28/08/2024
TSOKACI: 26-8-2024
Kisan Kare-Dangi A Arewacin Nijeriya
Daga: NAFI’U SALISU
Marubuci Kuma Manazarci
ALIYU ABDULLAHI GORA II Ya Yi Nazari Zai Kuma Karanto
Bisa dukkan alamu, da kuma yadda al’amurra ke wanzuwa a Nijeriya, ko shakka babu kashi cas’in da biyar cikin dari, al’amurra ne da su ke da alaka da cin amanar kasa da al’ummar ta.
Ga duk mai hankali da tunani, ya na ji tare da ganin irin abubuwan da ke wakana, kuma abubuwa ne da su ka cancanci a yi Allah-wadai da su, abubuwa ne da ba su da dadin ji, abubuwa ne da idan ka na jin yadda su ke wakana ko gani a kafafen yada labarai, to zuciyar ka za ta iya bugawa nan take matukar kana da kishin kasa da al’ummar ta.
Nijeriya kasa ce wadda Allah ya azurta ta kowace fuska, sai dai babbar matsalar da mu ke fuskanta ita ce yadda maciya amana su ka dabaibaye ta, su ka yi babakere a kan dukiyar kasa.
Babu dai kishin kasa a zukatan su, babu tsoron Allah da tausayin al’umma, babu tsoron mutuwa ko farfagabar mummunan karshe a rayuwar su, sun zama ‘yan bautar kudi da sayen rayuwar duniya ta kowace irin fuska, tamkar daga duniya babu sauran wani wuri da za a je.
A tarihin Nijeriya da kafuwar ta, ba a taba ganin cin amana da k**a-karya ba irin ta wannan zamanin da muke ciki, hatta kasashe makwabtan mu da Nijeriya ta fi su arziki da albarkar kasa, babu kasar da manyan ta su ke cin amanar kasa k**ar Nijeriya.
Tun da aka kafa Nijeriya, ba a taba tara dukiya da ma’adanan basa ba k**ar irin wannan zamanin na mulkin siyasa mai suna dimokraxiyya, amma babu wani lokacin da ‘yan kasa su ke ganin ta’addanci da ukubar rayuwa k**ar wannan zamanin.
An yi shugabanni da dama da su ka wuce a Nijeriya, k**a daga shugabannin mulkin soja da na farar hula, da Sarakuna da malamai da sauran al’umma, waxanda ba su tara dukiya da mabiya irin na yanzu ba, amma zukatan su cike da son kasa da kishin ta.
Zuciyoyin su su na kaunar al’ummar kasa da ma ita kan ta kasar, Ba su ci amanar kasa ba, ba su ci amanar al’ummar kasa ba, amma duk da haka an yi ma wasu daga cikin su kisan gilla k**ar su marigayi Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da sauransu.
Idan ka dauko tarihin Sardauna da Sir Abubakar Tafawa Balewa, wane laifi su ka yi da aka yi masu kisan gilla? Sun tsaya tsayin-daka sun bauta wa kasar nan, sun rike amanar kasa da -al’ummar ta.
Hatta da Turawan mulkin-mallaka sun ba su lambobin yabo na girmamawa saboda rike amanar kasa da al’ummar ta, amma yau an wayi gari, jagororin da su ke amsa sunan shugabanni a Nijeriya, ko shugabanni a yankin Arewacin Nijeriya, amma mafi yawancin su sun saida martaba da mutuncin Nijeriya, sun zubar da kimar Arewa, su na ji suna gani ana kashe bayin Allah, ana garkuwa da su a biya kudin fansa, ana farmakar garuruwa ana korar bayin Allah musamman manoma, wadanda su ka sadaukar da rayuwar su wajen noma abin da ‘yan kasa za su ci.
Wai a daidai lokacin da ya k**ata a ga wadancan manyan su na fada da nuna fushi tare da daukar mataki a kan zaluncin da ake yi wa bayin Allah, a’a, sai dai a hango su a wajen taron siyasa, ko taron bikin cika shekara a kan mulki.
Ku kalli yadda aka k**a Mai Martaba Sarkin Gobir Isah Muhammad Bawa, wanda dattijon kirki ne kuma basarake mai tsoron Allah da yaki da rashin gaskiya, amma manyan Arewa su na ji suna gani har aka kashe shi bayan an ci zarafin sa.
Shin yanzu da irin wannan shugabancin ne har wani zai fito ya kira kan sa da jagoran al’umma? Da irin wannan shugabancin ne ‘yan Nijeriya za su ce su na alfahari da kasar su ta haihuwa? Da irin wannan shugabancin ne dan Nijeriya kuma dan Arewa zai samu damar yin kasuwanci da sauran harkokin rayuwa cikin dadin rai da salama ballentana yayi barci da ido biyu?
Wannan kashe-kashen da ake yi a Arewacin Nijeriya da wasu sassan kasar nan, shiryayyen al’amari ne da aka samar da shi tun kafin shekara ta 1960, kuma shuwagabannin da su ka gabata sun ki yarda tare da amincewa wannan buri ya cika, kuma an bi ta kowacce irin hanya amma ba su amince ba, sai yanzu ne kwadayi da burin tara abin duniya ya sa ake kashe al’ummar Arewa, a rusa mu, a daidaita su.
Allah ya jikan marigayi tsohon shugaban kasa Umar Musa ‘Yar’adua, wanda a lokacin mulkin shi ya fitar da kudi domin samar da wutar lantarki a Arewacin Nijeriya don a samar da kamfanoni a bunkasa yankin, ta yadda al’ummar Arewa za su samu ayyukan yi, amma wasu tsirarun Sanatoci da Kwamishinoni da wasu Ministocin su ka karkatar da kudin s**a raba a tsakanin su.
Sai da wani daga cikin masu ba ‘ba shi shawara a kan samar da lantarki da sauran abubuwa ya same shi ya shaida ma shi abin da ya ke faruwa, nan take ‘Yar’aduwa yayi shiru ya sadda kan sa kasa tsawon lokaci, ashe labarin almundahanar da aka yi ne ya sa zuciyarsa ta tbuga, kuma daga wannan lokacin aka dauke shi zuwa kasar Saudiyya domin duba lafiyar sa, kuma tunda aka dawo da shi bai kara lafiya ba har Allah ya dauki rayuwar sa.
Idan a kan badakalar kudin wutar lantarki ran marigayi ‘Yar’adua ya baci har hakan ya zama sanadin ciwon zuciya, to yau wace irin barna da sata ce ba a yi?
Duk wadanda su ka fi kaurin suna wajen handama da baba-kere cikin manyan kasar nan ‘yan Arewa ne.
Su saci kudi su sa a k**a mutum a kulle, ga ‘yan ta’adda cikin gari da daji su na k**a mutane su na kashewa, su na yin garkuwa da su ana biyan kudin fansa, sun bar talakawa da yunwa da kuncin rayuwa da matsi, sun tura ‘ya’yan su kasashen Turai su na rayuwa mai kyau, amma talakan Nijeriya da ya tsinci kan sa ya na cin tafasa da dusar hatsi ba su bar shi ya ci tafasar a cikin salama ba, ba su bar shi ya jegona ya yi noma don sama wa kansa abinda zai ci a cikin sa ba.
Kasuwa ta gagari talaka, barci cikin salama ya gagari talaka musamman a yankin Arewa.
A lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari an tare Sarkin Fika a hanyar Abuja aka bude ma shi wuta, an kashe Hakimi a yankin Bauchi, an kashe a Katsina, an kashe a Zamfara, an kashe a jihar Neja, an kashe a Adamawa da sauran su, yanzu kuma gashi an kashe Sarkin Gobir, wanda duniya ta shaida Sarki ne adali.
Ina kira ga shugabannin Arewa, su sani cewa Allah ba ya barin addu’ar wanda aka zalunta ta tafi a banza, za ku mutu, kuma za mu hadu a gaban Allah, kuma Allah zai yi hisabi tsakanin mu da ku.
Ku dubi yadda kiri-kiri aka sa wa matatar mai ta Dangote ido, talaka ya na ganin zai samu sauki idan matatar ta fara samar da mai, amma wasu marasa kishin kasa su na kulla tuggu da makirci don ganin matatar ba ta samu damar da ya ke so ya samu ba. Wannan wane irin abin kunya ne?
Ruwa cikin cokali dai ya ishi mai hankali wanka!