Maibiredi Tv

Maibiredi Tv Domin kawo maku rahotanni akan al'amurran yau da kullum.
(2)

za ku iya kiranmu a +2348069807496 ko ku biyo mu a Whatsapp Channel ta wannan rariyar liƙau: https://whatsapp.com/channel/0029VanmLGu2Jl86PakU7U3G

Me za ku ce
11/05/2026

Me za ku ce

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Naira Biliyan 250 Wajen Gina Dakunan Kwanan Dalibai ​Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin ...
11/05/2026

Gwamnatin Tarayya Za Ta Kashe Naira Biliyan 250 Wajen Gina Dakunan Kwanan Dalibai

​Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin kashe kudi kusan naira biliyan 250 a cikin shekarar 2026 domin gina sabbin dakunan kwanan dalibai a manyan makarantun gaba da sakandare na kasar nan.

​Wannan mataki na kunshe ne a cikin wani babban shiri na kyautata jin dadin dalibai da kuma fadada damar samun ilimi mai inganci, wanda ake ganin shi ne jari mafi tsoka da aka taba zubawa a fannin gidajen dalibai a tarihin Najeriya.

​Ministan Ilimi, Maruf Olatunji Alausa, ya bayyana cewa wannan shiri zai magance matsalolin karancin masauki da dalibai ke fuskanta.

Za a kashe naira biliyan 100 wajen gina dakunan kwanan dalibai masu dauke da gado 500 a kowace jami'a daga jami'o'i guda 50 a fadin kasar nan. Kowanne aiki daya an kiyasta shi a kan naira biliyan 2.

​Za a gudanar da wasu ayyukan guda 24 na hadin gwiwa da masu zuba jari masu zaman kansu, inda gwamnati za ta bayar da biliyan daya, su kuma masu zuba jari su bayar da biliyan 3 a kowanne aiki. Wannan zai samar da masauki ga dalibai tsakanin 1,200 zuwa 1,500 a kowace makaranta.

​Hukumar tallafawa manyan makarantu ta TETFund ce za ta dauki nauyin samar da wadannan kudade, inda za a yi amfani da su wajen gina sabbi da kuma gyara tsofaffin dakunan kwanan dalibai da s**a lalace.

​Babban burin wannan shiri shi ne samar da yanayi mai kyau na koyo da koyarwa, tare da rage cinkoson dalibai a daki daya da ake samu a manyan makarantun kasar nan a halin yanzu.

​"Wannan shiri ne da zai tabbatar da cewa dalibanmu sun samu wurin kwana mai tsafta da walwala, wanda hakan zai taimaka musu wajen mayar da hankali kan karatunsu." — Maruf Olatunji Alausa

​Masana ilimi sun yi amanna cewa idan har aka kammala wadannan ayyuka, za a samu sauki kwarai wajen rage kuncin da daliban jami'o'i da kwalejoji ke fuskanta, musamman 'ya'yan talakawa da ke dogara da masaukin makaranta.

11/05/2026

Wajen kokarin yiwa yan Arewa sharri ya gamu da nashi gamon.

11/05/2026

Yadda yan bindiga kaiwa matafiya hari s**a halaka 10 tare da jikka da dama a hanyar Gusau zuwa Magami a karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara

11/05/2026

I got over 5,000 reactions on one of my posts last week! Thanks everyone for your support! 🎉

11/05/2026

Abin da Ibrahim Ibrahim Wambai ya yi bangaren ilimi kurrum ya isa Al'ummar Gusau 1 su kara zabensa karo na biyu- Clever

APC ta tantance sirikin Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda a matsayin dan takarar majalisar wakilaiJam'iyyar APC mai mulk...
11/05/2026

APC ta tantance sirikin Gwamnan jihar Katsina Dikko Radda a matsayin dan takarar majalisar wakilai

Jam'iyyar APC mai mulki a Nijeriya ta tantance Ahmad Uthman Muhammad a matsayin dan takarar majalisar wakilai

Ahmad Uthman Muhammad wanda surukin gwamnan jihar Katsina Dikko Radda ne dake auren yar gwamnan wato Aisha Dikko Radda

Ahmad ya wallafa a shafinsa cewa APC ta tantance shi cikin nasara

Ya fito takarar majalisar wakilai ta mazabar Yola South, Yola North and Girei Federal Constituency a jihar Adamawa

11/05/2026
11/05/2026

Fim ya zama gaske! Vijay Thalapathy ya shiga ofis a matsayin babban Ministan Tamil Nadu.

Jama'a sun nuna masa ƙauna tsantsa a ƙasar Indiya, fata dai Allah Ya fidda shi jin kunyarsu.

11/05/2026

Hon. Ahmad Lawal Lala, mai neman takarar kujerar ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Gusau da Tsafe a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya yanke fom ɗin tsayawa takara a hukumance domin fafatawa a zaɓe mai zuwa.
Muna roƙon addu’a da goyon bayan al’umma domin samun nasara.



11/05/2026

Yan Nigeria sun fara kokawa kan mita mai amfani da kati wanda sunce Sam bata dace da talakka ba.

Address

Oranti Plaza Eastern Bypass Opposite Salbas (MAIGORO) Filling Station Gusau
Gusau
632101

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Maibiredi Tv posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Maibiredi Tv:

Share

Category