26/10/2025
DA DUMI-DUMI: ‘Yan Sanda Sun Tarwatsa Ƙoƙarin Fashi a Azare, Sun K**a Mutane Biyu da Mak**ai.
Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Bauchi ta k**a wasu mutum biyu da ake zargi da aikata fashi da makami a garin Azare, Ƙaramar Hukumar Katagum, tare da kwato bindigogi biyu na gida da kuma babur da aka sace, bayan samun kiran gaggawa daga wani ɗan kasuwa a yankin.
A cewar sanarwar da kakakin rundunar, CSP Ahmed Mohammed Wakil, Anipr, Mnisma, MSPSP, ya fitar a yau Lahadi, 26 ga Oktoba, 2025, an samu kiran gaggawa daga wani mai suna Adamu Abdullahi daga unguwar Gandum Wambai, Azare, da misalin ƙarfe 5:00 na safe, inda ya bayyana cewa wasu barayi da mak**ai s**a kai masa hari a masana’antar GKY Food and Oil Mills, s**a sace babur ɗin sa.
Bayan samun rahoton, jami’an ‘yan sanda daga sashen Azare tare da hadin gwiwar ‘yan sa-kai s**a bi sawun barayin har zuwa ƙauyen Lafiya a kan hanyar Lafiya–Gwasame, inda s**a k**a su.
Wadanda aka k**a sun haɗa da:
1. Hassan Babangida, mai shekara 25
2. Abdullahi Hussaini, mai shekara 27 — dukkansu daga ƙauyen Hanafari, Ƙaramar Hukumar Jama’are, Jihar Bauchi.
Kayan da aka samu daga hannunsu sun haɗa da:
• Bindigogi biyu na gida
• Babur ɗin Bajaj da s**a sace.
Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Bauchi, CP Sani-Omolori Aliyu, psc(+), mni, ya yaba da saurin martani da nasarar jami’an rundunar tare da goyon bayan ‘yan sa-kai, yana mai tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da ƙoƙari wajen murkushe duk wata aikata ta’addanci ko fashi a jihar.
Ya kuma roƙi jama’a da su ci gaba da bayar da bayanai cikin lokaci ga ‘yan sanda domin inganta tsaro da kare rayuka da dukiyoyin al’umma.