13/09/2025
Titinin Sokoto–Badagry Zai Ƙarfafa Kasuwanci a Yammacin Afirka...Minista
Daga Binta Aliyu, Birnin Kebbi
Karamin Ministan Ayyuka, Muhammad Bello Goronyo, ya yaba wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu bisa jajircewarsa wajen inganta ababen more rayuwa a ƙasar nan, duk da ƙalubalen tattalin arziki da ake fuskanta.
Goronyo ya bayyana hakan ne yayin da yake duba aikin t**in tare da Ministan Ayyuka, Sanata David Umahi, a jihohin Kebbi da Sokoto a ranar Juma’a. Ya bayyana cewa aikin gina babban t**in Sokoto–Badagry Superhighway na daga cikin manyan shaidun yadda gwamnatin ke mai da hankali wajen cigaban kasa.
Ya bayyana cewa t**in, wanda zai ratsa jihohin Sokoto, Kebbi da Neja, zai taimaka matuka wajen bunkasa tattalin arziki da harkokin kasuwanci, musamman a yankin Sokoto da Kebbi, kafin ya kai ƙarshen sa a Badagry, Jihar Legas.
"Wannan aiki ba na Jihohin Sokoto, Kebbi ko Neja kadai ba ne.
Aikin kasa ne, domin yana haɗa sassa daban-daban na ƙasa kafin ya kai Badagry a Legas," in ji Goronyo.
Ministan ya jaddada muhimmancin aikin musamman dangane da dangantakar sa da Kasuwar Duniya ta Illela, inda aikin zai fara. Ya ce,
“Wannan t**i zai bude sabbin damammakin kasuwanci a wannan yankin da ya kai fiye da kilomita 1,000, yana haɗa Najeriya da Nijar, Mali da sauran ƙasashen makwabta.”
Goronyo ya bayyana aikin a matsayin “mai sauya tarihi”, inda ya bukaci al’ummomin da aikin zai shafa da su yaba wa gwamnatin tarayya bisa wannan ƙoƙari.
"Ina kira ga al’umma da su fahimci muhimmancin aikin da ake yi, kuma su nuna godiya ga Shugaba Tinubu bisa kulawa da wannan yanki," in ji shi.
“Ba wai muna yin kamfen ba ne. Idan an kammala wannan aiki, babu bukatar mu dawo da kamfen, domin Shugaban kasa ya riga ya nuna ƙauna da kulawa ga al’ummarsa.”
A ƙarshe, Goronyo ya yaba da jajircewar Minista Dave Umahi wajen aiwatar da Manufar “Sabon Fatan” Shugaban Kasa, musamman a ɓangaren ayyukan more rayuwa.