29/07/2025
Gwamna Bala Mohammed Ya Jagoranci Sulhu Tsakanin Manoma Da Makiyaya A Yankin Darazo Dake Bauchi
A kokarinsa na tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar Bauchi, Gwamnan Jihar, Sanata Bala Abdulƙadir Mohammed, ya jagoranci wani muhimmin zaman sulhu tsakanin manoma da makiyaya a karamar huk*mar Darazo.
Zaman wanda ya gudana sakamakon sabani da aka samu a 'yan kwanakin baya tsakanin manoma da makiyaya, ya samu halartar manyan jami’an tsaro na jihar da sauran masu ruwa da tsaki. Manoma sun zargi makiyaya da hana su gudanar da harkokin noma, lamarin da ya kai ga raunata wasu daga cikinsu.
Gwamna Bala, cikin jawabin da ya gabatar a taron, ya jaddada cewa makiyayi da manomi suna bukatar juna, k*ma babu wani da zai iya rayuwa cikin kwanciyar hankali ba tare da dayan ba. Ya ce: Abune sananne tun tarihi haka ake zaune cikin girmama juna da kauna.
Gwamna yace “Gwamnatina zata tabbatar da cewa manomi ya zauna a filin da aka ware masa don noma, haka makiyayi ma zai tsaya a filin kiwonsa ba tare da take hurumin juna ba.”
Ya k*ma bayyana cewa daga wannan shekara, duk wanda yayi noma a kan layin hanyar mota ko kusa da manyan hanyoyi zai fuskanci hukunci, domin hana rikice-rikice da k*ma kare rayuka da dukiyoyin jama'a.
Kwamishinan 'yan sanda na jihar Bauchi, CP Sani Aliyu Omolori, shima ya yi bayani kan matakan da s**a dauka kafin da bayan aukuwar rikicin, yana mai tabbatar da aniyarsu na tabbatar da doka da oda a kowane bangare na jihar.
A karshe, dukkan bangarorin biyu sun samu damar yin bayani da bayyana matsalolinsu cikin lumana, lamarin da ke nuna cewa akwai fatan samun daidaito da fahimtar juna nan gaba. Kuma SYLHU ya zauna da da yardan Ubangiji. Wanda hakan ne fatan kowa.
Lawal Muazu Bauchi
Mai taimakawa Gwamna Bala
Kan harkokin sabbin kafafun sadarwar zamani