15/01/2026
Da ɗumi-ɗumi: Ban damu ba don ɗana ya shiga Apc damuwata kawai yadd jam’iyyar APC ta saka 'yan Najeriya cikin Bala'in Talauci –Atiku Abubakar
Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa kuma jagoran jam’iyyar adawa, Atiku Abubakar, ya bayyana cewa matakin da ɗansa Abba Abubakar ya ɗauka na shiga jam’iyyar APC shawara ce ta kansa gaba ɗaya, ba tare da wani tilas ko matsin lamba daga gare shi ba.
Atiku ya ce a tsarin dimokuraɗiyya, irin waɗannan zaɓi ba abin mamaki ba ne, ko da kuwa siyasa da zumunci sun haɗu. Ya jaddada cewa shi a matsayinsa na ɗan dimokuraɗiyya, ba ya tilasta wa ’ya’yansa ra’ayi ko zaɓin siyasa, haka nan kuma ba zai tilasta wa ’yan Najeriya ba.
Sai dai Atiku ya nuna cewa abin da ya fi damunsa shi ne mulkin APC, wanda ya ce ya jefa ’yan Najeriya cikin matsanancin wahalar tattalin arziƙi da zamantakewa.
A cewarsa, talauci, tsadar rayuwa da rashin kyakkyawan shugabanci sun addabi jama’a.
Ya ƙara da cewa har yanzu yana tsayin daka tare da sauran ’yan kishin ƙasa masu ra’ayi ɗaya, domin maido da kyakkyawan shugabanci da kuma gabatar wa ’yan Najeriya madadin shugabanci nagari da zai kawo sauƙi, fata da cigaba.
“Dimokuraɗiyya ba tilas ba ce, amma APC ta kasa ba ta cika alkawari ga talaka ba,” in ji Atiku.