
25/07/2025
Allah Akbar.
BA'A KO ZAGIN WANDA YA MUTU ALAMOMI NE NA QARANCHIN KYAWAWAN HALAYE, RASHIN JIN KAI, DA RASHIN DABI'A NA GARI.
- Idan Mutum Ya Mutu Baya Iya Kare Kansa, Ko Bayyana Ayyukansa Wanda Ya Aywatar Don Kare Kansa Ga Maganganun Jama'a, Ko Neman Afuwa Ga Dukkan Kurakurai.
- Yin Ba'a Ga Matattu Sha-shanchi Ne Da Ragwanchi, Kuma Abu Ne Me Sauƙi Ka Hari Wanda Baze Iya Meda Martani Ba.
- Girmama Mamaci Cikakkiyan Ka'idar Da'a Ce Ta Duniya Wacce Aka Samo A Kusan Dukkanin Al'adu, Kabilu Da Wayewa.
- Iyali, Abokai Da Masoyan Mamacin Tuni Suna Chikin Makoki. Yin Izgili Ko Ba'a Ga Mamacin Su Yana Ƙara Musu Ciwo.
- Mutum Nagari Kan Fahimci Wahalhalu Tareda Yunkurin Gujewa Kara Musu Da Wata Wahalar Ko Cutarwar Da Bata Zama Dole Ba Musamman Ga Masu Zaman Makoki.
- Jama'a Zasuna Ganin Ka A Matsayin Maras Zuciya, Mai Cike Da Rashin Girmamawa, Kuma Mutum Maras Amana.
- Idan Ka Yi Wa Matattu Ba'a A Yau, Wasu Ba Za Su Yi Mamaki Ba Idan Ka Yi Musu Ba'a Bayan Sun Mutu.
- Koda Mutum Yana Da Aibu A Rayuwa, Mutuwa Lokaci Ne Domin Tunani Tare Da Jimami Ba Dariya Ko Ba'a Ba.
- Mai Hankali Yakan Yi Koyi Daga Abubuwan Da S**a Gabata, Maimakon Bata Ikonsa Da Lokachinsa Akan Kiyayya.
DAƊIN DAƊAWA:
Mutumin Da Yake Da Kyawun abi'u, Hankali, Bazai Taba Yin Ba'a Ko Zagin Mamachi Ba. Maimakon Yada Kiyayya, Mutum Mai Karfi Na Gaskiya, Yana Nuna Girmamawa Ko Da A Cikin Hali Na Jayayya, Ko Rashin Yadda Da Mahangar Juna.
Kuna So Wani Yayi Muku Ba'a Bayan Kun Mutu? Yi Ma'amala Da Jama'a Kamar Yadda Kuke So A Mu'amalanche Ku. Wannan Shine Alamar Mutumin Kirki.
- Ahmad Al-Najhry