14/08/2025
A taron FEC na jiya, Shugaba Tinubu ya sake bada approvals din aiki a Lagos na gyaran gadoji guda biyu, Third Mainland Bridge akan kudi N3.6Trillion, da kuma gyaran gadar Carter ita kuma akan kudi N360Billion, idan ka hada su jimilla ya k**a kusan N4Trillion. Idan ka tara wannan tiriliyoyin akan lissafin N7Trillion da nai a baya na aiyukan da aka kai jihar Lagos, kenan a cikin shekaru biyun gwamnatin Tinubu an tura kudi a kalla N11Trillion. Wato TIRILIYAN GOMA SHA DAYA KENAN!
A sanda nai rubutin farko, an samu yan arewa da suke cikin gwamnatin Tinubu sun min raddi kala kala, cewa Tinubu na aiki a Arewa. Sun lissafo min aiyukan da kusan karashen na gwamnatin Buhari ne, a matsayin aiyukan Tinubu a Arewa, ciki harda titin Kano zuwa Hadejia, wanda ni hanyar gida na ce, kuma na san kiris ne ya rage, a karasa shi lokacin Gwamnati Buhari, amma dan rinto, an hada a cikin jeran aiyukan arewa da Tinubu yayi.
Tambaya ta ga yan Arewa dake cikin gwamnatin Tinubu shine, da karashen aikin Buhari da ake rinto da shi, da kuma aiyukan da ake daure mu da igiyar zato cewa za ayi su nan gaba, shin jimmillar su gaba daya a jihohin Arewa 19, kudin su ya kai N11Trillion? Idan kun ce ya kai, toh dan Allah ku lissafo min su.
Wato dan kana cikin gwamnati ba lasisi bane na ka kyale a cuci al'ummar ka. Idan ka ga ba daidai ba, toh ko ba za ka iya magana ba, ya k**ata ka kauda kai, ka kyale wanda za su iya su yi domin a gyara, wani zubin gwamnati sai da s**a.
Ba na mantawa lokacin Obasanjo, da sahalewar yan Arewan da ke cikin mulki, aka saka hannu a dokar 13% derivation, wanda hakan ta sa har yau, ake kwashe kaso sha uku, na ribar arzikin man kasa, ana bawa jihohin da suke da arzikin mai. Ban ce kar a basu ba, amma kowa ya san duk duniya ba inda ake bada kaso 13% sai a Najeriya.
Idan ba muyi wa tufkar hanci ba tun yanzu, ban san ya zata kasance ba Idan Tinubu ya zarce har tsahon shekara 8 yana mulki. Ba mamaki idan dan Arewa zai je Lagos sai yayi Visa! Ko mu hadu mu taka musu birki, ko su take mu har illa masha Allah!
Salihu Tanko Yakasai
Dawisun Kanawa
August 14, 2025.