16/10/2025
Sauye-sauyen Da Tinubu Ya Kawo Suna Haifar da Gagarumin Cigaba Ga Jama’a — Minista
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana cewa tsarin sauye-sauyen da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu yake aiwatarwa yana haifar da sakamako mai kyau, wanda ke bai wa gwamnatocin jihohi damar gudanar da ayyuka masu amfani kai-tsaye ga jama’a.
Idris ya bayyana hakan ne a Maiduguri, Jihar Borno, a ranar Laraba, yayin da ya jagoranci kwamishinonin yaɗa labarai daga jihohin da jam’iyyar APC ke mulki a wani zagayen duba muhimman ayyukan Gwamnatin Tarayya da na jihohi, wanda wani sashe ne na taron musamman wata hurhuɗu da suke yi a jihohi.
Ministan ya ce sauye-sauyen da gwamnatin Tinubu ta aiwatar sun ƙara yawan kuɗaɗen da ake tura wa jihohi, wanda ya ba su damar aiwatar da manyan ayyuka masu tasiri ga rayuwar talakawa.
Ya ce: “Ina tabbatar muku da cewa ajandar sauye-sauyen Shugaban Ƙasa na aiki yadda ya kamata. Yana ƙara wa jihohi kuɗaɗe domin su yi amfani da su wajen yi wa jama’a aiki.”
Tawagar ta ziyarci sabuwar cibiyar bada lantarki ta hasken rana mai ƙarfin 12MW a Jami’ar Maiduguri, wadda Hukumar Samar Da Wutar Lantarki a Karkara (REA) tare da goyon bayan Bankin Duniya ta gina.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Mohammed Mele, ya bayyana cewa wannan cibiya tana wadatar da jami’ar da asibitin koyarwa da wutar lantarki, tare da rage musu kashe kuɗin wuta da kusan naira miliyan 170 a duk wata.
Haka kuma, tawagar ta duba tashar samar da wuta ta gaggawa ta Maiduguri mai ƙarfin 50MW, wadda gwamnatin Buhari ta ƙaddamar, kuma gwamnatin Tinubu ta ƙara inganta ta, tana samar da wuta ko da yaushe ga gidaje da masana’antu a cikin birnin da kewaye.
Yayin da yake jaddada nasarorin da Gwamnatin Jihar Borno ta samu, Idris ya yaba wa Gwamna Babagana Umara Zulum bisa gina manyan makarantun zamani guda 104 da ya yi a dukkan mazaɓun sanata uku na jihar cikin shekara guda, yayin da aka kusa kammala guda 35.
Yayin da s**a kai ziyara a ɗaya daga cikin makarantun da aka sanya wa sunan Shugaban Ƙasa Tinubu, Idris ya ce wannan shiri yana nuna yadda gyare-gyaren da Gwamnatin Tarayya take aiwatarwa suke ba jihohi damar zuba jari a fannin ilimi da makomar yaran Nijeriya.
Sauran ayyukan da aka ziyarta sun haɗa da gadar sama ta Borno Express Terminus, wadda za ta zama gada ta huɗu da gwamnatin jihar ta gina, inda aikin ya fara tun a farkon wannan shekara.
Idris ya ce wannan nasara alama ce ta haɗin gwiwa mai kyau tsakanin Gwamnatin Tarayya da na jihohi.
“Wannan shi ne abin da haɗin kai tsakanin Gwamnatin Tarayya da na jihohi zai iya haifarwa,” inji shi.
Tawagar ta kuma ziyarci tashar cajin motocin lantarki ta Herwa EV Station — ɗaya daga cikin tashoshi bakwai da gwamnatin Jihar Borno ta kafa tare da goyon bayan Hukumar Cigaban Arewa Maso Gabas (NEDC).
Idris ya ce wannan shiri ya yi daidai da manufar Gwamnatin Tarayya ta ƙaura zuwa tsaftataccen makamashi da sababbin hanyoyin samar da wuta.
A ƙarshe, aikin gina sabon sashen ƙasa da ƙasa na Babban Filin Jirgin Sama na Muhammadu Buhari, Maiduguri, yana ci gaba da tafiya.
Shugaba Tinubu ya amince da haɓaka filin zuwa na ƙasa da ƙasa a watan Maris 2025, wanda hakan ya sanya shi zama shi kaɗai irin sa a yankin Arewa-maso-gabas.