04/10/2025
Warware Gurguwar Fahimta Kan Sauye-sauyen Harajin Kuɗin Shiga Na Gwamnatin Shugaba Tinubu
Rubutawa: Michael Chibuzo
Fassarawa zuwa Hausa: Aliyu Samba
Yayin da kwanaki ƙididdigaggu s**a rage mu shiga sabuwar Shekara ta 2026, ranar da sabbin dokokin haraji guda biyu za su fara aiki, labaran ƙarya da gurguwar fahimta game da waɗannan dokoki na haraji sun ƙaru sosai a kafafen sada zumunta. Wasu daga ciki suna bayyana ne sak**akon rashin sani, yayin da wasu da yawa kuma wata manufa ce ta siyasa da neman ɓata sunan Gwamnati. A wannan rubutu, zan yi ƙoƙarin warware wannan gurguwar fahimtar game da harajin kuɗin shiga (income tax) a cikin Dokar Haraji ta Najeriya, 2025.
Manyan Jita-jitan Da Aka Fi Ji:
1. Daga ranar 1 ga Janairu, 2026, ‘yan Najeriya za su fara biyan harajin kuɗin shiga mafi tsada.
2. Gwamnati za ta rika cire haraji kai tsaye daga asusun banki na mutum.
3. Gwamnatin Tarayya na neman ƙarin kuɗin shiga ta hanyar kakabawa ‘yan Najeriya haraji mai nauyi.
4. Sabbin dokokin haraji za su hana kasuwanci da haɓakar tattalin arziki.
Zan bisu daki-daki domin warwarewa.
1. SHIN ZA A ƘARA NE, KO KUMA RAGE HARAJIN KUƊIN SHIGA?
Gaskiyar magana ita ce, mafi yawan ‘yan Najeriya za a rage musu haraji sak**akon sabbin tanade-tanaden da ke cikin sabuwar dokar haraji ta 2025, inda aka ware mutanen da ke samun N800,000 ko ƙasa da haka a shekara daga biyan kowanne irin haraji. Ma’ana, ma’aikaci mai karɓar albashin mafi ƙaranci ko ƙasa da haka ba zai biya haraji ba kwata-kwata.
Wasu na iya cewa mafi ƙarancin albashin gwamnati yanzu N70,000 ne a wata (N840,000 a shekara), wanda ya fi N800,000 da aka ware. Haka ne, amma abin lura shi ne, ba duka kuɗin shiga ake kira taxable income ba. Akwai abin da ake kira (Taxable Income), wato abin da ya rage bayan an cire rangwamen da aka amince da shi k**ar:
• Kudin Inshorar Lafiya NHIS (kimanin 5% na albashi)
• Rangwamen haya (20% na haya da bai wuce N500,000 ba)
• Gudunmawar gidauniyar gidaje ta ƙasa NHF (2.5% na albashi)
• Gudunmawar fansho (8% na albashi)
• Inshorar rayuwa, na ka da iyalin ka.
Misali, ma’aikacin da ke karɓar N70,000 a wata (N840,000 a shekara) kuma yake biyan haya N200,000 a shekara, tare da kudin Inshorar lafiya na NHIS, NHF da fansho, zai sami taxable income na N710,800 kacal. Wannan yana cikin iyakar nan da ta ware masu samun N800,000, hakan ya nuna ba zai biya haraji ba.
Ko wanda ke karɓar N80,000 a wata (N960,000 a shekara) zai iya shiga cikin waɗanda aka ware idan an yi amfani da irin waɗannan tsarin. A taƙaice, talakawa da ƙananan ma’aikata sun samu sauƙi, sai masu kuɗi sosai ne za su ɗan biya fiye da da.
2. SHIN ZA A CIRE HARAJI KAI TSAYE DAGA BANKI?
Amsar ita ce A’A! Ba za a rika cire haraji kai tsaye daga asusun bankin mutum ba.
Abin da dokar Haraji ta 2025 ta tanada shi ne, sashe na 29 ya wajabtawa bankuna su rika ba hukumar haraji rahoton masu asusu waɗanda ke da mu’amalar banki har ta fiye da Naira Miliyan 25 a wata ga mutum ɗaya, da Naira Miliyan 100 ga kamfani. Wannan ba yana nufin su cire haraji bane, bayanan ne kawai suke tattarawa don gano masu kuɗi da ke gujewa biyan haraji.
Mutanen da mu’amalarsu ba ta kai Naira Miliyam 25 a wata ba, ba zai shafe su ba kwata-kwata. Kuma a yanzu, fiye da kaso 90% na ‘yan Najeriya ba su da kuɗaɗen da s**a kai wannan adadi a asusun banki.
3. SHIN GWAMNATIN TARAYYA NA NEMAN KUƊI NE TA HARAJI?
Amsar ita ce A’A!
A haƙiƙa, sabbin dokokin an yi su ne domin rage nauyin haraji ga talakawa. Harajin kuɗin shiga da ake magana akai ma, ba na gwamnatin tarayya ba ne kai tsaye. Sashe na 3(2) na dokar haraji ta ƙasa ya bai wa Jihohi ikon karɓar harajin kuɗin shiga daga mutanen da ke zaune a cikin jihohinsu. Gwamnatin Tarayya kawai tana tattara haraji ne daga ma’aikatan soji, ma’aikatun diflomasiyya na ƙasashen waje, da kuma mutanen waje da ke samun kuɗi daga Najeriya.
Saboda haka, jihohi ne suke cin gajiyar harajin kuɗin shiga, ba gwamnatin tarayya ba. Wannan ke nuna cewa ba wai gwamnati na neman karin kuɗi daga talakawa bane, a’a, ana ƙoƙarin kawo sauƙi ne.
4. SHIN SABON DOKAR HARAJI ZAI HANA TATTALIN ARZIKI CI GABA?
A’a, akasin haka ne. Sabbin dokokin suna nufin taimaka wa ƙananan ƴan kasuwa ne da masu ƙaramin karfi.
Misali:
• Dokar haraji ta ƙasa ta ware ƙananan kamfanoni (masu juya kuɗin da bai kai Naira Miliyan 100 ba a shekara) daga biyan harajin riba gaba ɗaya. Wannan ya kai sama da kaso 90 cikin 100 na kamfanoni a Najeriya.
• Manyan kamfanoni kuwa za su ci gaba da biyan kaso 30% na Harajin Kuɗaɗen Shiga na Kamfanoni, amma akwai tanadi a doka cewa za a rage shi zuwa kaso 25% idan Kwamitin Tattalin Arziƙi na ƙasa da Jihohi sun tabbatar hakan ba zai cutar da ribar da ke shiga asusun tarayya ba.
Idan dokokin za su hana ci gaba, za a ƙara Harajin Kuɗaɗen Shiga na Kamfanoni zuwa fiye da kaso 30%,, amma abin da sabuwar doka ta tanada ragewa yake, ba ƙarawa ba.
KAMMALAWA
Daga abin da muka gani, sabbin dokokin haraji, musamman na kuɗin shiga al’amari ne mai sauƙi, domin zai kare talakawa ne, tare da goyon bayan ‘yan kasuwa ƙanana da nufin ƙarfafa ci gaban tattalin arziki.
Jihohi da hukumomin haraji ya k**ata su gudanar da wayar da kai sosai domin mutane su fahimci gaskiyar abin da aka tanada, maimakon su saurari jita-jita marasa tushe.
A ƙarshe, dole ne mu gane cewa biyan haraji nauyi ne na ‘yan ƙasa. Duk wanda ya cancanci biyan haraji bai da hujjar guduwa. Wannan sabuwar doka ma ta sanya masu kuɗi da manyan kamfanoni su kasa gujewa biyan haraji. Idan hakan ya tabbata, zai ƙara wa jama’a ƙarfin gwiwa wajen neman bahasi da gaskiya daga shugabanni kan yadda ake amfani da kuɗaɗen jama’a. Wannan kuwa, a ƙarshe, yana nufin ƙarfafa ci gaban ƙasa ne cikin sauri.