15/10/2025
Gwamnatin Tarayya da Tarayyar Turai sun kaddamar da shirin ilimi da ƙarfafawa matasa a Arewacin Najeriya
Gwamnatin Tarayyar Najeriya tare da Tarayyar Turai (EU) sun kaddamar da sabon shiri na ilimi da ƙarfafawa matasa mai darajar Yuro miliyan 40 domin inganta harkar ilimi a yankin Arewa maso Yamma na ƙasar.
An gudanar da kaddamarwar ne a Abuja, inda babban sakataren ma’aikatar ilimi ta tarayya, Abel Olumuyiwa Enitan, wanda Dr. Ejeh Usman ya wakilta, ya bayyana shirin a matsayin ginshikin manufar Renewed Hope Agenda ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma ‘Education Sector Renewal Initiative’ da ke nufin tabbatar da dama ga kowa wajen samun ingantaccen ilimi.
Shugabar sashen ilimi na matakin farko, Dr. (Mrs) Folake Davies Olatunji, ta ce shirin zai mayar da hankali ne wajen koyar da ilimi tun daga tushe, horar da malamai, inganta ilimin zamani ta hanyar fasaha da kuma bayar da damar ilimi ga kowa.
A nata jawabin, wakiliyar EU, Ms. Kate Kanebi, ta tabbatar da jajircewar Tarayyar Turai, inda ta bayyana cewa kuɗin da ya kai Naira biliyan 69.9 za su tallafa wajen samar da tsare-tsaren karatu cikin aminci, koyar da sana’o’in dogaro da kai musamman ga mata da marasa galihu.
Cibiyoyi irin su UBEC, TRCN, UNESCO, UNICEF, Plan International, Save the Children da kuma Bankin Duniya sun halarci taron.
Ƙarshe, taron ya kammala da alkawarin hadin gwiwa wajen tabbatar da ilimi mai inganci da ya shafi kowa a fadin ƙasar.