04/09/2025
Day 4: A yayin da ake gudanar da QUIZ domin gwada fahimtar dalibai, a karkashin Program na koyar da Gyaran waya, fasahar AI da Cybersecurity, yayin da ake cigaba da training matasa ilimin AI da Cybersecurity a karkashin gidauniyar Professor Isa Ali Pantami (Majidadin Daular Usmaniyya),
Training ne da gidauniyar ta samar domin koyar da matasan jahar gombe sana'ar gyaran waya da koyar dasu Introduction to Artifical Intelligence da Cybersecurity a karo na ukku, An fara da batch 1 wanda yake dauke da dalibai 250, akwai na safe, akwai na rana.
Gidauniyar zata cigaba da daukar batches na dalibai har sai an cimma target In Sha Allah, har zuwa sauran jahohin nigeria.
Allah ya saka da Alkhairi..