13/08/2026
Kabiru Adamu Abdullahi, wani jigo kuma tsohon na hannun daman jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya fice daga jam’iyyar NDC zuwa APC.
Abdullahi ya taɓa rantsuwa da Alƙur’ani kan ci gaba da kasancewa tare da Kwankwaso, tun bayan raba gari a siyasance da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf.
A wata wasiƙa da ya aika wa shugaban NDC na mazaɓar Kofar Ruwa da ke Ƙaramar Hukumar Dala a Kano, Abdullahi ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar, yana mai cewa rashin cikar alƙawuran da aka yi masa ne ya sa ya ɗauki matakin.
Ya ce ya shafe shekaru 29 yana tare da Kwankwaso, amma bai samu abin da yake tsammani ba, don haka ya yanke shawarar komawa APC domin marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya a zaɓen 2027.
“Na shafe shekaru 29 ina tare da Kwankwaso, amma babu abin da na samu sai rashin cika alƙawura. Zan je inda za a fi girmama ni,” in ji shi.