
26/05/2025
Mai-ɗakin shugaban Faransa, Macron ta kwaɗa masa mari
Wani bidiyo da ke nuna shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya sha mari a fuska daga hannun matarsa, Brigitte Macron, ya yadu sosai a kafafen sada zumunta.
Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a cikin jirgin shugaban kasa kafin su sauka a Vietnam, inda Macron ke fara wata ziyarar diflomasiyya a yankin Kudu maso Gabashin Asiya.
A cikin bidiyon, Macron na tattaunawa da Brigitte ne a bakin kofar jirgin lokacin da ta mika hannu ta buge shi a baki. Macron ya bayyana cikin mamaki, amma ya daidaita kansa cikin sauri sannan ya daga hannu yana gaisawa da ’yan jarida da ke jiran su.
Yayin da s**a sauka daga jirgin, Macron ya miƙa wa Brigitte hannunsa don su k**a hannu da hannu, amma ta ƙi, ta k**a sandar matattakala maimakon haka.
Bidiyon ya haifar da damuwa da muhawara, musamman saboda an dade ana tattauna dangantakar su. Brigitte na da shekaru 25 fiye da Macron, kuma ita ce malamar wasan kwaikwayo tasa lokacin da dangantakar su ta fara tun yana matashi.