05/11/2025
Jawo hankalin duniya ga shirin inganta karatun allo da tsangayu
Daga Mukhtar A. Halliru Tambuwal, Sakkwato
An kammala dukkan shirye-shirye domin gudanar da babban taron ƙasa da ƙasa wanda ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirka ta Yamma ta ECOWAS da haɗin gwiwar ƙungiyar Tarayyar Ƙasashen Afirka ta AU s**a shirya, domin raya ilimin makarantun allo da tsangayu.
Jam'iyyatu Ansaruddeen Attijjaniya da haɗin gwiwar ECOWAS da AU ne s**a tsara taron domin kawo sauyi a harkokin zaman lafiya da tsaro, bunƙasa ilimin makarantun tsangaya da almajiranci.
An tsara cewa taron zai mayar da hankali ne wajen tattauna batun gudummawar ilimin almajiranci da ƙalubalensa, hanyoyin inganta tsarin karatun allo da almajiranci a Afirka ta Yamma, da duba darussa daga Nijeriya. Za kuma a duba batun amfani da hanyoyin Zakka da Waqafi wajen inganta ilimi da tattalin arziƙi a Afirka.
Taron wanda zai gudana gobe Alhamis 4 ga watan Nuwamba, 2025 a Babban Ɗakin Taro na ECOWAS da ke Abuja zai haɗo kan masu ruwa da tsaki a harkar ilimin addinin Musulunci, hafizai, alarammomi, masu makarantun tsangaya da na allo. Harwayau, akwai manyan jami'an gwamnati, jami'an tsaro, ƴan kasuwa, da masu masana'antu daga sassa daban-daban na Afirka.
Ana kuma sa rai da halartar wakilan ƙasashen larabawa da jakadun ƙasashen Libiya, Mauritania, Chadi, Kamaru, Masar, da Morocco har ma da Turkiyya da sauran su.
Daga cikin manyan bakin akwai Ministar Ilimi ta Nijeriya, Farfesa Suwaiba Ahmed da za ta wakilci uwargidan Shugaban ƙasa Sanata Oluremi Tinubu, da Babban Mashawarcin Ministan Ilimi Kan Harkokin Almajirai da Yaran Da Ba Sa Zuwa Makaranta, Hon. Kakaba Shehu Balarabe, Barden Makarantun Allo da Tsangayu na Ƙasar Hausa.
Sauran sun haɗa da Dr Muhammad Ibn Chambas Shugaban Hukumar ECOWAS, kuma Babban Wakilin AU game da yaƙi da bazuwar ƙananan makamai a Afirka. Shi ne kuma zai zama shugaba na biyu na wannan babban taro.