HG TV

HG TV HGTV ingantacciyar majiya ce dake yada labarai da shirye-shiryen siyasa, mata, yara, wasanni, nishadi, tsaro, kiwon lafiya, kasuwanci da dai sauran su.
(2)

"HG TV: DA GASKIYA AKA SAN KI"
Domin bada talla da sanya labaran ku kira ko WhatsApp +2348032629076

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allah ya amshi rayuwar Jarumar Kannywood, Zainab Zee Diamond bayan fama da doguwar j...
07/09/2026

Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Allah ya amshi rayuwar Jarumar Kannywood, Zainab Zee Diamond bayan fama da doguwar jinya.

Ta rasu bayan sallar asuba.

Allah ya jikan ta da rahama ya mata gafara ya yafe mata kurakuran ta 🤲🤲🤲

28/08/2026

Juma'at Mubarak 🙏

Allah ya biya mana bukatun mu, ya Bude mana 'kofofin samu ya kare mu daga sharrin makiya🤲

Wani bidiyo da tsohuwar Jarumar Kannywood, Rukayya Dawayya ta wallafa a shafin ta ya tayar da kura a kafafen sada zumunt...
06/08/2026

Wani bidiyo da tsohuwar Jarumar Kannywood, Rukayya Dawayya ta wallafa a shafin ta ya tayar da kura a kafafen sada zumunta.

Rukayya Dawayya ta wallafa bidiyon tana nuna yadda ake shirya jigidar, inda ta ce ta binne ta na tsawon watanni shida, sannan a yi mata saukar karatun Al-Qur'ani tare da kunna turaren wuta na kwanaki kafin a fitar da ita.

Bayan yaɗuwar wannan bidiyon, masu amfani da kafafen sada zumunta sun fara bayyana ra'ayoyi mabanbanta, inda wasu ke cewa shin wannan jigida ba ta asiri ba ce ko kuwa wata hanya da ake amfani da ita domin burge miji?

Wasu ma sun ce tabbas wannan al'amari shirka ne 'karara kuma ya sa'ba wa ka'idodin Musulunci.

Me zaku ce akan wannan batu?

Like, comment, share, follow HG TV

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya gwangwaje mijin marigayiya Malama UmmulKhairi da aka hallaka  a Maraban Jos, Ma...
04/08/2026

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani ya gwangwaje mijin marigayiya Malama UmmulKhairi da aka hallaka a Maraban Jos, Malam Usman Aliyu da gida.



Like, share, comment, follow HG TV

24/07/2026

Wasu ayoyi masu albarka daga Suratul Rum masu jan hankali.



Like, share, comment, follow HG TV

A dai-dai lokacin da siyasar Jihar Gombe ke cigaba da zafi da ɗaukar sabon salo, d'an takarar Gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙ...
23/07/2026

A dai-dai lokacin da siyasar Jihar Gombe ke cigaba da zafi da ɗaukar sabon salo, d'an takarar Gwamnan Jihar Gombe a ƙarƙashin Jam'iyyar APC, Alhaji Jamilu Isyaku Gwamna ya bayyana cewa bai iya zagi da cin mutunci ba saboda gidan su gidan mutunci ne kuma shi siyasa a jinin jikin sa take.

Sai dai waɗan nan maganganu da Alhaji Jamilu Gwamna yayi suna ci gaba da tayar da kura a kafafen sada zumunta.

Shin ya kuke ganin lamarin zai kasance? Ku bayyana mana ra'ayoyin ku.

Iyalan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai sun musanta wata wasiƙa da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda...
23/07/2026

Iyalan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai sun musanta wata wasiƙa da ke yawo a kafafen sada zumunta, inda ake ikirarin cewa shi ne ya rubuta ta kuma ya sanya hannu.

A cewar sanarwar da Mohammed Bello El-Rufai ya fitar a madadin iyalan, wasiƙar mai taken 'Saƙon Gaggawa wacce ke dauke da kwanan watan 14 ga Yuli, 2026 ta bogi ce.

Sanarwar ta ce tsohon Gwamnan bai rubuta wasiƙar ba, kuma ba ta fito daga gare shi ba.

Sun kuma ce abin da ke cikin wasiƙar da rubutun hannun da ke cikin ta ba su da alaƙa da Malam El-Rufai, inda s**a yi kira ga jama'a da su yi watsi da ita.

Iyalan sun zargi masu ƙirƙirar wasiƙar da ƙoƙarin haddasa ruɗani da rarrabuwar kawuna saboda dalilan siyasa.

Wasiƙar da ake yaɗawa ta yi iƙirarin cewa an samu saɓani a cikin Jam'iyyar ADC kan batun ɗan takarar Gwamna a Jihar Kaduna, amma iyalan sun jaddada cewa wasiƙar ƙirƙirar ta kawai aka yi.

Me za ku ce akan wannan batu?



Like, share, comment, follow HG TV

23/07/2026

Rundunar 'yan sandan Jihar Kano ta cafke wasu mutane da ake zargin suna fashin adaidaita sahu a wasu sassa daban-daban na Jihar.

Rundunar na ci gaba da gudanar da bincike, ayayin da ta jaddada aniyarta ta ci gaba da yaƙi da masu aikata laifuka domin tabbatar da tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al'ummar Jihar.



, comment, share, follow HG TV

Wani mahaifi mai suna Malam Lawal Hamisu ya shigar da ƙara a gaban Kotun Shari’a ta biyu dake Magajin Gari a Jihar Kadun...
23/07/2026

Wani mahaifi mai suna Malam Lawal Hamisu ya shigar da ƙara a gaban Kotun Shari’a ta biyu dake Magajin Gari a Jihar Kaduna, inda yake neman Kotun ta umarci ’yar sa, Fatima Lawal ta gabatar da wanda zai aure ta.

Mai ƙarar ta bakin lauyan sa, H.B. Debo ya shaida wa kotun cewa 'yar sa Fatima mai shekara 27 ta kammala karatun HND amma har yanzu ba ta gabatar da wani mutum da ya nemi auren ta a hukumance ba.

Malam Lawal ya ce duk da cewa ’yar sa tana da samari, babu wanda ya taɓa zuwa gidan su domin neman auren ta.

Ya buƙaci kotun ta umarce ta da ta fito da wanda zai aure ta, sannan ta taimaka wajen ganin an ɗaura auren idan an cika sharuddan da s**a dace.

Malam Lawal ya kuma yi zargin cewa mahaifiyar Fatima ce ta haddasa matsalar da ke tsakanin sa da ’ya’yan sa.

A nata ɓangaren kuwa, Fatima ta musanta cewa tana da wanda ya nemi auren ta.

Ta na mai cewa duk da kasancewar ta tana da abokai maza, babu wani da ya gabatar da kan sa ga iyayen ta a matsayin mai neman auren ta.

Da yake jawabi, Alƙalin kotun, Malam Yakubu Abdullahi ya bayyana cewa shari’ar ta shafi dangantakar uba da ’yar sa, don haka tana buƙatar a yi taka-tsantsan kafin a yanke hukunci.

Alƙalin ya ce zai saurari kowanne ɓangare a lokuta daban domin gano ainihin musabbabin rikicin kafin ya yanke hukunci.

Daga nan kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 3 ga watan Agustan shekarar nan ta 2026.



Like, share, comment, follow HG TV

Shugaban Amurka, Donald Trump ya janye sojojin Kasar sa daga Najeriya.Daga wakiliyar mu Fatima Sha'aban.Gwamnatin Amurka...
03/07/2026

Shugaban Amurka, Donald Trump ya janye sojojin Kasar sa daga Najeriya.

Daga wakiliyar mu Fatima Sha'aban.

Gwamnatin Amurka ta sanar da janye mafi yawan dakarun ta da ta tura Najeriya domin taimakawa a yaƙi da ƙungiyoyin ta’addanci a yankin Tafkin Chadi.

Sanarwar ta fito ne daga Kwamandan Rundunar Sojin Sama ta Amurka da ke kula da Turai da Afirka, Janar Dagvin Anderson yayin da yake yi wa manema labarai bayani bayan taron Hafsoshin tsaro na Afirka na shekarar 2026.

A cewar sa, an kammala aikin haɗin gwiwar da aka tura sojojin domin gudanar wa, saboda haka aka janye yawancin su zuwa Amurka.

Sai dai Janar Anderson ya tabbatar da cewa Amurka ba za ta daina tallafa wa Najeriya ba domin za ta ci gaba da bayar da gudunmawa ta hanyar musayar bayanan sirri, ba da horo da kuma sauran nau’o’in haɗin gwiwar tsaro.

Ya ce haɗin gwiwar da ke tsakanin Amurka da Najeriya ya taimaka wajen raunana ayyukan Ƙungiyar ISIS da sauran ƙungiyoyin ta’addanci da ke addabar yankin Tafkin Chadi.

Haka kuma ya yaba wa Rundunar sojin Najeriya, yana mai cewa tana da ƙwarewa da ƙarfin gudanar da ayyukan tsaro, yayin da haɗin gwiwar Ƙasashen biyu ya samar da gagarumar nasara wajen yaƙi da ta’addanci.

Janar Anderson ya ce haɗin bayanan sirri tsakanin Amurka da Najeriya ya taimaka wajen kai farmakin da ya yi sanadin kashe Abu-Bilal Al-Minuki, wanda ake zargin shi ne mataimaki na biyu a jagorancin Ƙungiyar ISIS ta duniya.

Ya kuma yi kira ga Ƙasashen Afirka da su ƙara ƙarfafa musayar bayanan sirri domin yaƙar ta’addanci da safarar miyagun ƙwayoyi da sauran laifukan da ke ketare iyakokin Ƙasashe.

Like, share, comment, follow HG TV

Address

Kado
Abuja
900108

Telephone

+31208919899

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when HG TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to HG TV:

Shortcuts

Share