan rayuwarsa).”

A karshen Jawabinsa, Jagora ya yi fatan Allah Ya bayyanar da wanda da bayyanarsa ne za a samu mafita, karshen makiya ya zo, adalci ya tabbata, duk abubuwan nan su kwaranye, mu samu izzar da ba za mu ga irinta ba Insha Allah. “Muna fatan ya zama muna nan za a yi, don an kusa. In kuma Allah ya dauki ranmu kafin lokacin, Allah Ya dawo da mu a yi da mu, insha Allah.” Ya karkare.







11/September/2025

JAGORA (H) YA RUFE TARON MAKON HADIN KAN MUSULMI A ABUJA*“Duk Wanda Aka Ji Yana Kira Ga Rarraban Kawukan Musulmi, Yana M...
10/09/2025

JAGORA (H) YA RUFE TARON MAKON HADIN KAN MUSULMI A ABUJA

*“Duk Wanda Aka Ji Yana Kira Ga Rarraban Kawukan Musulmi, Yana Ma Makiya Aiki Ne.”

*“Al’ummar Musulmi Abu Guda Ne, Kuma Daukakarsu Na Cikin Haduwarsu Ne.”

Daga Ofishin Sayyid Ibraheem Zakzaky (H)

A yayin da yake gabatar da jawabin rufe taron Makon Hadin Kan Musulmi, wanda ya gudana a Abuja, a ranar Laraba 17 ga Rabi’ul Awwal, 1447, Jagoran Harkar Musulunci, Shaikh Ibraheem Zakzaky (H), wanda ya gabatar da jawabi ta hanyar bodiyo daga Iran, ya taya al’umma murnar zagayowar ranar haihuwar Manzon Rahma (S), wanda aka haifa a rana mai k**a ta yau, 17 ga Rabi’ul Auwal, shekara 1500 daidai da s**a gabata a Kidayar Kamariyya.

Shaikh Zakzaky ya bayyana cewa, ruwayar da ta fi shahara ta haihuwar Manzon Rahma (S) it ace 12 ga watan Rabi’ul Auwal, ruwaya mafi inganci kuma ita ce 17 ga watan. “Don haka mukan dauki tsakanin wadannan ranaku biyun, - 12 zuwa 17 mu yi abinda mukan kira Makon Hadin Kai, wanda akan yi tarurruka daban-daban don a kusanto da juna tsakanin al’ummar Musulmi.”

Sayyid Zakzaky, ya bayyana wannan lokacin a matsayin lokaci mafi dacewa fiye da kowane lokaci a tarihi na bukatar hadin kan Musulmi. Yace: “Domin a wannan lokaci ne makiya addini s**a fito muraran, s**a nuna suna gaba da Manzon Rahma (S) ne, suna gaba da Alkur’ani ne, suna gaba da sakon da ya zo da shi ne, suna gaba da al’ummarsa ce, suna kuma kokari ne su ga sun share wannan al’ummar, sun share wannan sakon a doron kasa.”

Ya cigaba da cewa: “Makiya sun fito da maitarsu balo-balo, hatta kalmomin da da s**an boye, amma yanzu sun fito suna fadi. S**a fadi cewa ba su da makiyi illa Musulmi, kuma za su yi iyakan iyawansu ne su ga sun murkushe su, sun zama ba su da wani tasiri a duniya.”

Jagoran ya yi bayani akan yadda makiya addini daya-bayan-daya suke bi suna kokarin ruguza kasashen Musulmi. “Daga kasashen Musulmi akwai Libya, wanda sun wargazata, da kuma Lebanon wanda yanzu suke kokarin su fada cikinta, da Sudan wanda yanzu aka kai musu matsalar rarraba, da kuma Afganinstan da s**a je s**a yi biji-biji da ita, - da ita ma s**a fara. To kuma suna hankoron Syria da Iraq. Duk sun ayyana cewa sai sun kawar da wadannan kasashe, karshe kuma za su nufi Jamhuriyar Musulunci ta Iran. Suna ganin in s**a gama da ita, k**ar sun gama da dukkanin al’ummun kenan.”

Ya kara da cewa: “Na’am, akwai Pakistan, da Indonesia, Malaysia, duk suna idanunsu, amma suna ganin wadancan kasashen su s**a fi zama ainihin kasashen da za su mutsittsika. Na ma tsallake muku Yeman, wanda a shekarun baya s**a dira a kanta, s**a dinga kisan ba jib a gani. Duk wannan aikinsu ne.”

Harwayau, Shaikh Zakzaky (H) ya bayyana yadda a daidai wannan lokacin dasisa da makircin da makiya addini s**a dinga yi na rarraba kawukan Musulmi ya fito fili fiye da kowane lokaci a tarihi. “A wannan lokaci ne ya fito balo-balo, ya nuna al’ummar Musulmi ashe akwai wadansu da suna ma makiya ne aiki. Balo-balo s**a fito suna marawa makiyan nan baya. Ba sai na baku misalai ba, wanda duk yake bin abinda ke gudana a duniyar nan, ya san abinda ke faruwa. Aka ga wasu mutane da s**a nuna balo-balo su ba al’ummar Musulmi ta dame su ba, su kujerun mulkinsu ya dame su, kuma su suna ma makiya ne aiki balo-balo.”

Jagora ya kara da bayyana wannan lokaci a matsayin lokacin da makiya s**a farwa al’ummar Musulmi na Palasdinu da kisan da ba a ga irinsa ba a tarihi. Yace: “Da can suna amfani da miyagun mak**ai na harbi da bindiga, s**a zo suna amfani da jiragen sama, s**a zo ba irin nau’in makamin da basu amfani da su akan al’umma wanda basu ji ba, ba su gani ba, maza, da mata da yara, galibansu mata da yara kanana, da ma jarirai.”

Ya bayyana sabon makamin da s**a canza wajen zaluntar Palasdinawa; “Yanzu sun zo da wani irin makami, shi ne a rutsa da mutane, a yunwatar da su, yunwar ta kashe su. Yanzu yunwa din ta zama makami da suke amfani da wajen kashe al’umma, galibansu jarirai wadanda akan haife su ya zama basu iya samun madara. Yanzu an hana mutane abinci, an hana musu magani, an hana musu ruwan sha, an hana musu wutar lantarki, an hana musu kuma mak**ashi k**ar mai da ire-irensu, an haramta musu komai, kuma an rutsa da su ana luguden wuta, kullu-yaumin ana kashe gomomi, har daruruwa ma wani lokacin, kuma galibansu mata da yara.”

Ya nuna takaicinsa akan yadda a sarari hukumomin Yammacin Duniya suke mara wa masu ta’asan bay aba tare da ko jin kunya ba, da kuma yadda ma’aikatansu na cikin al’ummar Musulmi suke nuna halin ko in kula akan lamarin. Yace: “Su da kansu sun fadi cewa, da ace al’ummar Musulmi za su zama al’umma daya, to da tuni sun mallaki wannan duniyar, don za su murkushe su ne gabadansu, saboda haka ba za su taba lamuncewa al’ummar Musulmi su zama abu daya ba.”

A nan ne ya yi kira da babban murya da cewa, mutum ya k**ata ya yi nazarin wa yake ma aiki? Yace: “Mun sha fada, mukan nanata, ba sau daya ba, ba sau biyu ba, cewa, duk wanda aka ji yana kira ga rarraban kawaukan Musulmi, ya yarda ko bai yarda ba, ya sani ko bai sani ba, yana ma makiya aiki ne. Ko ya yarda, ko kar ya yarda. Ko ya sani, ko kar ya sani, yana ma makiya aiki ne. Domin (kira ga rarraban Musulmi) aikin makiya ne, shirinsu ne rarraba din.”

Shaikh Zakzaky ya nuna takaicinsa akan yadda al’umar Musulmi s**a mai da abinda ya dame su shi ne abinda ya raba su, maimakon lura da abinda s**a hada su. Yace, ba mu ce ba abinda ya raba su ba. Inda ya bayyana al’ummar da Manzon Allah (S) ya koma ga Allah (T) ya barta dore akan addini, a matsayin wacce tata bamu gadon wasu abubuwa, daga ciki har da sabani akan shugabanci. Yace: “Ba a samu sabani akan matsayin Allah Ta’ala, da kasancewarsa Shi ne kadai abin bauta ba. Ba a samu sabani akan cewa Manzon nan shi ne Bawan Allah kuma Manzon Allah. Ba wani wanda yake kiranshi da ubangiji, ko dan ubangiji, ko daya daga wanda s**a taru s**a hadu s**a yi ubangiji. Har ma a Tashhud din mu, sai mun ambaci shi bawa ne, kafin mu ce shi Manzo ne. Kullum sai mun ce; ‘Wa ashhadu anna Muhammadan Abduhu wa Rasuluh.’ Saboda haka bamu da sabani kan matsayin Manzon Allah.”

Ya kara da cewa: “Kuma ba mu da sabani akan Alkur’ani. Duk da za ku ji zancen wawayen gari suna cewa akwai wasu masu Alkur’ani daban, amma fi’ilan dai Alkur’ani kwara daya ne, ba kari ba ragi.” Yace: “Amma al’umma ta saba akan fassaran Alkur’ani da kuma ruwayoyi. Don haka aka samu abinda ake ce ma Firka. An samu Firqoqi, an samu Mazhabobi, an samu Dariqoqi. Duk wannan a cikin addinin suke.”

Yace: “Duk lokacin da muke magana akan Firqa, ko Mazhaba, ko Darika, muna magana ne akan Juz’i (wato bangare). Amma in muka zo muna magana akan Musulunci, muna magana ne akan abinda ya dora akan duka wadannan. Shi Musulunci ne a sama. Su wadannan karkashin Musuluncin suke. Duk wanda ka ji yana rigima akan Firqa, to yana rigima akan bangare ne, ya bar tushe, ya bar asali yana magana akan reshe. Haka wanda yake rigima akan Mazhaba ko Darika, shi ma ya bar tushe ne ya koma reshe, don duk wadannan rassa ne… Da ma yanzu da ake yayin kungiyoyi. Dukkansu bangarori ne, ba su ne asasi ba, ba su ne kuma asali ba.”

Shaikh Zakzaky (H) ya jaddada cewa: “Mu muna magana akan asali ne. Sunanmu Musulmi, ba sunanmu wadannan rarrabe-rarrabenba, sunan al’ummarmu Musulmi. Shi ne Allah Ta’ala Yake cewa: “...هُوَ سَمَّاكُمُ الْمُسْلِمِينَ مِن قَبْلُ وَفِي هَٰذَا لِيَكُونَ الرَّسُولُ شَهِيدًا عَلَيْكُمْ وَتَكُونُوا شُهَدَاءَ عَلَى النَّاسِ ۚ...” Wato tun farko ma Shi Allah Ta’ala ne ya ambaci addinin babanku Ibraheem da Musulunci, da kuma a wannan lokacin wannan Manzon, domin ku zama shaida ga sauran al’ummu, kuma Manzo ya zama shaida akanku.”

Jagora yace, “Yanzu ana ta kiraye-kirayen sunannaki, da daukan kowane suna a matsayin shi ne ma addini, ai ta rigima akai, da kuma katangar karfen da aka sa a kwakwalwa, wanda babu katangar sam, ba ta da wujudi sam-sam, amma sai a kirkire ta a raba tsakanin al’umma, har mutum ya rika ganin cewa, wancan tsakaninsa da shi akwai shamaki, ra’ayinsu daban ne, fahimtarsu daban ne, har ma in ta yi k**ari ma sai yace addininsu daban ne. Alhali katanga aka saka masa a kwakwalwarsa, wadda ta fi katangar karfe karfi, saboda ta raba shi da dan uwansa Musulmi, alhalin addininsu guda.”

Yace: “Wannan lokacin da muke ciki, ba mu son ya zama sai makiya ne za su ingiza mu izuwa ga hadin kai, domin shi hadin kan nan a cikin addinin namu ne yake. Umurni ne na Allah Ta’ala; “Ku yi riko da igiyar Allah gabadayanku, kar ku rarraba.” Aka nuna illan rarraba tun a na farko. Sannan shi wannan Manzo (S) ya k**anta al’ummar Musulmi da misalin jiki guda, wanda idan wani bangare nasa ya yi ciwo, duk sauran bangarorin za su amsa da rashin bacci da kuma zazzabi. Idan aka taba wani bangare, duk gabadaya jiki ke amsawa. To haka al’ummar Musulmi suke, tamkar jiki guda ne.”

Shaikh Zakzaky ya bayyana wajabcin al’ummar Musulmi su hada kai su zama abu guda, da kuma haramci da munin rarrabuwa, wanda yace rarraba mummunan abu ne wanda zai kai ga mummunan natija. “Har wadanda ba suna addininmu ba ne, Allah Ya gaya mana cewa a hade suke wajen gaba da mu. “وَالَّذِينَ كَفَرُوا بَعْضُهُمْ أَوْلِيَاءُ بَعْضٍ ۚ إِلَّا تَفْعَلُوهُ تَكُن فِتْنَةٌ فِي الْأَرْضِ وَفَسَادٌ كَبِيرٌ” Yace, ‘Wadanda s**a kafirce tare suke sun damfaru da juna, in ku Muminai ba ku yi irin wannan ba (ku zama sashenku majibinta sashe ne), to za a samu fitina babba a doron kasa, da fasadi. Kuma yanzu abinda yasa duniya ta fada halin da take ciki kenan, saboda wadanda aka dora musu alhakin koyar da sauran al’umma sun raba kansu suna fada.”

Jagora ya bayyana cewa: “Ba mu da alami, wanda zai hada mu gabadayanmu ba tare da rarraba ba k**ar shi Manzon nan (S) da ya zo da addini. Shi ne Qudwa, shi ne abin koyi, shi ya zo da addini, shi ya aikata addini, ya dora mutane akan addinin, to wannan koyarwar na shi kan kansa, shi ne alami. Domin shi ne wanda za a gani a kwafa. Allah Ta'ala yana cewa: “لَّقَدْ كَانَ لَكُمْ فِي رَسُولِ اللَّهِ أُسْوَةٌ حَسَنَةٌ” Muna da kyakkyawan misali ga Manzon Allah (S), abin koyi ne shi wanda za a gani a kwafa. In muka sa Manzon Allah gabadayanmu a matsayin madubi wanda za mu kalla, mu yi koyi da shi, to duk za mu ga mun dunkule mun zama abu guda.”

Yace: “Yana da kyau mu fahimci cewa lallai hadin kan nan wajibinmu ne, kuma lallai shi ne karfinmu, shi ne daukakanmu, dolenmu ne mu yi, kuma bamu son ya zama makiyanmu ne za su tilastamu mu yi, za mu yi ne domin addininmu ne ya umurcemu da mu yi, domin in mun yi ibada ne. Saboda haka kira ga hadin kan al’ummar Musulmi shi ma ibada ne, wanda kuma duk ka ji yana kira zuwa ga rarraban al’ummar Musulmi, shi kuma yana fada da wannan Ibadan ne, yana kokarin ya rusa al’ummar ne.”

Jagora ya bayyana cewa, akwai wadanda duk yadda ake kira ga hadin kai, ba za su daina kira ga rarraba ba, saboda yin hakan sun dauke shi a matsayin kasuwanci ne da suke samu da shi. Yace: “Wadannan mutane ba za su cutar da mu da komai ba. Kamata ya yi wadanda suke kira ga haduwar al’umma din, su su tsaya wajen kira ga al’umma da haduwarta a aikace, ba kawai a zance ba. Domin haduwarmu a matsayinmu na al’ummar Musulmi, shi ne zai fitar da dukkanin al’umma (daga halin da take ciki).”

Jagora ya tabbatar da cewa, insha Allahul Azeem al’ummar Musulmi za su kasance al’umma daya. “Muna shekarun fata ne, ba muna shekarun rashin fata ba ne, muna fata Allah Ta’ala Ya gaggauta bayyanar wanda da bayyanarsa ne za a samu mafita. Domin mun san cewa alkawari ne Ya yi, kuma ba Ya saba alkawari. Lallai addinin nan zai dawo, kuma zai mallaki duniyar nan gabadayanta k**ar yadda ya mallaka”

“Allah Ta'ala Yana cewa:

وَعَدَ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنكُمْ وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَيَسْتَخْلِفَنَّهُمْ فِي الْأَرْضِ كَمَا اسْتَخْلَفَ الَّذِينَ مِن قَبْلِهِمْ وَلَيُمَكِّنَنَّ لَهُمْ دِينَهُمُ الَّذِي ارْتَضَىٰ لَهُمْ وَلَيُبَدِّلَنَّهُم مِّن بَعْدِ خَوْفِهِمْ أَمْنًا ۚ يَعْبُدُونَنِي لَا يُشْرِكُونَ بِي شَيْئًا ۚ وَمَن كَفَرَ بَعْدَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْفَاسِقُون.“

Suratun Nuor, 55.

A ranar Juma’a da ta gabata 12 ga Rabi’ul Auwal 1447 ne Harkar Musulunci karkashin Jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) ta fara gudanar da taron makon hadin kan Musulmi a garin Abuja. An tsawon kwanakin biyar a jere zuwa 17 ga watan, an saurari jawabai daga Malaman bangarori da darikokin Musulmi daban-daban daga sassan kasar nan, da s**a hada da da darikar Tijjaniyyah, da darikar Kadiriyya, da Ahlus-Sunnah, da kuma mabiya Mazhabar Ahlulbait (AS).






10/September/2025

ABUBUWAN MAMAKIN DA S**A FARU RANAR HAIHUWAR MANZON ALLAH— Daga Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)"Duniya ta haskaka ran...
10/09/2025

ABUBUWAN MAMAKIN DA S**A FARU RANAR HAIHUWAR MANZON ALLAH

— Daga Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H)

"Duniya ta haskaka ranar haihuwar Annabi. Kuma wadansu mu'ujuzozi daban-daban sun auku duk ranar haihuwar Annabi, an ga Gumaka rannan sun sunkuya, an ga katangar kisra ta tsage rannan, wanda har yanzu tana nan tsagaggiyar ta tun randa ta tsage a haihuwar Annabi (har yanzu). Wato in mutum ya je a Mada'in wasu kila sun je, za su ga wata katugar katanga, dayake katanga ake cewa (amma) soro ne, ban san yadda s**a yi soron ba, amma mun san yadda ake soro mu muna yin soro ya zama ainihin mun hada azarori ne, yauwa.

"To su kuwa wannan ya s**a yi katon zaure hamshaqi, da soro mai tulluwa, amma kuma bashi da al'amudai, ya s**a yi, da wane irin technology s**a yi a wancan lokaci wallahu a'alam, amma sai rabinsa ya rubda, kuma sauran ragowar yana nan har yanzu, ya zama kango ana zuwa amna ziyartansa a Mada'in cikin Iraq na yanzu, don lokacin Mada'in nan ne daular Farisa.

"To ranar haihuwar Manzon Allah wannan ya b***e, kuma ranar haihuwar Manzon Allah aka ga wutar da ma'abota zardusta su ke bautawa sai ta mutu. Wutar da ba su taba ganin mutuwar ta ba, wani ya ga tun ya na jariri ya ke ganin ta har ya girma, har ya tsufa wutar ba a taba ganin mutuwar ta ba.

"Na'am wuta ce, wani mai ne da'iman su ke zubawa, to rannan duk man da su ka malala rannan kawai bum ya mutu, aka kunna ma ya ki kunnuwa, saboda rannan akwai wani abu da ya faru-ranar haihuwar Manzon Allah kenan. Da wadansu mu'ujuzozi daban-daban da aka gani wanda ya ke nufin albishirinku duniya, mai cetonku na nan tafe, yauwa.

— Jagora Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) yayin jawabinsa na ganawa da wakilan 'yan uwa a ranar haihuwar Manzon Allah a shekarar 2023 a gidansa da ke Abuja.

— Cibiyar Wallafa Ayyukan Shaikh Zakzaky





17 Rabi'u Auwal 1447
10 September 2025

Address

Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Cibiyar Wallafa Ayyukan Shaikh Zakzaky posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Cibiyar Wallafa Ayyukan Shaikh Zakzaky:

Share