19/08/2026
Cikin hotuna yanda Rundunar Agaji ta Fityanul Islam Adamawa Ta Tattauna da Daraktocin Ćananan Hukumomin Central Zone Kan Tsaron Zagayen Maulidi
A yau, Rundunar Agaji ta Fityanul Islam, Reshen Jihar Adamawa, ta gudanar da wata muhimmiyar ganawa da Daraktocin Ćananan Hukumomin Central Zone na Jihar Adamawa, domin samun maslaha da fahimtar juna tare da tsara yadda za a gudanar da zagayen Maulidin ranar 12 ga watan Rabiâul Awwal cikin tsari, zaman lafiya da bin Ćaâidojin addini.
Ganawar ta mayar da hankali ne kan yadda za a samar da cikakken tsari wajen gudanar da zagayen, musamman ganin cewa a shekarun baya an samu wasu bata-gari da ke shiga cikin masu wannan ziyarar, inda wasu daga cikinsu ke bayyana da tufafin da ba su dace da taron addini ba tare da aikata wasu abubuwa da s**a saÉa wa Ćaâidojin Shariâa da kuma tarbiyyar Musulunci.
Saboda haka, a wannan shekarar, Rundunar Agaji ta Fityanul Islam ta yi ingantaccen shiri na musamman, tare da haÉin gwiwar jamiâan tsaron gwamnati, domin tabbatar da tsaro, kare mutuncin taron, da kuma dakile duk wani yunĆuri na kawo rashin tsari ko aikata abubuwan da s**a saÉa wa dokokin Ćasa da koyarwar Musulunci.
Haka kuma, ganawar ta kasance wata dama ta Ćarfafa haÉin kai tsakanin Rundunar Agaji ta Fityanul Islam da Daraktocin Ćananan Hukumomi, domin tabbatar da cewa dukkan masu ruwa da tsaki za su yi aiki tare wajen samun nasarar wannan gagarumin taro.
Rundunar ta jaddada cewa manufar wannan shiri ba wai hana mutane shiga cikin zagayen Maulidi ba ce, sai dai tabbatar da tsari, tsaro, kyawawan Éabiâu da mutunta dokokin addini da na Ćasa, tare da kare martabar wannan rana mai albarka.
A Ćarshe, Rundunar Agaji ta Fityanul Islam, Reshen Jihar Adamawa, ta yi kira ga dukkan mahalarta da masu son shiga cikin zagayen da su kasance masu bin doka, mutunta juna da kuma guje wa duk wani hali da zai iya kawo rashin zaman lafiya ko Éata martabar taron.
Da haÉin kan alâumma, shugabannin Fityanul Islam, Daraktocin Ćananan Hukumomi da jamiâan tsaro, ana sa ran gudanar da zagayen Maulidin na ranar 12 ga Rabiâul Awwal cikin tsari, aminci da zaman lafiya, in Allah Ya yarda.
E-sign
Aliyu samaila
State media and publicity