28/08/2025
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya Jaddada Fifikon Gwamnatinsa Kan Gina Ababen More Rayuwa da Walwalar Ma’aikata
Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya bayyana cewa gwamnatinsa ta mayar da hankali wajen gina ababen more rayuwa da inganta walwalar ma’aikata a fannoni masu muhimmanci, ciki har da bangaren shari’a, majalisar dokoki da kuma ma’aikatar gwamnati, domin karfafa inganci da kuma samar da jin daɗin aiki.
Gwamnan ya yi wannan bayani ne lokacin da ya duba aikin gyaran da ake gudanarwa a Kotun Al’ada da kuma Babbar Kotun Yola.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa ta kuduri aniyar samar da ingantattun kayan aiki da muhallin aiki domin bai wa ma’aikata damar gudanar da ayyukansu cikin nagarta da kwarewa.
Gwamna Fintiri ya ce, kasancewar bangaren shari’a daya daga cikin muhimman rassan gwamnati uku, ya sami kulawa ta musamman ta hanyar samar da ofisoshin zamani masu inganci da jin daɗi.
Haka kuma, Gwamnan ya yaba da ingancin aikin da kamfanin da ke gudanar da aikin gyaran kotunan ke yi, inda ya bayyana cewa kayan daki da yanayin wurin sun nuna nagarta da kwarewa. Ya tabbatar da cewa gine-ginen za a kammala su nan gaba kadan sannan a mika su ga bangaren shari’a don fara amfani da su.
Bugu da kari, Gwamna Fintiri ya bayyana cewa ginin Majalisar Dokokin Jihar Adamawa yana cikin cikakken gyara, yayin da Gidan Gwamnati ya samu sabon kyan gani tare da ofisoshi na zamani ga Gwamna da ma’aikata.
Ya ce kuma tsofaffin gine-ginen ma’aikata da hukumomi, wadanda wasu tun daga zamanin Gongola aka gina su, an rusa su domin gina sabbin gine-ginen da s**a dace da bukatun zamani da jin daɗin aiki.
A bangaren walwala kuwa, Gwamna Fintiri ya bayyana cewa ma’aikatan gwamnati tuni s**a fara amfana da karin girma da alawus-alawus na kudi, har ma daga matakin makarantar firamare. Ya bayyana wannan ci gaba a matsayin abin tarihi da bai taba faruwa ba, wanda ma’aikata s**a karɓa da matukar farin ciki.